'Yan Majalisa da Sanatoci 50 da Suka Dumama Kujera, Ba Su da Gudumuwa a Shekara 1

'Yan Majalisa da Sanatoci 50 da Suka Dumama Kujera, Ba Su da Gudumuwa a Shekara 1

  • Wani rahoto ya bayyana cewa, ‘yan majalisar wakilai 48 da kuma Sanatoci biyar ba su taɓuka komai a majalisa baa cikin shekara guda
  • Binciken ya nuna cewa majalisar dattawa ta gudanar da ayyuka 2,275, yayin da majalisar wakilai ta gudanar da ayyuka 4,239 a wannan taƙin
  • Matsalolin tsaro, tattalin arziki da ilimi ne suka fi daukar hankalin tattaunawa da muhawarar da aka buga a majalisun kasar nan

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Wani rahoto daga Erudite Growth and Advancement Foundation (ERGAF-Africa) ya gano ƴan majalisa masu tsumama kujera kawai.

Rahoton ya bayyana cewa a tsakanin ranar 14 ga Yuni 2023 zuwa 13 ga Yuni 2024, wasu ‘yan majalisa na tarayya ba su yi komai ba a zaman majalisar.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya kara rubuta littafi, ya fallasa aika aikar alkalai a Najeriya

Wasu daga cikin yan majalisa sun dumama kujera a shekara
Hoton zaman majalisar dattawan Najeriya Hoto: Nigerian Senate
Source: Twitter

The Cable ta wallafa cewa rahoton ya ce a cikin wannan lokaci, akalla ‘yan majalisar wakilai 48 da kuma Sanatoci biyar ba su motsa ba.

Yadda wasu ƴan majalisa su ke zaman dumama kujera

Business Day ta wallafa cewa an gano wadansu daga cikin ƴan majalisa ba su ba su ba da gudunmawa ko gabatar da kudiri, ko jawabi a muhawara a zamansu ba.

A cewar rahoton, majalisar dattawa ta gudanar da ayyuka 2,275, inda 663 daga ciki (29.1%) suka zama tattaunawa ce.

Majalisar wakilai kuwa ta yi ayyuka 4,239, daga ciki 507 (11.9%) ne gudummawar muhawara ce a zauren.

Rahoton ya kuma nuna cewa 15.5% na ayyukan majalisar dattawa sun shafi kudurin da aka karanta karo na farko, yayin da a majalisar wakilai 21% ne irin wannan.

Abubuwan da su ka fi ɗaukar hankali a majalisa

Rahoton ya rarraba batutuwan da aka tattauna a kai, inda ya nuna cewa a majalisar dattawa ta fi karkarta ga batutuwan tattalin arziki da 18.5%.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta ragargaji Atiku, El Rufa'i kan wata nasarar da Tinubu ya samu

Sauran inda aka fi mayar da hankali sun hada da batun tsaro da ya damu13.7%, sai kuma tattauna batutuwan ilimi da 10.9%.

A majalisar wakilai kuwa, tsaro ya fi daukar hankali da 16.9%, sai tattalin arziki 13.7% da ilimi 10.4%.

Wasu daga cikin yan majalisar wakilai ba tabuka komai ba
Hoton wani zama a majalisar wakilai Hoto: House of Representatives
Source: Twitter

Masu kokari wajen bada gudumuwa a majalisa

A bangaren muhawara, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya fi ba da gudummawa 38, yayin da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Julius Ihonvbere ya ja ragama da gudummawa 26.

A bangaren kudurori, shugaban majalisar dattawa, Sanata Michael Opeyemi, ne ya fi gabatar da su 10, yayin da Ihonvbere ya fi a majalisar wakilai da 12.

Haka kuma, Sanata Ngwu Osita ya fi shigar da koke a majalisar dattawa da guda 3, yayin da Okey Onuakalusi daga Oshodi-Isolo, Legas, ya yi zarra a bangaren a majalisar wakilai da guda 14.

'Yan majalisar da ake ganin ba su bada gudumuwa

Wasu daga cikin ‘yan majalisar da ba su yi wata gudummawa ba a zaman sun hada da: Abubakar Baba Zango (Adamawa) da Mohammed Inuwa Bassi (Adamawa).

Kara karanta wannan

Nijar: An harbe shugaban Boko Haram da ya maye gurbin Shekau har lahira

Sauran su ne Nnabufie Chiwe Clara (Anambra), Abdulkadir Rahis (Borno), Stainless Chijioke Nwodo (Enugu), da Yaya Bauchi Tongo (Gombe).

Sai Jonas Okeke, (Ehime mbano, Imo); Adamu Yakubu ( jigawa); Ibrahim Usman (Jigawa) da Sani Nazifi (Jigawa).

Sauran ƴan majalisa da su ka yi zamansu ba tare da ba da gudunmawa ba su ne Madawaska Dahiru (Jigawa) da Yahya Richifa (Kaduna); Yusuf Bashir (Kaduna).

Dan majalisa ya naɗa hadimai 106

A baya, mun wallafa cewa ‘dan majalisar jihar Nasarawa, Musa Gude, mai wakiltar mazabar Uke/Karshi, ya bayyana cewa ya nada hadimai 106.

Gude ya bayyana cewa wasu daga cikin hadiman za su karɓi ₦100,000, wasu ₦80,000, ₦50,000, ₦30,000, ₦20,000, har da ₦10,000 a kowane ƙarshen wata.

Wannan ƙuduri yana cikin tsarinsa na gudanar da jagoranci da zai tafi da dukkanin al'ummar da su ka zaɓe shi, tare da inganta rayuwarsu baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng