NAF: An Bude Shafin da Matasan Najeriya Za Su Shiga Aikin Sojan Sama
- Hedkwatar rundunar sojin sama ta Najeriya ta sanar da fara daukar sababbin sojojidaga ranar 27 ga Agusta 2025
- Ana neman kwararru daga fannoni daban-daban da suka hada da kiwon lafiya da tsaron zamani da ya shafi yanar gizo
- NAF ta ce ana neman ‘yan asalin Najeriya da suka cancanta, kuma ba za a bukaci ko kobo wajen daukar aikin ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rundunar sojin saman Najeriya ta bude kofar daukar sababbin sojoji domin cike guraben da ake da su a fannoni da dama.
Rahotanni sun nuna cewa rundunar ta fitar da fannonin guraben aiki da ake bukatar 'yan Najeriya su nema.

Source: Twitter
Legit ta tattaro bayanai kan sanarwar da aka fitar ne a shafin rundunar sojin saman Najeriya a dandalin sada zumunta na X.
NAF za ta dauki Sojojin sama a Najeriya
Rundunar ta bayyana cewa tsarin daukar sababbin ma’aikatan zai shafi matasan da suka kammala karatu ne kuma suke da kwarewa.
NAF ta kara da cewa duk wanda ke sha’awar shiga aikin zai yi rajista kyauta ta shafin yanar gizo na rundunar.
Guraben aiki da aka fitar sun hada da bangaren kimiyya, lafiya da kuma tsaron zamani na yanar gizo.
Wannan mataki, in ji rundunar, na da nufin daidaita tsari da bukatun yaki na zamani da ake fuskanta.
Shirin daukar ma’aikata ya zo a lokacin da hukumomi ke kara daukar matakai don dakile kalubalen zamani, musamman yadda fasahar zamani ke taka muhimmiyar rawa kan tsaro.
Sharudan daukar sojojin sama
Rundunar ta fayyace cewa duk mai neman sojan dole ne ya kasance dan asalin Najeriya da aka haife shi a kasar, kuma shekarunsa su kasance tsakanin 20 zuwa 32.
Duk da haka, rundunar ta ce manyan likitoci za su iya kaiwa shekaru 40 a lokacin da suke neman aikin.

Source: UGC
An kuma shimfida sharadin tsayin jiki, inda ake bukatar kada maza su kasance kasa da mita 1.66, yayin da mata kuma ba za su kasance kasa da mita 1.63 ba.
Dole ne kuma duk mai neman shiga aikin damarar ya kasance ba shi da laifi a kotu, ya na cikin koshin lafiya ta jiki da kwakwalwa.
Bukatar ilimi da kwarewar masu neman soja
Daga cikin sharuddan matakin karatu, an ce dole ne duk wanda ke neman aikin ya kasance ya samu sakamako mai kyau daga jami’a.
Baya ga haka, Punch ta rahoto cewa an an ce dole ne mutum ya mallaki takardar kammala hidimar kasa ta NYSC ko kuma wata shaida daga hukumar.
Rundunar ta ce wannan tsari zai baiwa rundunar damar samun kwararru da za su kara karfafa bangaren kimiya, kiwon lafiya da kuma tsaron yanar gizo, domin su ne ginshikan yaki a duniya.
Dangote zai dauki ma'aikata a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya bude shafin daukar ma'aikatan a fadin Najeriya.
Binciken Legit Hausa ya gano cewa za a dauki ma'aikatan ne domin cike gibin da aka samu a kamfanonin Dangote a jihohi.
Dangote ya bayyana cewa za a dauki ma'aikatan ne a matakai daban daban, inda ake bukatar wadanda suka yi karatu da masu kwarewa.
Asali: Legit.ng


