Hankalin Gwamna Namadi Ya Tashi bayan Karanta Rahoto, Ya Sanya Dokar Ta Baci a Jigawa
- Binciken da gwamnatin Jigawa ta gudanar kan ilimi a makarantun jihar ya tilasta Gwamna Umar Namadi ayyana dokar ta baci
- Gwamna Namadi ya ce hankalinsa ya tashi sosai da ya ga rahoton cewa 'yan aji daya a firamare ba sa iya karatu da rubutu
- A matsayin matakin gagawa, Gwamna Namadi ya ce ya raba ma'aikatar ilimi zuwa gida biyu, kuma ya dauki wasu matakai
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jigawa - Gwamnatin Jigawa ta ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi, inda ta gabatar da sauye-sauye masu zurfi domin magance ƙarancin fahimtar karatu da rubutu tare da ƙarfafa ginshiƙin ilimi a fadin jihar
Gwamna Umar Namadi, ya bayyana cewa binciken farko ya nuna yara takwas cikin 10 a ajin farko na firamare ba su iya karatu ko rubutu ba.

Kara karanta wannan
Asiri ya tonu: NNPCL ya gano hannun kungiyoyin kasashen waje a satar man Najeriya

Source: Twitter
Gwamna ya ayyana dokar ta baci a Jigawa
A tattaunawar da ya yi da jaridar Punch, Gwamna Namadi ya ce:
“Ina tabbatar maka, ilimi shi ne ginshiƙin kowace al’umma. Abin da muka gano ya firgita mu sosai, shi ya sa muka ayyana dokar ta baci da gaggauta ɗaukar wasu matakai."
A matsayin wani ɓangare na sauye-sauyen, gwamnatin Jigawa ta raba ma’aikatar ilimi gida biyu, watau ilimin a matakin farko da ilimin manyan makarantu.
Gwamna Namadi ya bayyana cewa an raba ma'aikatar zuwa gida biyu ne domin rage jinkiri wajen isar da sabis da kuma tabbatar da daidaito a harkar ilimi.
Gwamna ya dauki malamai 10, 000 aiki
Domin magance ƙarancin malamai, Gwamna Namadi ya ce gwamnatinsa ta dauki malamai 3,000 daga cikin 4,500 da ke aikin wucin gadi a shirin J-Teach.
Ya ce gwamnatin ta ɗauki sababbin malamai 3,000, sannan ta ƙara ɗaukar malamai 4,200 a matakin sakandare, lamarin da ya kai sama da malamai 10,000 da aka ɗauka cikin ƴan watanni.
Gwamnan ya kuma ce an ƙarfafa sa ido a makarantu da tuntubar iyaye ta hanyar ba da ƙarfi ga kwamitocin kula da makarantu (SBMCs) da ƙirƙirar kungiyoyin iyaye mata.
SBMCs suna bibiyar halartar malamai, yayin da kungiyoyin mata ke tabbatar da ɗalibai na zuwa makaranta, matakin da gwamnan ya ce ya inganta ilimin yara sosai.

Source: Getty Images
An tsoma karatun allo a cikin na zamani
Bugu da ƙari, jihar ta haɗa kai da kamfanin NewGlobe daga Birtaniya domin inganta karatun yara da kuma kwarewarsu a lissafi.
Gwamna Namadi ya ce wannan haɗin gwiwar ya riga ya fara samar da “sakamako mai ban mamaki” a makarantun firamare.
Gwamnatin ta haɗa tsarin karatun allo cikin ilimin zamani ta hanyar gyara makarantun Tsangaya da kuma gina manyan makarantu uku na kwana, kowanne na ɗaukar ɗalibai 1,500.
Makarantun suna haɗa koyar da Alƙur’ani da karatun boko da sana’o’i, tare da noma abincinsu da kansu, don dorewarsu.
Gwamna Namadi ya sallami hadiminsa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Jigawa, Umar Namadi, ya yanke hukuncin korar daya daga cikin masu ba shi shawara na musamman.
Gwamna Umar Namadi ya kori Rabi'u Garba Kaugama daga kan mukaminsa na mai ba shi shawara na musamman kan harkokin majalisar tarayya.
Bayan korar hadimi nasa, mai girma gwamnan ya kuma umarce shi da ya dawo da dukkanin kayayyakin gwamnati da ya san suna hannunsa.
Asali: Legit.ng

