Jerin gwamnoni da suka mulki jihar Kano, tun daga Audu Bako
- Jihar Kano ta dabo tumbin giwa ko da me kazo an fi ka ta cika shekaru 50 da kafuwa
- Gwamna Abdullahi Bako ne ya fara mulkar jihar a shekarar 1967
A shirin gudanar da bukukuwan cikar jihar Kano shekaru 50 da kirkira da a yanzu haka gwamnatin jihar ke yi, Wakilin jaridar Rariya Aliyu Ahmad ya kawo mana jadawalin gwamnonin da suka mulki Jihar tun daga shekarar 1967 zuwa 2015.
1. Kwamishinan 'Yan Sanda, Audu Bako - Daga Mayu, 1967 Zuwa Yuli, 1975

2. Kanal Sani Bello, Gwamnan Soja, daga Yuli, 1975 zuwa Satumba, 1978

3. Kaftin Ishaya Shekari, mulkin soja, daga Satumba, 1978 zuwa Oktoba, 1979

4. Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi, mulkin siyasa a karkashin jam'iyyar PRP, daga Oktoba, 1979 zuwa Mayu, 1983

KU KARANTA: Gwamnati ta ware naira miliyan dubu 46 don ƙarasa aikin madatsar ruwa na Kashimbila
5. Alhaji Abdu Dawakin Tofa, mulkin siyasa a karkashin jam'iyyar PRP, daga Mayu, 1983 zuwa Oktoba, 1983

7. Alhaji Sabo Bakin Zuwo, mulkin siyasa a karkashin jam'iyyar PRP, daga Oktoba, 1983 zuwa Oktoba, 1983.

8. Kwamared Hamza Abdullahi, mulkin soja daga Janairu, 1984 zuwa Agusta, 1985

9. Kanal Ahmed Muhammad Daku, mulkin soja daga Agusta, 1985 zuwa,1987

10. Kaftin Mohammed Ndatsu Umaru, mulkin soja daga Disamba, 1987 zuwa Yuli, 1988

11. Kanal Idris Garba, mulkin soja, daga Agusta, 1988 zuwa Janairu, 1992

12. Architect Kabiru Ibrahim Gaya, mulkin siyasa a karkashin jam'iyyar NRC, daga Janairu, 1992 zuwa Nuwamba, 1993

13. Kanal Muhammadu Abdullahi Wase, mulkin soja daga Disamba, 1993 zuwa Yuni, 1996.

14. Kanal Dominic Oneya, mulkin soja daga Agusta, 1996 zuwa Satumba, 1998.

15. Kanal Aminu Isa Kontagora, mulkin soja daga Satumba, 1998 zuwa Mayu, 1999.

16. Injiniya (Dr.) Rabiu Musa Kwankwaso, mulkin siyasa a karkashin jam'iyyar PDP, daga Mayu, 1999 zuwa Mayu, 2003

17. Malam Ibrahim Shekarau, mulkin siyasa a karkashin jam'iyyar ANPP, daga Mayu, 2003 zuwa Mayu, 20011

18. Injiniya (Dr.) Rabiu Musa Kwankwaso, mulkin siyasa a karkashin jam'iyyar PDP, daga Mayu, 2011 zuwa Mayu, 2015

19. Abdullahi Umar Ganduje, mulkin siyasa a karkashin jam'iyyar APC

Legit.ng ta binciko, Janar Yakubu Gowon ne ya kirkiri jihar Kano a zamanin mulkinsa a lokacin da ake yakin basasa, inda ya samar da wasu jihohi da suka hada da Ribas, Legas da sauran jihohi 9.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Sarkin Kano Muhammadu Sunusi yayi caccaka
Asali: Legit.ng