Ana Jimamin Harbe Masallata, an Kama Dan Shekara 65 na Safarar Makamai

Ana Jimamin Harbe Masallata, an Kama Dan Shekara 65 na Safarar Makamai

  • ‘Yan sanda a jihar Anambra sun cafke wani mutum mai shekaru 65 dauke da harsashi sama da 1,100 a hannunsa a garin Nkpor kusa da Onitsha
  • Kakakin rundunar, SP Tochukwu Ikenga, ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin safarar harsasai tare da bayyana sunayen wasu da ke da hannu a harkar
  • Rundunar ta ce bincike ya kara zurfi domin gano sauran mutane da ke cikin safarar da kuma dakile yaduwar makamai gaba daya a jihar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Anambra – Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta cafke wani mutum mai shekara 65 da ake zargi da safarar makamai, tare da kama shi da harsasai guda 1,100 a garin Nkpor.

Rahoton da rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta fitar ya nuna cewa an kama mutumin ne a kusa da Onitsha.

Kara karanta wannan

'An bar Arewa a baya,' Remi Tinubu za ta bude kamfani a Legas, an fara korafi

Sufeton 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode a wani taro
Sufeton 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode a wani taro. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa an kama shi ne bayan samun sahihin bayanai daga al’umma, wanda ya kai ga nasarar bin sawunsa a ranar Juma’a ta hannun jami’ai a Akwuzu.

Kakakin rundunar, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

SP Ikenga ya kara da cewa an fara bincike tare da tsaurara matakan zakulo sauran masu hannu a cikin wannan safarar.

Yadda aka cafke tsoho mai shekara 65

Ikenga ya bayyana cewa jami’an tsaro da ke Akwuzu sun samu bayanan sirri game da safarar makamai da ake gudanarwa a yankin Nkpor.

A cewar sa, an yi sintiri na musamman inda aka cafke wanda ake zargi mai suna Akpan Godwin da harsashi fiye da 1,100.

Ya kara da cewa wannan samame ya nuna yadda hadin kai tsakanin al’umma da jami’an tsaro ke taimakawa wajen yaki da miyagun ayyuka.

Wanda aka kama ya amsa laifinsa

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Shugaban Boko Haram, Bakura ya karyata labarin kashe shi

Bayan kama shi, Akpan Godwin ya amsa cewa yana da hannu a harkar safarar makamai a yankin, tare da bayyana wasu sunaye da ke harkar tare da shi.

Wannan furuci ya kara tabbatar da tsawon lokacin da aka dauka ana gudanar da harkar a jihar Anambra da kewaye.

Wata motar da aka kama ana safarar makamai a Zamfara a bara
Wata motar da aka kama ana safarar makamai a Zamfara a bara. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Ikenga ya ce rundunar ba za ta tsaya ga kama mutum daya ba, za a ci gaba da zakulo dukkan wadanda ke da hannu domin kawo karshen safarar makamai.

Matakin ‘yan sanda na gaba

Rundunar ta ce bincike ya shiga sabon mataki, inda aka tura jami’ai domin bin diddigin sauran wadanda aka ambata.

Vanguard ta wallafa cewa Ikenga ya yi alkawarin cewa za a sanar da al’umma ci gaban binciken a gaba, musamman idan aka samu karin nasarori.

Ya kuma bukaci al’umma da su ci gaba da ba da bayanai don tabbatar da cewa jihar Anambra ta kasance cikin kwanciyar hankali da tsaro.

Pantami ya magantu kan kashe masallata

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi Allah wadai da kashe masallata a Katsina.

Kara karanta wannan

Masu sayen baburan sata a Kano sun fada tarkon 'yan sanda, an kama mutum 10

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe mutane sama da 50 a wani masallaci a karamar hukumar Malumfashi suna sallar Asuba.

Tsohon ministan ya bukaci jami'an tsaro da su dauki matakin amfani da fasaha wajen yaki da 'yan ta'adda masu barna a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng