NEMA Ta Nemi 'Yan Jihohin Arewa 3 Su Kaura kan Fargabar Mummunar Ambaliya
- Hukumar NEMA ta fitar da gargadi ga mazauna jihohin Kebbi, Neja da Kwara da ke zaune kusa da kogin Niger da su fara barin wuraren
- Shugabar hukumar, Hajiya Zubaida Umar, ta umurci ofisoshin NEMA a jihohin da abin ya shafa su kara wayar da kan jama’a kan hatsarin ambaliya
- NEMA ta ce ruwan kogin Niger na karuwa daga jamhuriyar Benin, abin da zai iya jawo mummunar ambaliya a kwanaki masu zuwa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hukumar NEMA ta gargadi jama’a da ke zaune a kusa da kogin Niger a Kebbi, Neja da Kwara da su fara barin wuraren da ake fargabar ambaliyar ruwa na iya shafa.
Gargadin ya biyo bayan samun rahotanni daga jamhuriyar Benin cewa ruwan kogin Niger na karuwa, lamarin da ka iya haifar da mummunar ambaliya a sassan da ke iyaka da Najeriya.

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa shugabar hukumar, Hajiya Zubaida Umar ce ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta bukaci hukumomin jihohi da kwamitocin gaggawa na ƙananan hukumomi su dauki matakai na musamman.
Umarnin NEMA ga ofisoshinta a jihohi
NEMA ta umurci ofisoshinta a jihohi da dama su kara kaimi wajen fadakarwa da shirya jama’a kan yadda za su kare kansu.
Hajiya Zubaida Umar ta ce wajibi ne jama’a da ke zaune a wuraren da ake zargin ruwa zai shiga su koma wurare masu tsawo domin samun kariya.
Ta kuma jaddada cewa ofisoshin hukumar a jihohi su gudanar da tarukan wayar da kan jama'a kai tsaye domin kiyaye asarar rayuka da dukiyoyi.
Bukatar jihohi su karfafa shirye-shirye
Hajiya Zubaida ta roki gwamnatocin jihohi su karfafa hukumomin agajin gaggawa na jihohi (SEMA) da kuma kwamitocin gaggawa na ƙananan hukumomi (LEMCs).
Vanguard ta rahoto cewa ta ce dole a samu kyakkyawan tsari da zai baiwa jama’a damar sanin hanyoyin tserewa da wuraren da za su iya tsugunnawa idan ambaliya ta faru.
Shirye-shiryen kare rayuka da dukiyoyi
NEMA ta jaddada cewa tana gudanar da hadin gwiwa da hukumomi daban-daban domin rage illar ambaliyar da ake fargabar faruwarsu a wannan shekarar.
Hukumar ta ce tana fatan kare rayukan jama’a da kuma dukiyoyinsu musamman a jihohin da abin ya fi kamari.
A cewar sanarwar, jihohin Kebbi, Neja da Kwara ne suka fi fuskantar barazanar ambaliyar sakamakon kusancinsu da jamhuriyar Benin da kuma kasancewarsu a bakin kogin Niger.

Source: Twitter
NEMA ta shawarci jama’a da ke zaune a wuraren hadari da su ci gaba da bibiyar rahotanni da hukumomin tsaro da agaji ke fitarwa.
Haka kuma ta bukace su rika yin amfani da lambobin gaggawa da aka tanada idan ambaliyar ta tunkaro.
Kwale kwale ya kife da mutane a Sokoto
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta tabbatar da rasa rayuka a wani hadarin kogi a Sokoto.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu daga cikin mutanen da hadarin ya rutsa da su sun rasu yayin da aka ceto wasu.
Legit Hausa ta wallafa cewa jami'an hukumar sun ziyarci wajen da abin ya faru tare da zuwa gidajen wadanda hadarin ya rutsa da su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


