Asiri Ya Tonu: NNPCL Ya Gano Hannun Kungiyoyin Kasashen Waje a Satar Man Najeriya

Asiri Ya Tonu: NNPCL Ya Gano Hannun Kungiyoyin Kasashen Waje a Satar Man Najeriya

  • Kamfanin NNPCL ya bayyana cewa ya kusa cimma kashi 100 na samar da danyen mai sakamakon haɗin kai da hukumomin tsaro
  • Bashir Bayo Ojulari ya ce a baya kudin shigar man Najeriya ya ragu saboda satar mai, fasa bututu da gina haramtattun matatu a kasar
  • Ya jaddada cewa barazanar satar mai ta haɗa da ƙungiyoyin ƙetare, don haka akwai bukatar ƙarfafa haɗakar tsaro a fadin Afirka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya bayyana cewa yana kusantar cimma kashi 100 na iya samar da danyen mai bayan haɗin gwiwa da hukumomin tsaro.

Shugaban NNPCL, Bashir Bayo Ojulari, ya bayyana haka a wajen buɗe taron farko na shugabannin tsaron ƙasashen Afirka, a ranar Litinin a Abuja.

Shugaban NNPCL ya ce kamfanin ya kusa cimma kashi 100 na samar mai a Najeriya
Shugaban kamfanin NNPCL, Bashir Bayo Ojulari yana jawabi a taron shugabannin tsaron kasashen Afrika a Abuja. Hoto: @nnpclimited
Source: Twitter

Tasirin tsaro ga samar da mai a Najeriya

Kara karanta wannan

Makari: An fara ruguza yunkurin hada kai tsakanin malaman Izala da Darika a Najeriya

Bayo Ojulari ya ce wannan ci gaba ya samo asali ne daga haɗin kai na tsawon lokaci tsakanin masana’antar mai da iskar gas da hukumomin tsaron Najeriya, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A 'yan kwanakin baya, kudin shiga daga bututun mai da tashoshin jiragen ruwa sun ragu sosai, har ya taba sauka zuwa kashi 20 zuwa 30 kacal.
“Wannan shi ne lokacin da lalata bututun mai, satar danyen mai, haramtattun matatun mai da cin amanar kasa suka yi yawa a kasar.
“Yau zan iya bugn kirji, in shaida wa duniya cewa samarwar da mai a Najeriya yanzu ya kai kusan kashi 100.
“Wannan ya biyo bayan amfani da ƙwarewa, da kuma haɗin gwiwar hukumomin tsaro da na leken asiri, musamman wajen daidaita al’amura a yankin Neja-Delta."

- Shugaban NNPCL, Bashir Bayo Ojulari.

Kungiyoyin kasashen waje na satar mai

Ojulari ya bayyana cewa kamfanin ya shaida tasirin ayyukan soji kai tsaye, matakan leken asiri, da sintirin haɗin gwiwa wajen kare muhimman kayayyakin makamashi.

Jaridar The Cable ta rahoto Ojulari ya kara da cewa, wannan nasara ta samu ne bisa ƙoƙari na musamman da gwamnatin Najeriya, rundunar soji da jami'an leken asiri.

Kara karanta wannan

Yaki da zaman banza: Za a koya wa matasa miliyan 1.5 sana'o'i a Kano

Ya jaddada cewa barazana ga kayayyakin makamashi ba ta tsaya ga cikin gida kawai ba, domin akwai manyan ƙungiyoyin kasashen ƙetare masu amfani da gibin tsaron ƙasa, don satar mai da sauran haramtattun ayyuka.

Bayo Ojulari ya yi kira da a ƙara haɗin kai a tsaron iyakokin kasa a nahiyar Afirka, yana mai cewa dole ne a kare makamashi daga kungiyoyin kasashen waje masu satar mai.

NNPCL ya ce kungiyoyin kasashen waje na da hannu a satar mai a Najeriya
Shugaban kamfanin NNPCL, Bashir Bayo Ojulari yana jawabi a taron shugabannin tsaron kasashen Afrika a Abuja. Hoto: @nnpclimited
Source: Twitter

NNPCL ya nemi hadin kan kasashen Afrika

Shugaban NNPCL ya ci gaba da cewa:

“Yana da kyau mu yawaita gudanar da tarurrukan irin wannan domin inganta haɗin kai ta fuskar dabaru, tsari da gudanar da aiki a Afrika.
“A tare ne zamu iya kare albarkatun Afirka, mu ƙarfafa zaman lafiya, mu samar da yanayin ci gaba da walwala ga al’ummarmu."

Ya kuma sake tabbatar da cewa NNPCL zai ci gaba da tallafawa soji da hukumomin leken asiri, yana mai cewa bangaren mai da iskar gas na Najeriya zai ci gaba da taimaka wa shirye-shiryen tsaro a Afrika.

Ojulari ya kawo karshe jita-jitar barin NNPCL

A wani labarin, mun ruwaito cewa, an yi ta yada jita-jita kan cewa shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Bayo Ojulari ya yi murabus.

Kara karanta wannan

"An yaudari 'yan Najeriya": Kungiya ta kinkimo aiki kan takarar Jonathan a 2027

Jita-jitar da aka yada, ta sanya har EFCC da DSS sun fito sun musanta tilastawa Ojulari yin murabus baya an yi zargin cewa akwai hannunsu a ciki.

A ranar Litinin, 4 ga watan Agustan 2025, jita-jitar ta fara mutuwa bayan da aka ga shugaban na kamfanin NNPCL ya shiga ofis domin ci gaba da gudanar da ayyukansa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com