Shugaba Tinubu Ya Kadu da Allah Ya Yiwa Tsohon Gwamna kuma Jigon APC Rasuwa a Abuja
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi jimamin rasuwar tsohon gwamnan Filato na mulkin soji, Kanal Mohammed Mana (mai ritaya)
- Tinubu, wanda ake tsammanin yana Brazil bayan baro Japan, ya bayyana marigayin a matsayin jarumin soja, kuma dattijo mai kishin kasa
- Shugaban kasar ya aika sakon ta'aziyya ga yan uwa, abokan arziki sa daukacin al'ummar jihar Adamawa bisa wannan babban rashi da suka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
State House, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhini bisa rasuwar Kanal Mohammed Mana (mai ritaya), tsohon gwamnan mulkin soja a jihar Filato.
Marigayi Mohammed Mana, wanda tsohon Sanata ne mai wakiltar Adamawa ta Arewa, ya rasu da safiyar Asabar a babban birnin tarayya Abuja.

Source: Twitter
Shugaba Tinubu ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar tsohon gwamnan kuma babban jigon APC a jihar Adamawa, kamar yadda The Nation ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon Sanatan Adamawa ta Arewa ya rasu
Rahoton Daily Trust ya ce Marigayi Mana ya kasance jigo a jam’iyyar APC kuma sananne wajen bayar da gudummawa a harkokin siyasa da ci gaban al’umma.
Ya wakilci yankin Adamawa ta Arewa a Majalisar Dattawa tsakanin shekarar 2007 zuwa 2011, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa dokoki da kare muradun jama’arsa.
Har zuwa rasuwarsa, shi ne shugaban kwamitin sulhu na APC a jihar Adamawa, inda ya yi aiki tukuru wajen kawo hadin kai tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.
Tinubu ya yi alhinin rasuwar tsohon gwamna
A cikin sakon ta’aziyyar da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Asabar, Shugaba Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin dattijo mai kishin kasa.
Shugaban kasa ya ce Sanata Mohammed Mana kwararren jami’in soja ne, wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga hidimar kasa.
“Kanal Mana ya kasance mutum mai gaskiya, jarumi kuma mai kishin kasa wanda ya yi hidima ba tare da kasawa ba a kowane lokaci, lokacin yana cikin soja da bayan ya yi ritaya,” in ji Tinubu.
Shugaban ya kara da cewa gudummawar Samata Mana ga ci gaban kasa, musamman a fannin siyasa da shugabanci, za ta dade ana tunawa da su.

Source: Facebook
Shugaba Tinubu ya aika sakon ta'aziyya
“Mun yi babban rashi, daga yanzu mun rasa shawarwarin da yake ba mu irin na su na dattawa masu hangen nesa," in ji Tinubu.
Tinubu ya kuma mika ta’aziyya ga iyalan marigayin, abokansa da jama’ar Adamawa baki daya.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan marigayin, ya kuma bai wa iyalinsa hakurin jure wannan babban rashi.
Mahaifin gwamnan jihar Kogi ya kwanta dama
A wani rahoton, kun ji cewa mahaifin Gwamna Ahmed Usman Ododo na jihar Kogi, Ahmed Momohsani Ododo ya riga mu gidan gaskiya ranar Litinin da ta wuce.
Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da rasuwar mahaifin gwamnan a wata sanarwa da ta fitar, ta ce ya rasu yana da shekaru 83 a duniya.
A sanarwar da gwamnatin ta fitar, ta bayyana jimami tare da addu'ar Allah Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya kuma sanya shi a gidan Aljannah Firdaus.
Asali: Legit.ng

