Kaduna: Gwamnatin tarayya ta Samo wa Uba Sani Bashin Kasar Waje, Za a Karbo $25.35m
- Gwamnatin tarayya ta samu rancen dala miliyan 25.35 daga Kuwait domin rage yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar Kaduna
- Gwamnati ta bayyana cewa za ta tabbatar da cewa ko sisi bai zurare ba domin zakulo yaran da ke zaman gida a lungu da sakon Kaduna
- Kadan daga cikin ayyukan da za a aiwatar da kudin akwai shirin zai gina ko sabunta fiye da makarantu 200 a sassa daban daban
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Gwamnatin tarayya ta kulla yarjejeniyar samun rancen Dala miliyan 25.35 daga Cibiyar bunkasa tattalin arzikin Larabawa ta Kuwait.
Ta nemo rancen ne domin tallafawa shirin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Jihar Kaduna da kuma inganta bangaren ilimi baki daya.

Source: Twitter
RFI ta wallafa cewa yarjejeniyar rancen da gwamnatin tarayya ta rattaba wa hannu a madadin gwamnatin jihar Kaduna, na cikin wani hadin gwiwar kuɗi na Dala miliyan 62.8 tare da abokan cigaban ƙasa da ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana sa ran wannan hadin gwiwa zai faɗaɗa samun ingantaccen ilimi a yankin da ke fama da matsalar yaran da suka daina ko ba su fara karatu ba.
Gwamnatin jihar Kaduna ta samo bashin kudi
Jaridar Punch ta wallafa cewa a cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Kuɗi, Mohammed Manga, ya fitar, ya fadi yadda kudin zai tallafa masu.
Ya yi bayanin cewa za a kara karfafa shirin gwamnati na tabbatar da cewa ilimi ya kai ga kowane lungu da sako da yaro na jihar Kaduna.
Ya ce shirin zai bai wa fiye da yara 100,000 damar shiga makaranta, sannan za a gina ko sabunta fiye da makarantu 200 a cikin al’ummomin da ke da ƙarancin wuraren karatu.
Haka kuma za a inganta yanayin koyarwa da ilimin malamai domin ɗaga matsayin ilimi a yankunan da aka fi buƙatar hakan.
Ministan Kuɗi da Tattalin Arziki, Wale Edun, wanda karamar Ministan Kuɗi, Dr Doris Uzoka-Anite ya wakilta, ya ce wannan shiri na nuna jajircewar gwamnati kan yadda ta ke ayyukanta.
Ya ƙara da cewa, kasancewar har yanzu miliyoyin yara a Arewacin Najeriya ba sa zuwa makaranta, za a tabbatar da cewa an yi amfani da kudin yadda ya dace.
Gwamnatin Kaduna ta magantu kan inganta ilimi
Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya tabbatar da cewa jihar ta riga ta cika alƙawarin kuɗin haɗin gwiwa na Dala miliyan daya, tare da ƙara kason ilimi a kasafin kudin bana zuwa 26%.
Shugaban gidauniyar Kuwait Fund, Dr Wahid Al-Bahar, ya cewa sun bayar da lamunin domin a tabbatar da cewa kowane yaro ya samu damar yin karatu.
Gwamnati na shirin inganta ilimi a Najeriya
A baya, mun wallafa cewa gwamnatin tarayya ta sanar da sabon shirin inganta ilimi da ta kira BETA, domin magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta a sassan kasar nan.

Kara karanta wannan
Mazauna Katsina sun karyata ikirarin gwamnati na kubutar da su daga hannun 'yan ta'adda
Ministan ilimi, Dr Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a wani taro a Abuja, inda ya ce shirin zai bai wa iyaye mata tallafin kuɗi domin su tura ’ya’yansu makaranta a kai a kai.
Alausa ya ce tsarin ya haɗa da shirin mayar da yara makaranta tare da haɗin gwiwa da Hukumar Almajirai ta Kasa, domin tabbatar da cewa kowa ya samu ilimi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

