Gwamnatin Tarayya Ta Hada Gwiwa da Abba, Za a Kara Tunkudo Karin Wutar Lantarki Kano
- Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin samar da karfin wuta 20MW ga Masana’antar Challawa a jihar Kano domin inganta kamfanoni
- Hukumar NDPHC za ta yi haɗin gwiwa da NASENI da kuma kamfanin Haier wajen aiwatar da wannan aiki ta hanyar aiki da fasahar hasken rana
- Gwamnatin Kano ta tabbatar da cikakken goyon bayanta domin tabbatar da aikin ya samu nasara domin amfanin mutanen jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnatin tarayya ta sanar da wani muhimmin shiri na samar da karin wutar lantarki mai karfin 20 megawatts ga masana’antar Challawa da ke Kano.
Wannan shiri zai taimaka wajen habaka harkokin masana’antu da bunkasa tattalin arzikin jihar bayan ya kammala.

Source: Facebook
Wannan na kunshe ne a sakon da Ma'aikatar makamashi ta jihar Kano ta wallafa a shafinta na X a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan
'Da 'yar matsala,' An fara magana kan bai wa fursunoni damar yin zabe daga magarkama
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin tarayya da ta Kano na aikin lantarki
Sanarwar da ma'aikatar ta wallafa ta ce hukumar Niger Delta Power Holding Company (NDPHC) ce za ta jagoranci aikin tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Fasahar Kimiyya da Injiniya (NASENI) da Haier Technologies.
Shugaban NDPHC, Injiniya Jennifer Adighije, ta bayyana hakan ne yayin ziyarar aiki da ta kai masana’antar Challawa a jihar Kano.

Source: Facebook
Jennifer Adighije ta ce kamfanonin za su samar da tsarin samar da wuta ta hanyar fasahar hasken rana domin tabbatar da ingantaccen wutar da masana’antun za su dogara da shi.
A wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama’a na NDPHC, Emmanuel Ojor, ya fitar daga birnin Abuja, ya tabbatar da cewa Adighije ta kai ziyara Kano.
A cikin tawagarta akwai Daraktan Ayyukan Samar da Wuta, Injiniya Kassim Abdulahi, da kuma Daraktan Sashen Harkokin Cikin Gida, Injiniya Omoregie Ogbeide-Ihama.
Gwamnatin Kano ta za ta samar da wutar lantarki
A yayin taron da aka gudanar, kwamishinan wutar lantarki da makamashin zamani a jihar Kano, Injiniya Gaddafi Shehu Sani, ya tabbatar da kudurin gwamnati.
Ya bayyana cewa gwamnati a shirye take ta bayar da cikakken goyon baya don ganin aikin ya tabbata domin jama'ar Kano su ci moriyarsa.
Dakta Gaddafi Shehu Sani ya ce wannan shiri zai zama ginshiƙi wajen habaka masana’antu da samar da ayyukan yi ga dubunnan matasan jihar.
Haka kuma gwamnatin Kano ta bayyana cewa haɗin gwiwar za ta taimaka wajen rage dogaro da wutar lantarki daga cibiyar kasa wadda ta sha fama da matsaloli na rashin dorewa.
Mahangar masana kan wutar lantarki a Najeriya
Ibrahim Kiyawa, lauya ne kuma mai sharhi a kan makamashi a Kano, ya shaida wa Legit cewa akwai bukatar tsayayyen hasken wutar lantarki a ƙasar nan.
Ya ce lokaci ya zo da lamarin wutar lantarki ke ƙara taɓarɓarewa a Arewa Najeriya.
A kalamansa:
"Wutar lantarki dai ita ce jigon ci gaban al'umma ko ita ce hanya ɗaya idan an tsaida ita, za ta sama wa matasa aiki, kamfanonin da suka durƙushe za su dawo su buɗe, kuma za a samu alheri."
Gwamnan Kano ya rantsar da sababbin hadimai
A wani labarin, mun wallafa cewa gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ɗauki mataki na nuna ƙudurin gwamnati wajen yaki da rashawa don tabbatar da ci gaba.
Abba Gida Gida ya rantsar da Barista Sa’idu Yahya a matsayin sabon shugaban hukumar yaki da cin hanci da karɓar ƙorafe-ƙorafe (PCACC) ta jihar a ci gaba da aikin yaki da rasha wa.
An yi bikin rantsuwar ne a fadar gwamnatin jihar ranar Laraba, 20 ga watan Agusta, 2025, karkashin Kwamishinan Shari’a na Jihar, Barista Haruna Isah Dederi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

