Kano: Rundunar Ƴan Sanda Ta Fara Binciken Wasu Jami'anta da ake Zargi da Taimakon Ɓarayi

Kano: Rundunar Ƴan Sanda Ta Fara Binciken Wasu Jami'anta da ake Zargi da Taimakon Ɓarayi

  • Rundunar ƴan sandan Kano ta fitar da sababbin bayanai kan binciken zargin cin hanci, sata da ta'amali da 'yan daba da ake yi wa wasu daga cikin jami'anta
  • Sanarwar da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Lahadi ta ce an gano ɗaya daga cikin mutanen da ake tuhuma ɗan bijilanti ne
  • CP Ibrahim Adamu Bakori ya kuma bada umarnin a sauya wurin aiki na jami’an Sheka 23, domin a samu damar gudanar da cikakken bincike a kan zargin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoRundunar ƴan sandan Kano ta ce binciken zargin cin hanci da ya shafi wani jami’in ƴan sanda da wasu mutane biyu da ake zaton suna aiki da ofishinsu na Sheka ya fara nisa.

Kara karanta wannan

Ana jimamin harbe masallata, an kama dan shekara 65 na safarar makamai

Kwamishinan ƴan sanda, Ibrahim Adamu Bakori, ya umarci gudanar da bincike mai zurfi don gano hakikanin gaskiyar zargin hada kai da 'yan daba da karbar cin hanci daga wadanda ake zargi.

An fara binciken yan sandan Kano
Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori (H), Wasu jami'an 'yan sanda (D) Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Sanarwar da Kakakin rundunar, SP Abdullah Haruna Kiyawa ya fitar a shafinsa na Facebook ta ce an gano wasu bayanai a kan mutanen da ake zargi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fara binciken 'yan sanda a Kano

Sanarwar ta ce binciken ya tabbatar da cewa mutanen biyu da ake magana a kansu ba dukkaninsu ne ƴan sanda ba.

Daya daga cikinsu na daga cikin ƴan sandan sarauniya yayin da ɗayan kuma ɗan sa-kai ne daga kungiyar bijilanti da ke taimaka wa sashen Sheka.

Sai dai, rundunar ta bayyana cewa hujjojin da mai ƙorafi ya bayar ba su wadatar ba, kuma bai tabbatar da zargin da ake yi.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Kwamishinan 'yan sanda, CP Ibahim Adamu Bakori ya umarci a kwashe jami’in da ake tuhuma da sauran jami’ai 22 daga sashen Sheka zuwa wasu wuraren aiki domin baiwa masu bincike damar samun bayanai ba tare da matsin lamba ba."

Kara karanta wannan

Masu sayen baburan sata a Kano sun fada tarkon 'yan sanda, an kama mutum 10

Zargin da ya sa ake binciken 'yan sandan Kano

Wani bawan Allah, Muhammad Sani Muhammad ya kira sunayen wadansu 'yan sanda da ya ce kowa a yankin ya san barayi ne.

Baya ga wannan, ya yi zargin cewa suna karbar 'balas' a wajen masu sayar da miyagun kwayoyi da sauran sanannun 'yan daba da barayi a yankin.

Taswirar jihar Kano
Taswirar jihar Kano Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sai dai sanarwar rundunar ta bayyana cewa binciken da aka fara, ba a kai ga gano cewa akwai kamshin gaskiya a ikirarin Muhammad Sani Muhammad ba.

Sai dai duk da haka, rundunar ta dakatar da jami'in kwastabulary da jami'in bijilantin da ake zargi da hannu a taimakon bata garin.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Hukumar ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da bada haɗin kai da sahihan bayanai da za su taimaka wajen kammala binciken cikin nasara."

Sanarwar ta ce rundunar 'yan sandan Kano za ta tabbatar da adalci bayan bin diddikin dukkanin zarge zargin da aka yiwa jami'anta.

Kara karanta wannan

Nijar: An harbe shugaban Boko Haram da ya maye gurbin Shekau har lahira

'Yan sanda sun rutsa an ta'adda a daji

A baya, mun wallafa cewa rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta yi nasarar fatattakar wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne cikin daji a karamar hukumar Shanga.

Rahotanni sun bayyana cewa a lokacin artabun, jami’an tsaro sun kashe mutum uku yayin da suka yi musayar wuta da ‘yan ta’addan, suka kuma kwato AK-47 da jigida da harsasai.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Bello M. Sani ya yabawa gaggawar kwamandan sashen Shanga da tawagarsa tare da jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin jami’an tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng