Dahiru Bauchi: 'Yan Tijjaniyya a Duniya Sun Dura Yobe Yin Gagarumin Mauludi

Dahiru Bauchi: 'Yan Tijjaniyya a Duniya Sun Dura Yobe Yin Gagarumin Mauludi

  • Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya bukaci ‘yan Najeriya da su dage wajen yi wa shugabannin ƙasa addu’a domin samun jagoranci na gari da zaman lafiya
  • Buni ya bayyana cewa addu’a mai kyau kan ja hankalin shugabanni kan gaskiya da rikon amana, yayin da addu’a marar kyau ke kawo gazawa a shugabanci
  • Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya bayyana haka ne yayin ganawa da shugabannin Darikar Tijjaniyya karkashin Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Yobe – Gwamna Mai Mala Buni na Yobe ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi ta addu’o’i na neman taimakon Allah ga shugaba Bola Tinubu, da sauran shugabanni a matakai daban-daban.

Gwamnan ya bayyana cewa addu’a na taka muhimmiyar rawa wajen sanya shugabanni su yi ayyuka masu amfani ga jama’a, tare da taimaka wa kasar wajen samun zaman lafiya da tsaro.

Kara karanta wannan

An dauki gwamna 1 a Najeriya, an ba shi lambar yabo ta 'Zabin Jama'a' a kasar Faransa

Mai Mala Buni tare da 'yan Tijjaniyya a jihar Yobe
Mai Mala Buni tare da 'yan Tijjaniyya a jihar Yobe. Hoto: Mamman Muhammad
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai game da jawabin da gwamnan ya yi ne a cikin wani sako da mai magana da yawunsa, Mamman Muhammad ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buni ya yi jawabin ne a Damaturu lokacin da shugabannin gidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi suka kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnati.

Buni ya bukaci a yi wa Tinubu addu'a

Gwamna Buni ya bayyana cewa samun jagoranci na gari da kyakkyawan sakamako daga shugabanni na da alaƙa da yadda ake yi musu addu’a.

Ya ce idan jama’a suka yi addu’a mai kyau, shugabanni za su yi jagoranci mai kyau da samar da ayyukan cigaba.

“Ina kira gare mu da mu dage wajen yi wa shugaban ƙasa da gwamnoni da duk masu rike da madafun iko addu’a.

- In ji shi.

Ya ƙara da cewa abin da ake bukata shi ne ‘yan Najeriya su hada hannu wajen addu’o’i maimakon yin fatan sharri ga shugabanninsu.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta ragargaji Atiku, El Rufa'i kan wata nasarar da Tinubu ya samu

Bukatar addu’a ga jami’an tsaron Najeriya

A cewar Gwamna Buni, jihar Yobe ta taba ganin yadda addu’a ta taimaka wajen samun sauƙi a yaki da ta’addanci.

Don haka ya bukaci jama’a su kara dagewa wajen yi wa jami’an tsaro addu’a domin ci gaba da samun nasara.

Ya ce:

“Ya zama wajibi mu ci gaba da yi musu addu’a domin Allah ya ba su ƙarfin guiwa da nasara a ayyukansu na kare rayuka da dukiyoyin al’umma,”

Za a yi Mauludin Tijjaniyya a Yobe

Tun da farko, shugaban gidauniyar Sheikh Dahiru Usaman Bauchi, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi, ya ce sun zo jihar Yobe ne domin bikin mauludin Sheikh Ahmadu Tijjani.

Ya bayyana cewa wakilai daga ƙasashen waje kamar Morocco da Algeria, sauran kasashe da kuma wasu jihohin Najeriya sun isa jihar.

Ibrahim Dahiru Bauchi na gaisawa da Mai Mala Buni
Ibrahim Dahiru Bauchi na gaisawa da Mai Mala Buni. Hoto: Mamman Muhammad
Source: Facebook

Ibrahim Dahiru Bauchi ya ce sun zo ne domin yi wa Najeriya addu’a tare da yin fatan alheri ga shugabanni da al’umma.

Kara karanta wannan

Bayan dawowa daga London, Ganduje ya bi sawun Shettima da Zulum wajen ta'aziyya Kogi

Sheikh Daurawa ya yi wa mata nasiha

A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi wa mata nasiha ta musamman a jihar Kano.

Yayin nasihar, Sheikh Daurawa ya lissafa muhimman abubuwa bakwai da ya kamata kowace mace ta kiyaye idan tana saon samun daraja.

Legit Hausa ta rahoto cewa malamin ya bayyana haka ne wani taro da daliban jami'ar North West da ke jihar Kano suka shirya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng