Jam'iyyar ADC Ta Yi Martani bayan an Zarge Ta da Yaudarar 'Yan Najeriya
- Jam'iyyar ADC ba ta ji dadin kalaman da Sanata Yusuf Datti Baba-Ahmed ya yi ba, inda ya zarge ta da yaudarar 'yan Najeriya
- ADC ta bayyana cewa ko kalaman tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasan, wani ra'ayi ne kashin kansa
- Sai dai, duk da sukar da ya yi mata, ta bukaci ya shigo cikin hadaka don ya ba gudunmawarsa wajen ceto Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC ta mayar da martani kan kalaman da ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya yi.
Jam'iyyar ta bayyana caccaka da zargin da ya yi wa hadaka a matsayin “ra’ayinsa na kashin kai” wanda ba shi ne ainihin abin ADC ta sanya a gaba ba.

Source: Twitter
ADC ta fitar da sanarwa bayan jefa zargi

Kara karanta wannan
Datti Baba Ahmed: Abokin takarar Peter Obi ya yi wa hadakar 'yan adawa tonon silili
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mataimakiyar sakataren yaɗa labarai ta kasa ta jam’iyyar ADC, Jackie Wayas, ta fitar, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam'iyyar ADC ta sake jaddada aniyarta ta haɗa ’yan adawa gabanin zaɓen 2027.
Sanata Baba-Ahmed dai ya zargi hadakar 'yan adawa da “yaudarar ’yan Najeriya” tare da ikirarin cewa ba su da karfin ceto kasar daga halin koma bayan da take ciki.
Haka kuma ya bayyana cewa yana da niyyar sake yin takara tare da Peter Obi a 2027.
Menene manufar hadaka?
Sai dai ADC ta jaddada cewa haɗaka wani yunƙuri ne na haɗin kai wanda aka tsara don samar da madadin gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Sanarwar ta nuna cewa hadakar ta haɗa fitattun shugabanni kamar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, Sanata David Mark, Ogbeni Rauf Aregbesola, Rotimi Amaechi, da kuma Peter Obi.
ADC ta yi wa Datti Baba-Ahmed martani
Jam’iyyar ADC ta kuma fayyace cewa kalaman da Sanata Yusuf Datti Baba-Ahmed ya yi ba su wuce ra’ayinsa na kansa ba.
"Maganganun Sanata Datti Baba-Ahmed ra’ayinsa ne na kashin kai, kuma ba su wakiltar matsayar ADC ko 'yan hadaka."
- Jackie Wayas
Haka kuma jam’iyyar ta mika masa goron gayyata, inda ta bayyana shi a matsayin muryar da ake girmamawa, tare da rokonsa da ya shigo cikin hadakar.

Source: Twitter
"Sanata Datti Baba-Ahmed muryar da ake mutuntawa ce, wacce kullum take tsayawa kan gaskiya da adalci."
"Tunda wannan haɗaka yunƙuri ne na haɗa karfi da basirar dukkan ’yan ƙasa masu kishin ƙasa, muna fatan zai shiga cikin tafiyar don bayar da gudummawarsa wajen ganin an cimma burin samar da Najeriya mai kyau."
- Jackie Wayas
Jam'iyyar ADC ta caccaki Shugaba Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta caccaki Shugaba Bola Tinubu, bayan ya yi nade-naden mukamai ga 'yan Arewa.
ADC ta bayyana cewa shugaban kasan ya ba da mukaman ne domin gani ya samu kuri'un 'yan Arewa a zaben 2027.
Sai dai, jam'iyyar ta bayyana cewa 'yan Arewa sun waye kuma ba za su bari a yaudare su bayan an dade da maida su saniyar ware a mulkin Tinubu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
