Al'umma Sun Samu Sauƙi: Sojoji Sun Damƙe Hatsabibin Ɗan Bindiga, Yaransa 13
- Sojojin Najeriya sun yi ram da fitaccen ɗan ta’adda da ake zargin cewa ya addabi jihohin Kaduna da kuma Plateau
- Rundunar ta yi nasarar cafke Adamu Buba, wanda aka fi sani da ‘Mai Pankshin’, tare da mutane 13 da ke cikin tawagarsa
- Jami'an OPSH suka ce an kwato bindigogi, harsasai da babura, yayin da a wasu hare-hare aka kashe ‘yan ta’adda
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Rundunar sojin Najeriya ta samu babban nasara yayin yaki da matsalar tsaro na cikin gida bayan cafke fitaccen ɗan ta’adda.
Rundunar sojoji ta tabbatar da cafke dan bindigar da ake nema, Adamu Buba, wanda aka fi sani da ‘Mai Pankshin’.

Source: Twitter
Hatsabiban yan bindiga sun shiga hannun sojoji
Rahoton Vanguard ya ce an yi nasarar kama Mai Pankshin ne tare da wasu mutum 13 daga cikin tawagarsa.

Kara karanta wannan
'Yakin ba na sojoji kadai ba ne,' Janar Buratai ya kawo dabarar murkushe 'yan ta'adda
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hedikwatar tsaro (DHQ) ta bayyana hakan a ranar Juma’a, inda ta ce waɗannan miyagun mutane ne suka jagoranci hare-haren kisan kai da ta’addanci a jihohin Plateau da Kaduna.
Daraktan ayyukan yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, ya bayyana cewa sojojin Operation Safe Haven sun kai farmaki a Riyom, Barkin Ladi, Jos ta Kudu.
Sauran wuraren da suka kai harin sun hada da Bassa da Jos ta Arewa a Plateau, da kuma Jaba da Zangon Kataf a Kaduna.
An kwato bindigogi, harsasai da babura daga hannunsu, yanzu haka ana gudanar da bincike a kan su domin gano bayanai da suka shafi sauran miyagun ayyuka.

Source: Facebook
Kokarin jami'an tsaro wajen yaki da ta'addanci
A wani bangare, Kwamandan rundunar OPSH, Manjo Janar Foluso Oyinlola, ya mika makamai 220 da harsasai 1,874 da aka kwato daga miyagu ga hukumar kula da makamai a Jos.
Daga 13 zuwa 20 ga watan Agustan 2025, sojojin Najeriya sun gudanar da jerin hare-hare a wurare daban-daban.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta ragargaji Atiku, El Rufa'i kan wata nasarar da Tinubu ya samu
An yi nasarar kashe ‘yan ta’adda da cafke masu laifi da kuma ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.
Samamen sojoji Arewa maso Yamma da Gabas
A Arewa maso Gabas, dakarun Operation Hadin Kai sun kai hare-hare a Borno da Yobe, inda suka kashe Boko Haram da ISWAP, tare da ceto mutane uku.
Haka kuma, an kwato makamai, bama-bamai, babura da kuɗi N191,700 daga hannun ‘yan ta’addan, yayin da aka kama wasu mutane tara da ke taimaka musu.
A Arewa maso Yamma, dakarun Operation Fagge Yamma sun kashe ‘yan ta’adda a Zamfara, Katsina da Sokoto, inda aka kubutar da mutum 46 da aka yi garkuwa da su.
Sojoji sun musanta cewa Turji ya mika wuya
Mun ba ku labarin cewa Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta fito ta yi bayani kan rahotannin da ke cewa tantirin dan bindiga, Bello Turji, ya mika wuya.
Rundunar ta bayyana cewa hatsabibin dan bindigan bai ajiye makamansa ba, domin har yanzu sojoji na ci gaba da farautarsa.
Hakazalika, rundunar ta musanta cewa dakarun sojoji suna yin kisan gilla a yankin Kudu maso Gabas na Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng