Gwamnatin Jigawa Ta Ayyana Hutun Rana 1 ga Ma'aikata saboda 'Wani Muhimmin Biki'
- Ma'aikata za su kasance tare da iyalansu na yinin yau Laraba, yayin da gwamnatin jihar Jigawa ta ayyana hutun rana daya
- Gwamnatin Jigawa ta ayyana Laraba, 27 ga Agusta, a matsayin ranar hutu domin bikin murnar cikar jihar shekaru 34 da kafuwa
- Legit Hausa ta zakulo bayanai game da asalin Jigawa da yadda Malam Inuwa-Dutse, ya jagoranci fafutukar kafuwarta a 1991
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jigawa - Gwamnatin Jigawa ta ayyana Laraba (yau) a matsayin hutu domin bikin cikar shekaru 34 da kafa jihar.
Wannan umarni ya fito ne cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikatan Jigawa, Muhammad Dagaceri, ya sanya wa hannu, aka kuma rabawa ’yan jarida a Dutse.

Source: Facebook
An ba da hutu a jihar Jigawa
Gwamnatin ta bukaci al’ummar jihar su halarci bukukuwa da shirye-shiryen da aka tanada a sassan jihar don bikin wannan rana ta musamman, inji jaridar Punch.
Haka kuma gwamnati ta taya duk ’yan asalin Jigawa murna kan wannan gagarumin tarihi, tare da ƙarfafa gwiwarsu kan yin addu’a domin ci gaban jihar da Najeriya baki ɗaya.
A cewar sanarwar, hutun ya shafi ma’aikata da mazauna jihar domin su huta da yin godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa zaman lafiya da ni’imomin da ya ba jihar.
“Wannan hutun da aka ayyana zai bai wa jama’a damar shiga bukukuwa da addu’o’in da aka shirya,” a cewar sanarwar.
Gwamnatin Jigawa ta ba mutane shawara
Dagaceri ya shawarci jama’a da su yi amfani da wannan dama wajen yaba wa ci gaban da aka samu tun daga kafa jihar zuwa yanzu, tare da roƙon kyakkyawar makoma.
Gwamnati ta kuma jaddada muhimmancin haɗin kai da ci gaba, tana mai cewa wannan hutun na nuna aniyar jihar wajen girmama tarihi ta da kuma ƙarfafa zumunci tsakanin jama’a.
A cewar sanarwar:
“Wannan mataki ya nuna yadda jihar ke girmama tarihin kafuwarta da kuma ƙarfafa zumunci a tsakanin jama’a."

Kara karanta wannan
'Yan sanda sun dauki mataki yayin da masu Mauludi suka fara zagayen gari a Jigawa
Takaitaccen bayani game da kafuwar Jigawa
Jigawa ta kasance daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da aka kafa a ranar 27 ga Agusta, 1991, a lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida.
Kafin haka, Jigawa tana cikin jihar Kano, a Arewa maso Gabashin Kano, kuma tana da iyaka da ƙasar Nijar. Dutse ce babban birnin jihar.
Jihar Jigawa na da ƙananan hukumomi 27 kamar yadda wani rahoto da aka wallafa a shafin Wikipedia ya bayyana.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka jagoranci fafutukar samar da jihar shi ne Malam Inuwa-Dutse, tsohon kwamishina a ma’aikatar noma a lokacin mulkin Audu Bako, gwamnan tsohuwar Kano.

Source: Original
Takaitaccen bayani game da mutanen Jigawa
Ita ce ta tara a jerin jihohi mafi girma ta fuskar yawan jama’a a Najeriya, inda yawancin mazauna Jigawa suka kasance Hausawa da Fulani.
Mafi rinjayen al’ummar Jigawa Musulmai ne, kuma tana daya daga cikin jihohin da ake gudanar da Shari’ar Musulunci a ƙasar.

Kara karanta wannan
ASUU: Malaman jami'a sun fara yi wa gwamnatin Tinubu zanga zanga a fadin Najeriya
Daga cikin abubuwan tarihinta akwai Dutsen Habude a Birnin Kudu, wanda aka gano ya samo asali tun zamanin Neolithic.
Har ila yau, Hadejia (tsohuwar Biram) na daga cikin ƙasashen “Hausa bakwai na asali” da aka sani a tarihi.
An sanya dokar ta baci a Jigawa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, binciken da gwamnatin Jigawa ta gudanar kan ilimi a makarantun jihar ya tilasta Gwamna Umar Namadi ayyana dokar ta baci.
Gwamna Namadi ya ce hankalinsa ya tashi sosai da ya ga rahoton cewa kaso 80 cikin 100 na 'yan aji daya a firamare ba sa iya karatu da rubutu a jihar.
A matsayin matakin gaggawa, Gwamna Namadi ya ce ya raba ma'aikatar ilimi zuwa gida biyu, kuma ya dauki wasu matakai na dawo da martabar ilimi a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
