Dakarun Sojoji Sun Hallaka Kwamandojin Boko Hakam da 'Yan Ta'adda 11

Dakarun Sojoji Sun Hallaka Kwamandojin Boko Hakam da 'Yan Ta'adda 11

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar rage mugun iri na wasu daga cikin 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram
  • Sojojin sun kashe kwamandoji biyu da wasu mayaka bayan sun yi yunkurin kai hari a karamar hukumar Gwoza a jihar Borno
  • Hakazalika, sojojin sun kwato makamai masu tarin yawa tare da babura daga hannun 'yan ta'addan na Boko Haram

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai a Arewa maso Gabas sun kashe manyan kwamandoji biyu na Boko Haram a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun kuma hallaka wasu ’yan ta’adda 11 a wani samame na baya-bayan nan da suka kai a garuruwan Bitta da Wulgo da ke karamar hukumar Gwoza, jihar Borno.

Sojoji sun kashe kwamandojin Boko Haram
Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, tare da dakarun sojoji Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ya sanar da hakan, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

Al'umma sun samu sauƙi: Sojoji sun damƙe hatsabibin ɗan bindiga, yaransa 13

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun kashe kwamandojin Boko Haram

Kwamandojin da aka kashe da sune Abu Nazir (Munzir na Juye) da kuma Abu Fatima (Munzir na Koloram), waɗanda suka jagoranci yunƙurin kai hare-hare biyu a garuruwan biyu, a ranakun Alhamis 21 ga watan Agusta da Juma’a 22 ga watan Agusta.

A yayin waɗannan hare-hare, sojojin kasa tare da haɗin gwiwar rundunar sojojin sama sun yi nasarar hallaka ’yan ta’adda 13, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Manjo Janar Abdulsallam Abubakar, ya bayyana cewa ’yan ta’addan sun yi kokarin kutsawa cikin garuruwan Bitta da Wulgo a tsakar daren Alhamis ta hanyoyi daban-daban.

Sai dai, ya ce sojoji sun tarbe su da luguden wuta mai tsanani wanda ya ɗauki sa’o’i har zuwa safiyar Juma’a.

Sojoji sun kwato makamai hannun 'yan Boko Haram

Kwamandan ya ce an kwato babura guda shida da ke hannun ’yan ta’addan tare da bindigogi AK-47 da dama da kuma ɗimbin harsasai.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Malaman Musulunci sun yi zanga zanga kan alaƙar Najeriya da Isra'ila

Ya kara da cewa da dama daga cikin ’yan ta’addan sun tsere da raunuka masu tsanani a yayin da aka fatattake su.

Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Garuruwan Bitta da Wulgo na daga cikin wurare bakwai da aka sake mayar da mutane a karamar hukumar Gwoza.

A baya, ’yan Boko Haram sun kori mazauna wuraren lokacin da suka mamaye Gwoza a 2014 tare da kafa “Daular Musulunci” a garin.

Sai dai, dakarun sojojin Najeriya sun sake kwato Gwoza da wasu garuruwan da ke karkashinta, ciki har da Bitta da Wulgo, sannan gwamnatin jihar Borno ta kuma maido da jama’a garuruwan.

Sojoji sun kama makamai

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji na rundanar Operation Hadin Kai sun samu nasarar cafke wasu makamai da aka yi yunkurin yin safararsu daga Borno.

Sojojin sun kama makaman ne da aka boye a cikin wata babbar jaka a kan hanyar Maidguri zuwa Kaduna.

An gano kayan ne a wajen wani shingen bincike na sojoji bayan direban motar ya nuna shakku kan abin da ke cikin jakar, wadda aka ba shi sako ya kai Kaduna.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng