Mata Mai Albashin N30,000 Ta Fadi Dalilin Maida N4.8m da aka Yi Kuskuren Turawa a Asusunta

Mata Mai Albashin N30,000 Ta Fadi Dalilin Maida N4.8m da aka Yi Kuskuren Turawa a Asusunta

  • Wata baiwar Allah a jihar Borno mai suna Fa'iza AbdulKadir ta bayar da mamaki matuka bayan an aika mata N4.8m bisa kuskure
  • Matar da ke aikin shara a wata cibiyar lafiya a jihar ta bayyana cewa har kasa barci ta yi a lokacin da kudin ke asusunta
  • Jama'a sun bayyana cewa dama matar da ke karbar albashin N30,000 ta fita daban, kuma a haka ta ke rainon yaranta biyar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno – Wata baiwar Allah mai shara a cibiyar kiwon lafiya, Faiza Abdulkadir ta sake nuna wa duniya cewa har yanzu akwai sauran masu gaskiya.

Fa'iza da ke karɓar albashin N30,000 a wata, ta mayar da N4.8m da aka tura cikin asusun bankinta da kuskure a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Kara karanta wannan

Kano: Jami'an NDLEA sun cafke matashi da tramadol 7,000 daga Legas

Fa'iza ta mayar da kudin wasu bayin Allah
Taswirar jihar Borno Hoto: Legit.ng
Source: Original

Dan uwan matar, Ibrahim Muhammad AbdulRahman ne ya tabbatar da haka a shafinsa na Facebook, ya ce duk da kuncin rayuwa da ta ke fama da shi, ba ta rike kudin ba.

Fa'iza ta maida kudin wasu bayin Allah a Borno

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa da take magana da manema labarai, Faiza ta bayyana cewa tsoron Allah ne ya sa ta ki rike kuɗin da ba nata ba.

Ta shaida cewa:

“Kuɗin ba nawa ba ne. Na mayar da shi domin samun kwanciyar hankali, da kuma kauce wa fushin Allah a ranar lahira."

Faiza ta ce ta shafe kwanaki uku tana bin duk wata hanya da ta dace a bankinta kafin ta kammala mayar da kuɗin ga mai shi.

Baiwar Allah ta bayyana cewa:

“Ban huta ba cikin waɗannan kwanaki uku. Har ma ban iya cin abinci da kyau ba sai ranar da na tabbatar da cewa na maida da kuɗin."

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya kusan 5,000 na kokuwar samun gurbin aiki 98 a Taraba

Borno: Ma'aikatan banki sun jinjinawa Fa'iza

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an banki da maƙwabta sun bayyana Faiza a matsayin mace mai gaskiya da rikon amana, duk da cewa tana rayuwa ne a kan albashin N30,000 tare da ‘ya ’yanta biyar.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum
Hoton gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum Hoto: The Governor of Borno State
Source: Twitter
“Ba mu yi mamaki ba, saboda yadda take da tarbiyya da kuma yadda take rainon ‘ya’yanta. Mace ce mai ɗabi’a da rayuwa cikin sauƙi tare da ‘ya’yanta biyar."

Wani ma’aikacin banki ya ce abin da Faiza ta yi ya burge su ƙwarai, musamman ganin halin da take ciki amma duk da haka ta zabi yin adalci da tsoron Allah.

Yanzu haka, labarin gaskiya da rikon amana na Faiza Abdulkadir ya zama abin koyi ga jama’a da dama, musamman a lokacin da ƙalubale na tattalin arziki ke jefa mutane cikin halin wuya.

An hallaka kwamandojin Boko Haram a Borno

A baya, kun ji cewa Dakarun rundunar Operation Hadin Kai a Arewa maso Gabas sun samu nasarar halaka manyan kwamandojin Boko Haram guda biyu tare da wasu mayakan 11.

Kara karanta wannan

Hafsan hafsoshi ya bukaci 'yan Najeriya su dauki makamai? Hedkwatar tsaro ta yi bayani

Rahotanni sun ce sojojin sun tarwatsa ’yan ta’addan ne a garuruwan Bitta da Wulgo, bayan sun yi ƙoƙarin kutsawa unguwanni a daren Alhamis 21 ga watan Agusta da kuma Juma’a 22 ga watan Agusta, 2025.

Kwamandan rundunar, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ya ce dakarun kasa da na sama sun haɗa kai wajen kai farmaki wanda ya ɗauki sa’o’i kafin a murkushe ’yan ta’addan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng