Sarki Muhammadu Sanusi II Ya Gana da Obasanjo, an Yada Hotunan Haduwarsu
- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya kai ziyara jihar Lagos inda ya gana da tsohon shugaban ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo
- A wata wallafa, an nuna Sanusi II ya samu rakiyar manyan fadawa ciki har da Mai girma Wazirin Kano da Galadiman Kano
- Hakiman Kano da suka raka shi sun haɗa da Magajin Gari da Sarkin Yaƙi yayin tattaunawa da tsohon shugaban Najeriyan a Lagos
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ziyarci jihar Lagos da ke Kudancin Najeriya inda ya gana da tsohon shugaban kasa.
Sanusi II ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo a jihar a yau Asabar 23 ga watan Agustan 2025.

Source: Facebook
Sanusi II ya gana da Obasanjo a Lagos
Shafin Sanusi II Dynasty ya tabbatar haka a daren Asabar 23 ga watan Agustan 2025 da muke ciki a manhajar Facebook.
Sanarwar ta bayyana cewa basaraken ya gana da Obasanjo ne a Lagos inda suka tattauna wasu batutuwa.
An tabbatar da cewa basaraken ya samu rakiyar wasu manya a masarautar ciki har da Wazirin Kano.
Sauran sun hada da Galadiman Kano, Magajin Garin Kano da Sarkin Yaƙin Kano da sauran na kusa da basaraken.
Sanarwar ta ce:
"Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi II, ya ziyarci tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, a birnin Lagos.
"A wannan ziyara, Mai Martaba ya samu rakiyar manyan Hakiman Kano, ciki har da Wazirin Kano, Galadiman Kano, Magajin Garin Kano da Sarkin Yaƙin Kano.
Sarkin ya kai ziyarar ce a yau Asabar, 23 ga Agustan shekarar 2025 da muke ciki a Lagos."

Source: Facebook
Sarki Sanusi II ya halarci daurin aure a Ogun
Har ila yau, kafin zuwa Lagos, basaraken ya ziyarci jihar Ogun domin shaida daurin aure da liyafa a birnin Abeokuta.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta ragargaji Atiku, El Rufa'i kan wata nasarar da Tinubu ya samu
Basaraken ya samu damar halartar daurin auren Faizah Omoteniola da Abdul-Hakeem Babatunde a Abeokuta wanda aka gayyace shi.
An tabbatar da cewa bayan halartar auren da kuma liyafa ne ya wuce Lagos inda ya gana da Obasanjo.
Hakan na cikin wata sanarwa daga sahfin Sanusi II Dyansty da aka wallafa a shafin Facebook wanda ke yada abubuwan Masarautar Kano.
"Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Dr. Muhammad Sanusi II, CON, ya halarci bikin ɗaurin aure da liyafar biki na Faizah Omoteniola da Abdul-Hakeem Babatunde a Abeokuta."
- Cewar wata sanarwar
Kano: Sanusi II ya dakatar da dagaci
A baya, kun ji cewa Masarautar Kano ta sauke Mai unguwa saboda zargin karya doka, kin amsa umarnin Sarki da cin amanar al’umma wanda aka tabbatar hakan saba doka ne.
Sarkin Kano ya gargadi sauran masu rike da sarauta da su guji rashin gaskiya da neman abin hannun talakawa, domin kare martabar masarauta da kuma sauke hakkin da aka daura musu.
Masarautar ta ce ba za ta lamunci duk wani rashin gaskiya daga basarake a Kano ba da ke sabawa ka’ida da amanar da aka dora masa da cewa za a dauki tsattsauran mataki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
