Bayanai Sun Kara Fitowa daga EFCC, An Ji Gaskiyar Dalilin Neman Surukin Atiku Ruwa a Jallo
- Ana zargin EFCC ta ayyana neman surukin Atiku, Abdullahi Bashir Haske ne saboda dangantakarsa da tsohon mataimakin shugaban kasa
- Mai magana da yawun hukumar EFCC ta kasa, Dele Oyewale ya musanta wannan zargi, yana mai cewa sun jima suna binciken Bashir Haske
- Oyewale ya ce EFCC ta dauki matakin ayyana nemam surukin Atiku ne bayan ya karya sharuddan belin da aka ba shi a baya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta yi karin haske kan dalilin da ya sa ta ayyana neman Abdullahi Bashir Haske, ɗan kasuwa kuma surukin jagoran adawar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar.
EFCC ta yi watsi da zargin da wasu ke yi cewa ta ayyana neman Bashir Haske ne saboda dangantakarsa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku.

Kara karanta wannan
Hafsan hafsoshi ya bukaci 'yan Najeriya su dauki makamai? Hedkwatar tsaro ta yi bayani

Source: Twitter
Mai magana da yawun EFCC na kasa, Dele Oyewale ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da wakilin jaridar Daiy Trust ranar Juma'a, 22 ga watan Agusta, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku Abubakar na cikin jagororin adawa da ake ganin suna da niyyar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Me yasa EFCC ke neman surukin Atiku?
A hirar da aka yi da shi ta wayar tarho, Dele Oyewale, ya kira wannan zargin na cewa saboda Atiku EFCC ke farautar Bashir Haske, da “zargi mara amfani."
Ya bayyana cewa hukumar EFCC ta dauki tsawon shekaru ta na binciken Bashir Haske, kuma yana kan beli ne amma ya karya sharuddan belin.
Oyewale ya ce:
"Abdullahi Bashir Haske mutum ne da muka dade muna bincike a kansa. Mun ba shi beli amma ya karya sharuddan belin, shi ya sa muka ayyana nemansa ruwa a jallo. Ta yaya wani zai yi irin wannan zargi?’”
Yadda EFCC ta ayyana neman surukin Atiku
Hukumar ta EFCC ta fitar da sanarwa a daren Alhamis inda ta bayyana cewa tana neman surukin Atiku kan zargin haɗin baki wajen aikata laifi da kuma safarar kudin haram.
A sanarwar da EFCC ta wallafa a X, ta roƙi jama’a su taimaka da bayanai kan inda Abdullahi Bashir Haske yake ta hanyar kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko wani daga cikin ofisoshin EFCC.

Source: Twitter
Hukumar ta kuma bukaci ‘yan Najeriya su bayar da sahihan bayanai ta ofisoshinta da ke manyan birane kamar Ibadan, Uyo, Sokoto, Maiduguri, Benin, Makurdi, Kaduna, Ilorin, Enugu, Kano, Lagos, Gombe, Fatakwal da Abuja.
Wannan lamari dai ya tayar da kura a Najeriya, inda aka fara zargin EFCC na neman taba Atiku ne ta hanyar surukinsa, zargin da hukumar ta musanta.
EFCC ta tsare wasu jami'an hukumar NAHCON
A wani labarin, kun ji cewa hukumar EFCC ta tsare manyan jami’an hukumar NAHCON ta kasa bisa zargin almundahana da ta shafi aikin Hajjin bara.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta ragargaji Atiku, El Rufa'i kan wata nasarar da Tinubu ya samu
Rahotanni daga majiyoyin cikin jami'an EFCC sun tabbatar da cewa wadanda aka kama suna tsare a hannun hukumar EFCC tun kwanakin baya.
An tattaro cewa EFCC ta bukaci jami’an da su dawo da kuɗin da ake zargin sun amsa, amma suka ki yin hakan, abin da ya sa aka ci gaba da tsare su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
