Sheikh Makari na Kokarin Hada kan Musulmi, Ya Gana da Izala, Darika, Salafiyya da Ahmad Gumi

Sheikh Makari na Kokarin Hada kan Musulmi, Ya Gana da Izala, Darika, Salafiyya da Ahmad Gumi

  • Tawagar Malamai da kungiyoyi ƙarƙashin jagorancin Farfesa Ibrahim Makari ta kai ziyara ga manyan shugabannin addini
  • An jaddada cewa haɗin kan musulmi ba yana nufin barin mazhaba ko fahimta ba ne, illa kawar da husuma da kafirta juna
  • Shugabannin da aka ziyarta sun nuna goyon baya ga wannan yunƙuri na samar da murya guda ga al’ummar musulmi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Babban yunƙuri na haɗa kan al’ummar musulmi a Najeriya ya samu sabon salo, bayan da tawagar gamayya ta malamai da kungiyoyi masu fafutukar haɗin ta fara aiki.

Malaman addini, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Ibrahim Ahmad Makari ta fara ziyarar tuntubar shugabannin addini a sassa daban-daban na ƙasar.

Lokacin da tawagar Farfesa Makari ta ziyarci Izala da Sheikh Gumi
Lokacin da tawagar Farfesa Makari ta ziyarci Izala da Sheikh Gumi. Hoto: Prof. Ibrahim Maqari|Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Farfesa Makari ya wallafa a Facebook cewa wannan ƙoƙari na gudana ne ƙarƙashin inuwar Babban Majalisar Malamai ta ƙasa.

Kara karanta wannan

'Da 'yar matsala,' An fara magana kan bai wa fursunoni damar yin zabe daga magarkama

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an fara aikin ne domin neman kawar da gaba, husuma da kafirta juna, tare da haɗa ƙarfi da yunkuri wajen kare martabar addini da wanzar da fahimtar juna.

Tawagar Ibrahim Makari ta ziyarci malamai

A ranar Asabar 23 ga Agusta, 2025, tawagar ta kai ziyara ga kungiyoyi da dama ciki har da Fityanul Islam.

Haka zalika ta ziyarci Jama’atu Izalatul Bid’ah wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), shugaban Majlisus-Shura na ɗariƙar Tijaniyya ta ƙasa, da kuma kwamitin limamai na Birnin Tarayya Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa shugabannin da aka ziyarta sun bayyana jin daɗinsu tare da nuna goyon bayansu ga wannan yunƙuri.

Sun bayyana cewa haɗin kai da kawar da husuma wani ɓangare ne na ayyukan da suke gudanarwa a cikin addini tun da dadewa.

Dalilin kokarin hada kan Musulmai

A jawabin da aka bayyana yayin ziyarar, an jaddada cewa wannan yunƙuri bai yi nufin raba ɗalibai da malaman su ko barin fahimta da mazhabar da kowanne ya gamsu da ita ba.

Kara karanta wannan

Majalisar Musulmi a Taraba ta zafafa hukunci a kan masu 'kauyawa day' da ajo

Farfesa Makari ya fayyace cewa babu laifi wajen tattauna mas’alolin saɓani tsakanin malamai muddin an girmama juna kamar yadda shari’a ta tanada.

Malamin ya jaddada cewa manufar ita ce samar da ƙasa da al’ummar musulmi masu murya guda wajen isar da saƙon addini cikin hikima da haɗin kai.

Tawagar Farfesa Makari tare da Sheikh Ahmad Gumi
Tawagar Farfesa Makari tare da Sheikh Ahmad Gumi. Hoto: Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Tawagar Makari ta gana da Ahmad Gumi

Daga cikin shugabannin da tawagar ta gana da su har da babban malamin addini, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi.

Malamin ya wallafa a Facebook cewa sun tattauna muhimmancin samar da haɗin kai da murya ɗaya ga al’ummar musulmi a Najeriya.

Tawagar ta bayyana cewa wannan tafiya bata da alaƙa da wata kungiya ta siyasa ko wata takamanman fahimta ta addini, sai dai samar da mafita ga al’umma.

Gwamna Buni ya gana da 'yan Darika

A wani rahoton, kun ji cewa tawagar malamai da jagororin Darikar Tijjaniyya sun gana da gwamnan Yobe, Mai Mala Buni.

Sheikh Ibrahim Shehu Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewa sun ziyarci Yobe ne domin yin gagarumin bikin Mauludi.

Gwamna Mai Mala Buni ya bukaci malaman da su yi wa shugaba Bola Tinubu da sauran shugabanni addu'ar samun nasara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng