EFCC Ta Baza Koma, Tana Neman Surukin Atiku Abubakar Ruwa a Jallo

EFCC Ta Baza Koma, Tana Neman Surukin Atiku Abubakar Ruwa a Jallo

  • Hukumar EFCC ta ayyana Bashir Haske, surukin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo
  • Hukumar ta bayyana cewa Haske, ɗan kasuwa mai shekaru 38, mai gidaje a unguwannin Ikoyi da Victoria Island ne da ke jihar Legas
  • EFCC ta roƙi al’umma su ba da duk wani bayani da zai taimaka wajen cafke shi ta hanyar tuntuɓar ofisoshinta ko kuma ta waya da imel

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa

FCT, Abuja – Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Ƙasa Ta'annati (EFCC) ta ayyana Abdullahi Bashir Haske, surukin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, a matsayin wanda take nema ruwa-a-jallo.

Hukumar ta zarge shi da laifuffukan da su ka hada da almundahana da haɗin baki wajen aikata laifi da kuma halatta kuɗin haram.

Kara karanta wannan

'Akwai matsala a N70, 000,' Amurka ta fitar da rahoto kan mafi karancin albashin Najeriya

Hukumar EFCC na neman surukin Atiku
Hoton Abdullahi Bashir Haske da EFCC take nema Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Source: Facebook

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da hukumar EFCC ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Alhamis 21 ga watan Agusta, 2025.

EFCC na neman surukin Atiku Abubakar

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya fitar ya ce suna buƙatar haɗin kan jama'a don cafke Abdullahi.

Sanarwar ta ce:

"Ana sanar da jama’a cewa Abdullahi Bashir Haske, wanda hotonsa yake sama, ana nemansa da laifi a gaban EFCC bisa zargin haɗin baki da kuma halatta kuɗin haram.”

EFCC ta ce matashin mai shekaru 38 yana da gidaje biyu a jihar Legas: lamba 6 a titin Mosley, Ikoyi, da kuma lamba 952/953 a titin Idejo, Victoria Island.

EFCC ta nemi taimako don kama surukin Atiku

Hukumar ta bukaci ‘yan Najeriya da su taimaka da bayanai don gano inda Abdullahi ya shiga ta hanyar bayar da sahihan bayanai.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta rufe shafukan 'yan Najeriya miliyan 13 a Facebook, Instagram da TikTok

Ta jaddada cewa za a iya tuntuɓar ofisoshinta a duk faɗin ƙasar nan, ciki har da Ibadan, Uyo, Sakkwato, Maiduguri, Benin, Makurdi, Kaduna, Ilorin, Enugu, Kano, Legas, Gombe, Fatakwal, da Abuja.

Shugaban hukumar EFCC Ola Olukayode
Hoton Shugaban Hukumar EFCC Hoton: Economic and Financial Crimes Commission
Source: Twitter

Haka kuma, hukumar ta bayyana cewa za a iya isar da bayani ta hanyar kiran wayar hukumar ko kuma ta imel domin isar da bayanan da za su kai ga cafke shi.

EFCC ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da gudanar da yaƙi da rashawa da almundahana, tare da neman goyon bayan jama’a wajen ganin an kama mutanen da ake tuhuma da aikata laifuka makamantan haka.

Hukumar EFCC ta tona asirin ƴan siyasa

A baya, kun ji hukumar EFCC ta bayyana cewa wasu ‘yan siyasa na amfani da makirci na musamman kafin su hau mulki domin kauce wa bincike daga hukumomi.

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana haka ne a wani taro da aka shirya tare da hadin gwiwar Hukumar Da’ar Ma’aikata (CCB) don karfafa yaƙi da cin hanci da rashawa.

Ya ce ‘yan siyasa suna bayyana kadarori da ba su mallaka ba a kafin su kama aiki domin su cimma manufa ta tara dukiya kafin a fara bincikensu da zargin wawashe kuɗin ƙasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng