Lokaci Ya Yi: Fitacciyar Yar Wasan Barkwanci Ta Rasu a 'Taron Matar Gwamna' a Najeriya

Lokaci Ya Yi: Fitacciyar Yar Wasan Barkwanci Ta Rasu a 'Taron Matar Gwamna' a Najeriya

  • An shiga jimami a yankin karamar hukumar Ugwunagbo da ke jihar Abia bayan mutuwar yar wasan barkwanci a wurin taro
  • Rahotanni sun nuna cewa yar wasan ta yanke jiki ta fadi ne tana tsakiyar nishadantar da mutane a wurin taron yau Litinin
  • Rundunar yan sanda ta ce har yanzu ba ta samu rahoton faruwar lamarin a hukumance ba, yayin da jama'a ke dakon karin bayani

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Abia - Fitacciyar mai rawar barkwanci da nishadantar da al'umma, Mrs. Nwandinma Dickson, wadda aka fi sani da “Nwayi Garri,” ta mutu a ranar Litinin.

Mai wasan barkwancin ta gamu da ajali ne bayan ta fadi tana cikin wasa a taron da aka shirya a karamar hukumar Ugwunagbo.

Yar wasata mutu a wurin taro a Abia.
Hoton marigayi mai wasan barkwanci a Abia, Nwayi Garri Hoto: Bright Destiny
Source: Facebook

Jaridar Punch ta ce marigayiyar mai shekaru 65, ‘yar asalin garin Oza Umuebukwu da ke yankin Nneji a Ugwunagbo ce a jihar Abia.

Kara karanta wannan

"Rashin tausayi" ADC ta caccaki gwamnonin PDP, ta fadi kuskuren da suka yi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanai sun nuna cewa ta shirya yin rawa da wasan kwaikwayo a babban taron da ake sa ran matar gwamnan jihar Abia, Priscilla Chidinma Otti, za ta halarta.

Rahotanni sun nuna cewa matar gwamnan ce ta dauki nauyin shirya wannan taro a garin Ugwunagbo, sai dai ya rikide zuwa alhini.

Yadda yar wasar ta mutu a taro a Abia

An ce matar ta sanya kayan wasan, tana yawo a rumfuna daban-daban tana gaisawa da jama’a tare da nishadantar da su da irin salon ta na rawa, yayin da ake jiran zuwan babbar bakuwa, Misis. Otti.

Shaidu sun bayyana cewa tana tsakiyar rawar da take yi ne kwatsam ta tsaya, sai kuma ta durkushe, lamarin da jama’a suka dauka a matsayin wani bangare na wasan.

“Lokacin da ta tsaya cak, jama’a sun dauka wani salo ne, suka ci gaba da tafi. Sai kawai ta fadi, mutane suka yi dariya suna tunanin wasa ne.

Kara karanta wannan

Kwale kwale ya kife da mutanen da ke tserewa harin 'yan bindiga a Sokoto

"Amma daga bisani lokacin da mutane suka ga ta jima ba ta tashi ba, sai aka kai mata dauki, nan fa suka ga tana fitar da kumfa a baki,” in ji wani shaida.

An garzaya da yar wasar zuwa asibiti

Shugaban karamar hukumar Ugwunagbo ya shiga cikin lamarin, ya dauke ta da motarsa zuwa asibiti, amma likitoci sun tabbatar da rasuwarta

‘Yan uwanta sun ce a farko marigayiyar ta nuna ba ta son zuwa taron, amma daga baya ta yanke shawarar tafiya saboda alƙawarin da ta dauka, rahoton Daily Post.

Taswirar Abia.
Taswirar jihar Abia da ke Kudu maso Gabashin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ana tunawa da Nwayi Garri a matsayin mai sa mutane farin ciki da gudummawar da ta bayar ga al’adun gargajiya a yankin.

A halin yanzu dai al’umma na jiran karin bayani kan abin da ya haddasa mutuwar fitacciyar mai wasan barkwancin daga hukumomi.

Hukumomi ba su fitar da wata sanarwa ba tukuna, sai dai jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, DSP Maureen Chinaka, ya ce ba a kawo masu rahoto a hukumance ba.

Fitaccen jarumin Nollywood, Adibie ya mutu

A wani labarin, kun ji cewa jarumin masana'antar Nollywood , Fabian Adibie ya rasu yana da shekara 82 a duniya bayan fama da jinya.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye: Mutane 17 yan gidan sarauta sun fara neman karagar Sarki bayan ya rasu

Mutuwar dattijon ta yi matukar taba mutane musamman abokan aikinsa a masana'antar Nollywood duba da irin girman da yake da shi a idonsu.

Adibie ya yi fice wajen fitowa a fina-finan Nollywood na gargajiya, inda ya zama ɗaya daga cikin fitattun jaruman da ake ganin girmansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262