ADC: An Samu Wanda Zai Dawo da Tallafin Man Fetur idan Ya Zama Shugaban Kasa a 2027
- Tsohon dan takarar shugaban kasa a inuwar ADC, Dumebi Kachikwu ya ce bai kamata a cire tallafin man fetur a Najeriya ba
- Kachikwu ya ce kamata ya yi gwamnati ta zakulo masu karkatar da kudin tallafin, ta hukunta su maimakon laifinsu ya shafi talakawa
- Ya kuma musanta batun cewa Bola Tinubu ya cire tallafin man fetur, yana mai cewa tun asali babu tanadin shi a kasafin kudi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - 'Dan takarar shugaban kasa na ADC a zaben 2023, Dumebi Kachikwu, ya bayyana cewa jam’iyyar ba za ta lamunci wasu tsofaffin ‘yan siyasa su shigo su kwace iko ba.
Kachikwu ya kuma jaddada cewa zai sake neman takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa, yana mai cewa bai kamata wani dan Arewa ya nemi takara a 2027 ba.

Source: Facebook
Mista Dumebi Kachikwu ya yi wannan furucin ne a wata hira da aka yi da shi a baya-bayan nan, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Dan takaran ADC ya gargadi Atiku Abubakar
Ya ce wasu ‘yan siyasa sun hada kai domin kwace jam’iyyar ADC daga hannun wadanda suka sha wahala wajen gina ta, don cimma burinsu na shugabanci a zaben 2027.
Kachikwu ya ce ADC na nan kan manufofinta na bayar da dama ga sababbin fuska, ba wai ga wadanda suka riga suka samu dama amma suka kasa ceto Najeriya daga talauci da matsalolin tattalin arziki ba.
“Ina gargadin duk wani dan takarar da yake son amfani da ADC, musamman Atiku Abubakar, ya hakura. Ya kamata Atiku ya koma ya huta. Mun taba ba shi dama a baya amma bai yi abin da ake bukata ba.”
An nemi 'yan Arewa su hakura da takara a 2027
Da yake magana kan zaben 2027, Kachikwu ya ce kowa na da ‘yancin tsayawa takara, amma ya kamata a ba yankin Kudu dama kamar yadda Arewa ta samu a baya.
“Idan akwai wanda zai kalubalanci shugaban kasa mai ci, Bola Tinubu, to ya kamata ya fito daga Kudu. Wannan shi ne adalci da rikon amana a tsarin siyasar Najeriya,” inji shi.
Kachikwu ya sha alwashin dawo da tallafin fetur
Game da batun tallafin fetur, Kachikwu ya yi bayanin cewa idan ya zama shugaban kasa zai dawo da tallafin mai domin 'yan kasa su amfana, rahoton Politics Nigeria.
“A ganina ya kamata kowace kasa mai arzikin man fetur ta bayar da tallafi ga jama’arta. Ba daidai ba ne talakawa su ci gaba da wahala saboda rashin iya tafiyar da tsarin tallafi.
"Abin da ya kamata mu yi shi ne gurfanar da wadanda suke wawure kudin da ake warewa don tallafin mai, ba wai a dauke tallafin gaba daya ba," in ji shi.

Source: Twitter
Kachikwu ya ce bai kamata a dora laifin cire tallafin fetur a kan Tinubu ba, domin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne bai tanadi kudin tallafi a kasafin kudi ba.
Kachikwu ya soki hadakar 'yan adawa a ADC
A wani labarin, kun ji cewa Dumebi Kachikwu ya yi zargin cewa haɗakar ƴan adawa shiri ne domin cika burin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Ya yi ikirarin cewa haɗakar ƴan adawa da ta rungumi ADC a matsayin jam'iyyar da za ta yi amfani da ita, ta gama tsara wanda za ta ba tikitin takara a 2027.
Kachikwu ya kuma yi zargin cewa Peter Obi na shirin barin ƙawancen domin ya bi wata hanya wajen cimma burinsa na takarar shugaban ƙasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


