Gwamna Ya Kara Albashi, Wasu Ma'aikata za Su Samu Rabin Miliyan a Wata

Gwamna Ya Kara Albashi, Wasu Ma'aikata za Su Samu Rabin Miliyan a Wata

  • Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, ya sanar da karin mafi ƙarancin albashi daga N76,000 zuwa N104,000
  • Albashin likitoci da malaman jami’a ma ya karu sosai, likitoci za su samu sama da rabin Naira miliyan
  • Kungiyoyin kwadago sun yaba da matakin, suna cewa ya zama babban nasara ga ma’aikatan jihar Imo

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A wani sabon mataki da ya jawo farin ciki ga ma’aikatan jihar Imo, Gwamna Hope Uzodimma ya sanar da amincewa da sabon mafi ƙarancin albashi.

Karin albashin ya kasance sakamakon tattaunawa da shugabannin kungiyoyin kwadago a daren Talata a gidan gwamnati dake Owerri.

Gwamnan Imo da ya yi wa ma'aikata karin albashi
Gwamnan Imo da ya yi wa ma'aikata karin albashi. Hoto: Imo State Government
Source: Facebook

Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa karin albashin ya hada da sauye-sauye ga wasu muhimman fannoni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnati ta dauki wannan mataki ne domin gina kyakkyawar alaka da 'yan kwadago, da kuma inganta jin dadin al’ummar jihar baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Badakalar N6.5bn: Gwamnatin Kano ta bar manyan lam'a wajen wanke hadimin Abba

Karin albashi da sauye-sauye a Imo

Uzodimma ya ce gwamnatin Imo ta dauki matakan karfafa tattalin arzikin jihar ta hanyar kara kudin shiga daga cikin gida daga N400m zuwa sama da N3bn a kowane wata.

Ya kara da cewa daga shekarar 2020 zuwa yanzu, kudin da ake samu daga tarayya sun ninka, daga N5bn–7bn zuwa N14bn.

A kan haka ya yi karin albashi, inda ikitoci a jihar za su rika karɓar N503,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Malaman makarantu da suka hada da jami'o'i a manyan makarantu sun samu karin mafi karancin albashi zuwa N222,000.

Rahoton TVC ya nuna cewa gwamnatin ta yi karin albashi ga sauran ma'aikata daga N76,000 zuwa N104,000

Tasirin cire tallafin man fetur a Imo

Gwamnan ya bayyana cewa cire tallafin mai ya kawo ƙarin tsadar rayuwa, amma kuma ya bada dama ta karin kudin shiga da ake rabawa jihohi.

Rahotanni sun nuna cewa ya ce gwamnati na kokarin ganin al’umma suna ganin sauyin wannan mataki a zahiri.

Kara karanta wannan

Babu zama: Kwankwaso ya dura Legas bayan ruguza kasuwar Hausawa

Uzodimma ya kuma sanar da cewa daga 27 ga watan Agusta za a fara biyan ragowar fansho na N16bn ga tsofaffin ma’aikata.

Ya ce an aiwatar da manyan sauye-sauye a bangaren lafiya, ciki har da kafa tsarin inshorar lafiya da kuma gyaran cibiyoyin kiwon lafiya.

Shugaban kwadagon Najeriya, Joe Ajaero
Shugaban kwadagon Najeriya, Joe Ajaero. Hoto: Nigeria Labour Congress HQ
Source: Facebook

Martanin kungiyoyin kwadago a Imo

Shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC) a jihar, Uchechigemezu Nwigwe, ya bayyana wannan karin albashi a matsayin babbar nasara ga ma’aikata.

Ya ce gwamnan ya ceci ma’aikata daga tsananin kuncin tattalin arziki, tare da sanya Imo cikin jerin jihohin da ke biyan albashi mai tsoka.

Haka zalika, shugaban kungiyar TUC na jihar, Uchenna Ibe, ya yabawa gwamnan karin albashi da ya yi.

A karshe, gwamnan ya bukaci ma’aikata su nuna godiya da aiki tukuru, da gujewa rashin gaskiya da sakaci domin tabbatar da ci gaban jihar.

Amurka ta koka kan albashin Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta yi magana kan mafi karancin albashin Najeriya.

Rahoton da kasar ta fitar ya nuna cewa raguwar darajar Naira ya shafi sabon mafi karancin albashin kasar.

Bayan doguwar tattaunawa da barazanar yajin aiki tsakanin gwamnatin Najeriya da 'yan kwadago ne aka mayar da albashin zuwa N70,000.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng