‘Abin da ba Ku Sani ba’: Tinubu Ya Fadi babban Abin da Ya Cimma bayan Hawa Mulki

‘Abin da ba Ku Sani ba’: Tinubu Ya Fadi babban Abin da Ya Cimma bayan Hawa Mulki

  • Shugaba Bola Tinubu ya bugi kirji kan abubuwan ci gaba da ya kawo tun bayan hawansa mulki a Najeriya a karshen Mayun 2023
  • Mai girma Tinubu ya bayyana bangaren da ya kawo sauyi a kasar inda ya yaba da nasarorin sauye-sauyen tattalin arziki
  • Ya jaddada wa masu saka jari na Brazil cewa Najeriya kasa ce mai yalwa, ya nemi haɗin kai a masana’antu, makamashi da abinci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Brasília, Brazil - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya shawarci masu son zuba hannun jari a Najeriya.

Shugaba Tinubu ya tabbatar wa masu saka hannun jari daga Brazil cewa babu cin hanci da rashawa a Najeriya tun bayan hawansa mulki.

Tinubu ya yi alfahari kan cin hanci a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Tinubu ya roki a zuba jari a Najeriya

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin taro da ministoci daga kasashen biyu da mambobin 'Brazil Business Group' a ranar Litinin, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

JIBWIS ta ƙalubanci masu cewa an yi wa Jingir ihu a Abuja, ta sanya kyautar kuɗi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce sauye-sauyen da gwamnati ta aiwatar sun fara kawo sakamako a kasa inda suka tattauna batutuwan hadin gwiwa.

Tinubu ya ce Najeriya kasa ce mai fadi da damarmaki, inda ya bukaci kamfanonin Brazil su zuba jari a bangaren abinci, masana’antu, makamashi da fasahar zamani.

Ya amince cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da aka fara sun yi tsanani a farko, amma a yanzu sakamakon yana fara bayyana, kuma jama’a sun fara gani.

A cewarsa, yanzu Najeriya na da kudi don gudanar da harkokin tattalin arziki cikin gaskiya da rikon amana inda ya kara da cewa babu cin hanci a yanzu.

Shugaban ya bayyana misali da Babban Bankin Najeriya, inda ya ce yanzu ba sai an san wani ba kafin samun kudin musayar kasashen waje.

Tinubu ya bugi kirji game da cin hanci a gwamnatinsa
Bola Tinubu yayin wani taro a fadar shugaban kasa. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Tinubu ya tuna da huldarsa da Brazil a baya inda ya ce lokaci ya yi da za a bar cika baki, a koma ayyuka na zahiri.

Kara karanta wannan

'Iya kudinka, iya gaskiyarka,' Sarkin Musulmi ya ce mai dukiya ke sayen adalci a Najeriya

Ya ce a baya an bari wasu matsaloli sun hana ci gaba, amma yanzu gwamnatinsa ta yanke shawarar kawo karshen hakan gaba daya.

Tattaunawar Tinubu da shugaban Brazil

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Tinubu ya halarci liyafar kasa a fadar Itamaraty Palace tare da shugabannin Brazil.

A wajen liyafar, sun tattauna batutuwan bunkasa kasuwanci, karfafa kirkire-kirkire da samar da yarjejeniyoyi don fadada hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

Sababbin yarjejeniyoyin da aka rattabawa hannu tsakanin Najeriya da Brazil za su bude wasu hanyoyin ci gaban kasuwanci, kirkire-kirkire da fasahar zamani.

Tinubu ya ce wannan sabon mataki zai tabbatar da dorewar tattalin arziki, samun sababbin hanyoyin ci gaba da kuma bunkasa kyakkyawar alaka tsakanin kasashen biyu.

Tinubu ya bar Japan zuwa Brazil

Kun ji yadda shugaba Bola Tinubu ya tashi daga Yokohama, Japan, zuwa Brazil inda ya fara ziyarar aiki ranar Lahadi, 24 ga watan Agusta.

A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, ya yi yada zango a Los Angeles kafin ya nufi Brasília, babban birnin Brazil ganin tsawon tafiyar.

Wannan tafiya ta zama mataki na biyu a rangadin ƙasashen biyu da ya fara daga Abuja ranar 15 ga watan Agusta 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.