NSIB Ta Gano Wasu Bayanai kan Hatsarin Jirgin Kaduna, An Ji Halin da Fasinjoji 6 ke Ciki
- A yau Talata ne jirgin kasa ya sauka daga layin dogo bayan ya taso daga Abuja kafin ya karasa tasharsa da ke Rigasa a jihar Kaduna
- An ruwaito cewa jirgin ya sauka daga kan titinsa, lamarin da ya jawo kifewar wasu taragon jirgin wanda ya jefa fasinjoji cikin fargaba
- Hukumar NSIB ta bayyana cewa fasinjoji shida sun samu raunuka a hatsarin kuma ta fara bincike don gano ainihin abin da ya faru
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Ana ci gaba da samun bayanai kan halin da fasinjojin jirgin kasan da ke jigila daga Abuja zuwa Kaduna suke ciki bayan hatsarin da ya auku.
Aƙalla fasinjoji shida sun ji rauni bayan jirgin kasa mai zuwa Kaduna ya kife a KM 49 tsakanin tashar Kubwa da tashar Asham, a ranar Talata, 26 ga watan Agusta, 2025.

Kara karanta wannan
Ta faru ta ƙare: Hukumar jiragen ƙasa ta dakatar da zirga zirga daga Kaduna zuwa Abuja

Source: Twitter
Hukumar Binciken Tsaro ta Najeriya (NSIB) ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan hulda da jama'a, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NSIB ta ce fasinjoji 6 sun samu raunuka
A ciki sanarwar, hukumar NSIB ta bayyana cewa mutane shida ne suka ji rauni, amma babu wanda ya rasa ransa sakamakon hatsarin jirgin kasan.
NSIB ta tabbatar da cewa ta tura tawagar bincike zuwa wurin da lamarin ya faru domin tattara shaidu, tattaunawa da masu ruwa da tsaki, da kuma fara bincike kan abubuwan da suka haddasa hatsarin jirgin
Idan baku manta ba, jirgin kasan ya gamu da hatsari ne sakamakon sauka daga layinsa, an ce wasu daga cikin taragon jirgin sun kife
Wane mataki hukumar NSIB ta dauka?
Da take bayanin abubuwan da aka gano bayan hatsarin jirgin kasan, NSIB ta ce:
“Bayanan da muka samu kawo yanzu sun nuna cewa mutane shida sun ji rauni, babu wanda ya mutu.
"Mun tura tawagar bincike zuwa wurin domin tattara shaidu, tattauna da masu ruwa da tsaki, da fara bincike kan dalilan da suka jawo wannan hatsari.
“Hukumar NSIB tana jajantawa wadanda suka ji rauni kuma tana tare da fasinjojin da lamarin ya shafa.
"Binciken mu zai mai da hankali kan gano ainihin dalilan da suka haddasa kifewar jirgin kasan tare da bayar da shawarwari don hana faruwar irin haka a nan gaba."
NSIB ta jajantawa wadanda suka ji rauni
A nasa bangaren, shugaban hukumar NSIB, Kyaftin Alex Badeh, ya ce,
“Muna jajantawa duk wadanda suka ji rauni. Hukumarmu ta tura masana bincike zuwa wurin domin gano ainihin abin da ya haddasa wannan kifewar.
“Manufarmu ita ce tabbatar da cewa zirga-zirgar jiragen kasa a Najeriya tana da aminci ta hanyar gudanar da bincike mai zaman kansa kuma a fili.”
Hukumar NSIB ta kuma tabbatar da cewa za a ci gaba da sanar da jama’a yadda binciken ke tafiya, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Source: Twitter
Yaran Dawisu suka tsira daga hatsarin jirgin
A wani rahoton, kun ji cewa Salihu Tanko Yakasai ya bayyana yadda 'ya 'yansa uku da 'yan uwansa guda biyu suka tsallake rijiya ta baya a hatsarin jirgin kasan Kaduna.
Tsohon hadimin na Abdullahi Umar Ganduje ya ce a farko sun tsara shiga jirgin da ya yi hatsarin amma daga bisani suka canza shawara, suka biyo mota.
Ya ce akwai yayansa uku da 'yan uwansa biyu da suka yi niyyar yin tafiya a jirgin da ya yi hatsari amma Allah ya tseratarsu da suka canza shawara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

