'Yan Najeriya kusan 5,000 na Kokuwar Samun Gurbin Aiki 98 a Taraba
- Mutane akalla 4,489 ne su ka nemi aiki a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Bali, da ke jihar Taraba bayan ta sanar da cewa za ta dauki ma'aikata
- Shugaban kwalejin, Dr. Mohammed Usman ne ya sanar da haka duk da cewa sun tallata guraben aikin da ba su kai 100 ba
- Ya bayyana cewa duk da yawan wadanda ke neman guraben aikin, ya ce za su yi zama na tsanaki domin tantance mutanen da su ka dace
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Taraba – Hukumar Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Bali, Jihar Taraba ta karɓi takardun neman aiki daga mutane akalla 4,489 a makarantar.
Wannan na zuwa ne bayan kammala makarantar ta buga bukatar neman ma'aikata, inda ta bayyana cewa akwai guraben mutum 98 da za a dauka aiki.

Kara karanta wannan
Mazauna Katsina sun karyata ikirarin gwamnati na kubutar da su daga hannun 'yan ta'adda

Source: Twitter
Daily Trust ta wallafa cewa Shugaban makarantar, Dr. Mohammed Usman, ya bayyana wannan adadi ne yayin da yake gabatar da jawabi a gaban kwamitin gudanarwa na kwalejin.
Yadda jama'a ke neman aiki a Taraba
Trust Radio ta ruwaito cewa Dr. Muhammad Usman ya ce za su yi aikin duba takardun da aka aika masu a tsanake domin tantance wadanda su ka cancanta.
Shugaban makarantar ya ƙara da cewa duk wanda aka zaɓa daga cikin masu neman guraben aikin, za a sanar da shi ta hanyar adireshin da ya bayar ko kuma ta lambar waya da aka saka a takardun neman aiki.

Source: Original
Ya jaddada cewa makarantar ba za ta yi sakaci ba wajen tabbatar da cewa wadanda suka cancanta kadai za su shiga jerin wadanda za a kira.
Wannan, a cewarsa, zai taimaka wajen tabbatar da samun ma’aikata nagari da za su iya bayar da gudunmuwa wajen bunkasa makarantar.

Kara karanta wannan
'Da 'yar matsala,' An fara magana kan bai wa fursunoni damar yin zabe daga magarkama
An yabi shugaban kwalejin na Taraba
Kwamitin gudanarwa na makarantar ya yaba da yadda shugabancin makarantar ke tafiyar da duk wani aiki bisa ƙa’ida da kuma bin umarnin ma’aikatar ilimi ta tarayya da dokokin kwalejin.
Mahalarta taron sun kuma jaddada bukatar gudanar da tsarin daukar ma’aikata bisa gaskiya da adalci, domin karfafa gwiwar jama’a da masu neman aiki kan yadda ake tafiyar da harkokin makarantar.
Wannan mataki, kamar yadda kwamitin ya bayyana, na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen ciyar da makarantar gaba tare da samar da sahihan ma’aikata.
Ana sa ran daukar sababbin ma'aikatan bisa tsari zai taimaka matuka wajen inganta tsarin koyarwa da gudanarwa a makarantar.
Taraba: Majalisar Musulmi ta fusata da 'Kauyawa Day'
A wani labarin, mun wallafa cewa Majalisar Musulmi ta Taraba ta haramta shagulgulan "Kauyawa Day" da "Ajo" a Jalingo tare da sanar da tsauraran matakan karya dokar.
A cikin hudubar da aka yi a masallatai a fadin garin ranar Juma’a, limamai sun gargadi Musulmi a kan gudanar da shagulgula a tsarin da ya saba da koyarwar addinin Musulunci.
Imam Tajudeen Nuhu, limamin babban masallacin Mayo Gwoi a Jalingo, ya bayyana cewa duk wanda aka samu da karya dokar, za a kaurace wa bukukuwa ko jana'iza a gidansa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng