'Iya Kudinka, Iya Gaskiyarka,' Sarkin Musulmi Ya ce Mai Dukiya ke Sayen Adalci a Najeriya
- Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ce adalci a Najeriya ya zama na mai kuɗi yayin da talaka ke fama da kunci
- Ya bayyana cewa yanzu masu kuɗi ne kawai za su iya samun adalci a kotunan kasar nan, tare da gargadin lauyoyi kan illar haka
- Sarkin Musulmin ya bayyana takaicin yadda bangaren shari'a ya gama tabarbare wa a Najeriya tare da watsi da hakkin jama'a
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Enugu – Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiya na Arewacin Najeriya, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya ce akwai matsala a ɓangaren shari'a.
Ya yi gargadi cewa adalci a Najeriya yana ruguje wa saboda yanzu masu kuɗi ne kawai ke iya sayen adalci a gaban alkalai.

Kara karanta wannan
'Da 'yar matsala,' An fara magana kan bai wa fursunoni damar yin zabe daga magarkama

Source: Facebook
Channels TV ta wallafa cewa Sarkin Musulmi ya bayyana hakan a lokacin da ya yi jawabi a taron shekara-shekara na ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA) da aka gudanar a Enugu ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin Musulmi ya ce akwai matsala a shari'a
Tribune Online ta wallafa cewa Alhaji Sa'ad ya ce yadda talaka ke gaza samun adalci a kotuna abin damuwa ne matuka da ke buƙatar gyara.
Ya ce:
“A yau, adalci ya zama abin sayar wa, inda talakawa ke zama waɗanda ake zalunta, yayin da masu kuɗi ke aikata laifuka iri-iri amma suna yawo a titi ba tare da hukunci ba.”
Sarkin Musulmin ya nuna damuwa cewa cin hanci da rashin adalci na lalata tsarin shari’a a fadin kasar nan.
Kiran Sarkin Musulmi ga lauyoyi
Alhaji Sa'ad Abubakar III ya yaba wa NBA bisa taron, yana mai cewa hakan na da alaƙa da gaggawar da ake da shi na buƙatar lauyoyi su tsaya kan gaskiya wajen sauke nauyin aikinsu.

Kara karanta wannan
Jerin sunaye: Mutane 17 yan gidan sarauta sun fara neman karagar Sarki bayan ya rasu
Mai alfarma Sa'ad Abubakar III ya jaddada cewa dole lauyoyi da masu ruwa da tsaki a fannin shari’a su ci gaba da tsayawa kan gaskiya domin tabbatar da adalci da daidaito a ƙasar nan. Ya ce:
“Ku yi ƙoƙari wajen tabbatar da cewa kowa, har ma waɗanda ke da iko, ya kasance ƙarƙashin doka kuma ana iya ɗaukar mataki a kansu. Idan muka yi hakan, za mu magance manyan matsalolin shugabanci da ƙasa ke fama da su.”
Ya ƙara da cewa adalci shi ne tubalin zaman lafiya a kowace al’umma, saboda haka dole a tabbatar da shi.
Ya bukaci mahalarta taron da su tattauna manyan batutuwan da su ka shafi makomar Najeriya, musamman gyaran doka domin ta dace da al’adun da adalci na zamantakewa.

Source: Facebook
Haka nan, ya yi korafi kan yadda Najeriya ke da manufofi masu kyau amma akasari ana gaza aiwatar da su.
Sarkin Musulmi ya soki shafukan sada zumunta
A baya, mun wallafa cewa Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya zargi kafafen sada zumunta da haɗin gwiwa da ƙungiyar ‘yan ta’adda don yada labaran ƙarya.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a taron kwamitin zartarwa na Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa da aka gudanar a Maiduguri, jihar Borno
A cewarsa, ya kamata hukumomin tsaro su ɗauki kafafen sada zumunta da muhimmanci kamar irin na sauran barazanar tsaro, don hana yaɗa labaran bogi da tada hankalin jama’a
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng