Dangote na dab da Kafa Sabon Tarihin Dukiya bayan Ya Samu Ribar $1.2bn

Dangote na dab da Kafa Sabon Tarihin Dukiya bayan Ya Samu Ribar $1.2bn

  • Fitaccen attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote, na dab da kafa tarihi yayin da kuɗinsa suka kara habaka zuwa akalla Dala biliyan 30
  • Alhaji Dangote ya samu karin ne bayan matatarsa mansa da ke jihar Legas mai tace gangar mai 650,000 a rana ta ci gaba da aiki ganga ganga
  • Masana sun ce Dangote na iya zama ɗan Afrika na farko da yawan dukiyarsa za ta kai Dala biliyan 30, wanda zai ba shi damar kafa tarihi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar LegasAttajirin Afrika kuma shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ƙara samun ribar akalla Dala biliyan 1.20 a dukiyarsa a bana.

Wannan gwaggwabar riba ta kara yawan dukiyar da ya tara, lamarin da ya ƙara kusantar da shi zama ɗan Afrika na farko da dukiyarsa ta kai Dala biliyan 30.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta hada gwiwa da Abba, za a kara tunkudo karin wutar lantarki Kano

Alhaji Aliko Ɗangote, Shugaban rukunin kamfanin Dangote
Dangote a yayin wata hira da manema labarai Hoto: Getty
Source: Getty Images

A halin yanzu, Bloomberg Billionaires Index ya ƙididdige arzikin Dangote ya kai Dala biliyan 29.3, sama da Dala biliyan 28.1 da ya fara da shi a cikin shekarar 2024.

Arzikin Aliko Dangote ya karu a yanzu

Legit.ng ta wallafa cewa karuwar arzikin attaijirin Afrika ya jawo hasashen yiwuwar dukiyar Dangote ta kai Dala biliyan 30 nan ba da jimawa ba.

Idan hakan ta tabbata, zai zama mutum na farko daga Afrika da ya kai wannan matsayi a tarihin kasuwanci.

Sai dai a farkon shekara, arzikin Dangote bai karu sosai ba inda a watan Afrilu aka ga ya tashi da Dala miliyan 153 kawai.

Daga baya ya sauka da Dala miliyan 400, amma cikin watanni biyu da suka gabata, darajar hannun jari da kuma tasirin sabon matatar mai mansa sun kara yawan dukiyarsa.

Yadda arzikin Dangote yake karu wa

Babban kaso na arzikinsa yana fitowa daga hannun jarinsa a kamfanonin da ake sayar da hannun jari a kasuwar Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan dawowa daga London, Ganduje ya bi sawun Shettima da Zulum wajen ta'aziyya Kogi

Kamfanin simintin Dangote na da darajar Dala biliyan 5.54, Kamfanin sukarinsa kuma ya kai darajar Dala miliyan 357, NASCON ya kai Dala miliyan 117, sannan hannun jarinsa a UBA ya kai kusan Dala 484,000,000.

Attajiri mafi arziki a Najeriya
Alhaji Aliko Dangote a wata hira da ya yi a baya Hoto: Getty
Source: Getty Images

Karin Dala biliyan 1.20 ya samo asali ne daga ƙarfafa kasuwar hannun jari da sakamakon ribar da ya samu daga kamfanonin.

Amma ribar ta fi shigo wa ne daga matatar mai ta Dala biliyan 20 da ke Lekki, a jihar Legas wacce ta fara aiki tun a farkon shekarar 2024.

Dangote ya canza farashin mai

A wani labarin, kun ji cewa matakin da matatar Dangote ta ɗauka na sassauta farashi a rumbun ajiya ya haifar da tasiri mai kyau a kasuwar man fetur, inda aka samu ragi.

Wannan ya sa 'yan kasuwa da NNPCL suka fara rage farashin a gidajen mai, musamman a Legas, inda ake samun ragin da ke bai wa talakawa damar samun man fetur a ƙasa da abin da aka saba.

Sai dai fa, har yanzu akwai ra’ayoyi da dama na cewa wannan sauƙin bai kai ga cimma saukin da ake so ba, inda su ka ce lallai a kara rage farashi domin kowane dan Najeriya ya mora.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng