Abu Ya Girma: Gwamna Ya Shirya Tsige Sarki Mai Martaba a Najeriya
- An kama Sarkin Ipetumodu daga jihar Osun, Joseph Oloyededa da laifin cinye kudin tallafin korona da ya karba da bayanan bogi a kasar Amurka
- Bayan tabbatar da laifinsa, kotun Amurka ta yanke masa hukuncin daurin watanni 56, lamarin da ya jawo sarautarsa ta fara tangal-tangal
- Gwamnatin jihar Osun na shirin tsige Sarkin sakamakon wannan laifi da ya aikata, wanda ya jawo masa daurin shekaru sama da hudu a kurkuku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osun - Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun na shirin tsige Mai Martaba Sarkin Ipetumodu, Oba Joseph Oloyede biyo bayan daurin sama da shekaru hudu da aka masa a Amurka.
Rahotanni sun nuna cewa matukar ba a samu wani sauyi daga baya ba, Gwamna Adeleke zai tube wa Sarkin rawani sakamakon laifin da ya aikata har aka daure shi.

Source: Facebook
Leadership ta tattaro cewa a makonnin da suka shude, Gwamnatin jihar Osun ta ce ba za ta yanke hukunci kan makomar sarkin ba har sai an kammala shari’arsa a Amurka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane laifin Sarkin ya aikata a Amurka?
A jiya Talata, 26 ga watan Agusta, 2025 aka kammala shari'ar Sarkin, inda kotun Amurka ta yanke masa hukuncin daurin watanni 56 a gidan gyaran hali.
Alkalin kotun Tarayya na Amurka, Mai Shari'a Christopher A. Boyko ne ya yanke wa basaraken wannan hukunci bayan kama da shi da laifin zambar Dala miliyan 4.2 na tallafin korona.
Ofishin Antoni-Janar na Amurka da ke yankin Ohio ya bayyana cewa bincike ya nuna Oba Oloyede da abokinsa Edward Oluwasanmi sun hada kai sun ci kudin tallafin korona.
Rahoton bincike ya nuna cewa wadanda ake tuhumar sun cike bayanan karya tare da karbar wadannan makudan kudi da aka ware don bai wa yan kasuwa rance a lokacin annobar korona.

Kara karanta wannan
Abin kunya: Amurka ta daure Sarkin Najeriya da ya sace Naira biliyan 6.4 na COVID 19
Kotun Amurka ta daure Sarki dan Najeriya
A watan Afrilu, duka wadanda ake tuhuma sun amsa laifin yin zamba da laifin lakume sama da Dala miliyan 4.2 daga kudaden tallafin gwamnati.
Bayan tabbatar da tuhumar da ake wa Sarkin, Kotun Amurka ta yanke masa hukuncin daurin watanni 56.
Kotun ta kuma umarci Sarkin ya biya fiye da Dala miliyan 4.4, sannan ya mika gidansa da sauran kadarorin da ya mallaka ta hanyoyin da doka ta haramta.

Source: Twitter
Gwamnan jihar Osun ya fara shirin tsige Sarki
A halin yanzu, ana jiran ganin matakin da gwamnatin Osun za ta dauka kan Sarkin bayan ta tabbata ya aikata laifin zamba kuma an daure shi a Amurka.
Bayanai sun nuna cewa matukar ba a samu wani sauyi ba, Gwamna Adeleke zai sauke Oba Joseph Oloyede daga matsayin Sarkin.
Kotu ta tura wani basarake gidan yari a Osun
A wani labarin, kun ji cewa wata kotu a Ede a jihar Osun ta ba da umarnin tsare wani basarake da aka dakatar, Jimoh Abdulkabir.
Rahotanni sun nuna cewa ana tuhumar basaraken ne mai shekara 45, wanda aka dakatar daga matsayin Loogun na Edeland, kan bata suna ga wani mutumi, Adam Akindere.
Tun farko dai Sarkin Ede, Oba Munirudeen Lawal ya dakatar da basaraken ne bisa zargin rashin ladabi kuma hannunaa a badakar filaye.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

