'Lokaci Ya Yi da Za a Dauki Mataki,' ACF Ta Shiga Takaicin Yadda ake Zubar da Jinin 'Yan Arewa

'Lokaci Ya Yi da Za a Dauki Mataki,' ACF Ta Shiga Takaicin Yadda ake Zubar da Jinin 'Yan Arewa

  • Kungiyar ACF ta nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a Arewa da yadda ake ci gaba da kashe mutane babu kakkautawa
  • Shugaban ACF, Cif Mamman Osuman, ya ce yankin na fama da asarar rayuka da bala’o’i iri iri, yayin da jama'a su ka rasa yadda za su yi
  • Kungiyar ta bayyana cewa lokaci ya wuce da jama'a za su rufe idanunsu kamar ba su ganin yadda ake salwantar da rayukan jama'a ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta bayyana damuwa matuƙa kan yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a Arewacin Najeriya.

Kungiyar ta ce ta’addanci, garkuwa da mutane, da kuma wasu miyagun laifuffuka sun ruguza al’ummomi tare da jefa iyalai cikin baƙin ciki.

Kara karanta wannan

Kano: Jami'an NDLEA sun cafke matashi da tramadol 7,000 daga Legas

ACF ta ce bai dace a bar yan ta'adda na kashe jama'a ba
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Ajuri Ngalela
Source: Facebook

PRNigeria ta wallafa cewa Shugaban kungiyar, Cif Mamman Osuman (SAN) ne ya bayyana haka a yayin taron kwamitin zartarwa na ƙasa karo na 78 na ACF da aka gudanar a sakatariyar kungiyar da ke Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Arewa na cikin tashin hankali,' ACF

Shugaban kungiyar ACF, Cif Mamman Osuman (SAN) ya bayyana cewa bai kaata a ci gaba da zuba idanu ana kashe jama'a kamar kiyashi ba a yankin.

A cewarsa:

“Wannan lokaci ne mai wahala da ba a saba gani ba, inda siyasa, cin amana, laifuffuka, da masifu iri iri ke hallaka mutanenmu. Mun rasa yara, matasa, mata da dattawa — ba wai kawai sakamakon masifu daga Allah, kamar ambaliya ba, har ta miyagun ayyukan 'yan ta’adda, ’yan fashi, barayi da ’yan bindiga.”

Ya jaddada cewa wajibi ne iyalai da al’ummomin Arewa su rungumi haɗin kai da tsaro tare da yin tunani mai zurfi kan nema wa kansu mafita.

Kara karanta wannan

'Ka dawo gida da gaggawa: An buƙaci Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci a jihohin Arewa 2

Shugaban kungiyar, Cif Mamman Osuman (SAN) ya gargadi jama’a kada su zauna a gefe ko su rufe idanu kamar ba su ganin abin da ke faruwa.

ACF ta yi jimamin rasuwar shugabannin Najeriya

A yayin taron, kungiyar ta yi ta’aziyya kan rasuwar manyan shugabannin Arewa da suka hada da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Sauran sun hada da tsohon shugaban Kotun Ƙoli Mai Shari’a Mohammed Uwais, Farfesa Jubril Aminu, Cif Audu Ogbeh da kuma fitaccen attajiri, Alhaji Aminu Dantata.

ACF ta yi jimamin rasuwar Muhammadu Buhari
Hoton tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari Hoto: Bashir Ahmad
Source: Twitter

Shugaban ACF, Osuman, ya tabbatar da cewa kungiyar za ta ci gaba da kare muradun Arewa a cikin tsarin Najeriya guda.

Haka kuma, kwamitin ya yi nazari kan shirin bikin cika shekara 25 da ACF za ta gudanar a watan Oktoba.

Taron ya kuma samu gabatar da rahoto kan halin da kasa ke ciki wanda daga ƙarshe za a fitar da sanarwa ta bakin mai magana da yawun kungiyar, Farfesa Tukur Baba.

ACF ta fadi sharadin goyon bayan dan takara

A baya, mun wallafa cewa Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta fusata a kan batun da jami’in gwamnatin tarayya, George Akume, a kan babban zaben 2027 da ke karatowa.

Kara karanta wannan

'Da 'yar matsala,' An fara magana kan bai wa fursunoni damar yin zabe daga magarkama

Jami’in hulda da jama’a na ACF, Farfesa Tukur Muhammad Baba, ya bayyana cewa ba yanzu lokaci ba ne da ya dace a fara maganganu a kan yadda za a gudanar da zaben.

Maimakon haka, ya bukaci gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta fi mayar da hankali wajen tabbatar da jin daɗin ‘yan ƙasa da warware matsalolin da ake fuskanta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng