Kamfanin Amurka Ya Kawo Shirin da Za a Tallafa wa Matasa Sama da 300,000 a Najeriya

Kamfanin Amurka Ya Kawo Shirin da Za a Tallafa wa Matasa Sama da 300,000 a Najeriya

  • Wani kamfani daga kasar Amurka da hadin guiwar gwamnatin jihar Imo ya kaddamar da shirin tallafa wa matasa akalla 300,000 a Najeriya
  • Shirin zai bai wa matasan horon kasuwancin zamani da kirkire-kirkire, sannan zai ba su damar samun jari
  • Kamfanin ya bayyana cewa shirin zai taka muhimmiyar rawa wajen gina matasan Najeriya musamman masu hazakar kirkire-kirkire

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Imo - Wani kamfanin harkokin kasuwanci da samar da damarmaki na Amurka (USMAC), tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Imo, ya kaddamar da wani gagarumin shiri a Najeriya.

Manufar ita ce bunkasa kirkire-kirkire da kasuwancin matasa, tare da tallafa wa matasa ‘yan Najeriya 300,000 a shekaru biyar masu zuwa.

Gwamnan Imo, Hope Uzodinma.
Hoton gwamnan Imo a fadar gwamnatinsa da ke Owerri Hoto: Hope Uzodinma
Source: Facebook

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa an yiwa shirin taken "Discovering and Incubating the Next Generation of Nigerian Innovators and Entrepreneurs."

Kara karanta wannan

Najeriya ta samu rancen $238m daga Japan, minista ya lissafa ayyukan da za a yi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubuwan da matasa za su samu a shirin

A karkashin shirin, za a bai wa matasa horo a fannin kasuwanci, samun jagoranci daga manyan masana a Silicon Valley, da kuma ba su jarin da za su fara kasuwanci.

Wakilin USMAC a Najeriya da Afirka, Matt Ifesieh, ya bayyana cewa shirin wani mataki ne na bai wa matasan Najeriya damar shiga harkokin kasuwancin zamani.

A wurin kaddamar da shirin, Ifesieh ya ce:

"A yau muna cikin zamani na fasaha, inda kirkire-kirkire suke jagorantar rayuwarmu gaba daya.
"Wannan shiri zai bai wa matasan Najeriya dabarun kasuwanci na zamani, tsare-tsaren kasuwanci masu tasiri, da kuma damar samun jarin kasuwanci na duniya musamman daga Silicon Valley.”

Kamfanin Amurka ya yi hadin gwiwa da Imo

Shirin ya yi daidai da manufar gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, a karkashin shirin “Imo Scale Up Programme," wanda zai samar da ayyukan yi sama da 300,000 da tallafawa dubban masu kirkire-kirkire.

Kara karanta wannan

Nijar: An harbe shugaban Boko Haram da ya maye gurbin Shekau har lahira

Wannan shiri na gudana tare da hadin gwiwar Cibiyar Imo Digital, UC Berkeley’s Sutardja Centre for Entrepreneurship and Technology, da sauran abokan hulda.

Shugaban USMAC, Dr Chris Burry, ya ce shirin zai taimaka wajen gina “hazikam matasa da masu basirar kirkire-kirkire” a Najeriya.

Matasa za su samu damarmaki a Najeriya.
Hoton wasu matasa a wurin aiki a kamfani Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya kara cewa sama da kashi 95% na masu kafa manyan kamfanoni a duniya suna da kwarewa a harkar kirkire-kirkire na zamani.

Dr. Chris Burry ya tabbatar da cewa Founder Dojo zai kawo irin wannan tsarin a Najeriya domin mutane su amfana musamman matasa.

Ya kuma yabawa Gwamna Uzodimma bisa kafa Digital City a Imo, yana mai kiran shi da “misali ga sauran jihohi a Najeriya” wajen hada kai tsakanin gwamnati da masu zaman kansu.

Gwamnatin Tinubu ta dawo da shirin GEEP

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Shugaban Bola Tinubu ta dawo da shirin GEEP wanda ke bai wa kananan yan kasuwa rancen kudi da kuma tallafi a Najeriya.

Gwamnatin ta canza fasalin shirin zuwa RHGEEP 3.0 kuma ana sa ran 'yan Najeriya miliyan biyar za su amfana daga nan zuwa 2027.

Ta bayyana cewa duk da nasarorin da aka samu a GEEP 1.0 da 2.0, sabon shirin RHGEEP 3.0 ya zo da sauyi na musamman.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262