Mazauna Katsina Sun Karyata Ikirarin Gwamnati na Kubutar da Su daga Hannun 'Yan ta'adda

Mazauna Katsina Sun Karyata Ikirarin Gwamnati na Kubutar da Su daga Hannun 'Yan ta'adda

  • Wasu daga cikin al’ummar Mantau a Katsina sun ce ‘yan bindiga sun sako mutane 76 ba tare da an gindaya masu wani sharadi ba
  • Sun bayan haka ne bayan gwamnati ta ce dakarun sojin sama sun yi luguden wuta suka kubutar da mutanen daga hannun 'yan ta'adda
  • Amma wasu daga cikin wadanda aka sako karyata haka, inda su ka ce 'yan ta'addan ne su ka tausaya masu, sannan aka sako su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina – Al’ummar kauyen Mantau da ke ƙaramar hukumar Malumfashi a jihar Katsina, inda hare-haren ‘yan bindiga suka addabi mutane, sun ja da gwamnati.

Sun karyata ikirarin da gwamnatin Umaru Dikko Radda ta yi na cewa dakarun sojin Najeriya ne su ka samu nasarar kwato wasu mutum 76 da aka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Bayan korafe korafe, Tinubu ya dauki alƙawari bayan kisan masallata a Katsina

Rundunar sojin saman Najeriya
Wasu daga cikin jami'an sojin Najeriya (H), Jiragen sojin saman Najeriya suna shawagi (D) Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Arise News ta wallafa cewa mazauna yankin sun ce fitaccen shugaban ‘yan bindiga mai suna Babaro ne ya sako mutanen ba tare da wani sharadi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Katsina ta yi ikirarin ceto jama'a

Daily Post ta wallafa cewa gwamnatin jihar Katsina ta ce an ceto wasu mutane da aka yi garkuwa da su bayan dakarun rundunar sojin saman Najeriya sun ragargaza mafakar Babaro.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Dr. Nasir Mu’azu, ya tabbatar da cewa sojojin sama sun kai farmaki a cibiyar Babaro da ta dade tana zama tushen tsoro ga al’ummomin yankin.

Ya ce:

“Da safiyar Asabar, dakarun NAF sun kai hari na musamman a tsaunin Pauwa, inda aka kubutar da mutane 76 daga ciki har da mata da yara. Amma abin bakin ciki, yaro guda ya rasa ransa a yayin harin."

Ta ce waɗanda aka kubutar sun haɗa da duka mutanen da aka yi garkuwa da su a lokacin harin da aka kai Unguwar Mantau, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 50.

Kara karanta wannan

'Mun sha azaba,' Adadin bayin Allah da 'yan ta'adda su ka hallaka a Katsina ya haura 55

Katsina: Wadanda su ka kubuta sun yi bayani

Sai dai, wasu daga cikin wadanda aka sako sun yi ikirarin cewa ba aikin sojoji ba ne ya ba su damar shakar iskar 'yanci ba.

Guda daga cikin mutanen mai suna Firdausi Auwal, ta ce:

“Sun ce yaran da ke tare da mu suna ta kuka suna damunsu, shi ya sa suka sake mu. Suka raka mu ta cikin daji zuwa babban titin Kankara sannan suka umarce mu da mu tafi. Mun ga jirgin sama yana shawagi a lokacin, amma ba ta hannunsu aka ceto mu ba.”
Mazauna Katsina sun koka ga gwamanti
Gwamnan jihar Katsina, Umaru Dikko Radda Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Source: Twitter

Haka nan, Fatima Haliru, wadda aka kama tare da jaririyarta mai watanni uku, ta ce ‘yan bindigar suna da makamai da kayan sadarwa.

Ta ƙara da cewa:

“Sun sako mu ne saboda tausayi ga ‘ya’yanmu da kananan yara, ba wai saboda harin sojoji ba.”

Fatima ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar da su ƙara tura jami’an tsaro zuwa Mantau da sauran ƙauyukan makwabta domin hana sake afkuwar irin wannan mummunan lamari.

Kara karanta wannan

Masu sayen baburan sata a Kano sun fada tarkon 'yan sanda, an kama mutum 10

Adadin Katsinawan da aka kashe ya karu

A wani labarin, kun ji cewa al’ummar Gidan Mantau da ke ƙaramar hukumar Malumfashi, jihar Katsina, sun shiga cikin matsanancin tashin hankali bayan mummunan harin ‘yan ta’adda.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an gano gawarwaki sama da 50 a yankin, yayin da jami’an tsaro da mazauna kauyen ke ci gaba da bincike don gano mutanen da aka nema aka rasa.

Wadanda suka tsira daga harin sun bayyana irin azabar da suka sha a hannun maharan, inda suka ce rayuwarsu ta shiga cikin hali na rashin tabbas a yanzu haka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng