Ana Fama da 'Yan Bindiga, Gwamnatin Katsina Ta Aika Sako ga Mutanen Jihar kan 2027

Ana Fama da 'Yan Bindiga, Gwamnatin Katsina Ta Aika Sako ga Mutanen Jihar kan 2027

  • Gwamnatin jihar Katsina ta jawo hankalin jama'a kan aikin yin rajistar katin zabe da hukumar INEC take yi
  • Mai ba Gwamna Dikko Umaru Radda shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Ya'u Umar Gwajo-Gwajo, ya ce yin rajistar yana muhimmanci
  • Ya bukaci jama'ar jihar da su fito yin rajistar domin samun damar shiga harkokim zabe a nan gaba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Mai ba gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Ya’u Gwajo-Gwajo, ya yi kira ga mazauna jihar da su fito don yin rajistar katin zabe.

Hadimin na Gwamna Radda, ya shawarci mutanen da suka cancanta da su karɓi katin zaɓe na dindindin (PVC) domin tabbatar da shiga harkokin zaɓe nan gaba.

An bukaci jama'a su fito yin rajistar katin zabe a Katsina
Hoton gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, yana jawabi a wajen wani taro Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a Katsina a ranar Asabar, 23 ga watan Agustan 2025, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya dauko hanyar maida Kano 'Jagaba' a yawan masu kada kuri'a a 2027

An bukaci mutane su fito rajistar katin zabe

Alhaji Ya'u Umar Gwajo-Gwajo ya yi kira ga ’yan kasa da suka cancanta da su shiga cikin shirin yin rajistar masu kada kuri’a.

Ya yi kira musamman ga waɗanda suka kai shekara 18 kwanan nan ko kuma waɗanda ke son sauya rumfunan zaɓensu, da su shiga shafin rajistar INEC na yanar gizo domin yin rijista.

Alhaji Ya'u Umar Gwajo-Gwajo ya kuma tunatar da su cewa za a fara yin rijista ta zahiri mako mai zuwa a dukkan ofisoshin INEC na jiha da kananan hukumomi, rahoton gazettngr ya tabbatar.

Hadimin gwamnan ya jaddada muhimmancin fitowar mutane yin rajista, saboda matsayin da jihar take da shi na kasancewa ta biyar da ke da mafi yawan masu rijista a kasar nan.

"Katsina ce jiha ta uku mafi yawan jama’a a Najeriya. Don haka, ya kamata mu yi kokari mu zama jiha ta uku da ta fi yawan masu rijista."

Kara karanta wannan

Bayan dawowa daga London, Ganduje ya bi sawun Shettima da Zulum wajen ta'aziyya Kogi

"Wannan kuwa ba zai yiwu ba sai idan dukkan manya masu shekaru 18 da sama da hakan sun shiga yin rajista."

- Alhaji Ya'u Umar Gwajo-Gwajo

Yayin da yake yin nuni da bayanan INEC, Alhaji Ya'u Umar Gwajo-Gwajo ya bayyana cewa fiye da mutane 505,000 sun riga sun yi rajista a fadin kasar nan cikin kwanaki biyar kacal na fara aikin.

Gwamnatin Katsina na son mutane su yi rajistar katin zabe
Hoton gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Hadimin Radda ya jawo hankali kan zabe

Ya yi kira ga masu rike da mukaman siyasa, ƙungiyoyin farar hula, sarakunan gargajiya, kafafen yaɗa labarai da duk masu ruwa da tsaki da su wayar da kan jama’a tare da karfafa su kan fitowa yin rajista.

Haka kuma ya shawarci waɗanda tuni suke da katin PVC da kada su sake yin rajista don guje wa maimaitawa.

Gwamnan Katsina ya nada hadimai

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya nada manyan mataimaka na musamman.

Gwamna Radda ya nada mutane 15 wadanda suka fito daga sassa daban-daban na jihar domin su yi aiki tare da shi.

Hakazalika, Gwamna Radda, ya nada Rabiu Aliyu Kusada, a matsayin shugaban hukumar otel na Katsina

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng