Tinubu Ya Magantu daga Japan, Ya Fadi Abin da ba a Sani ba game da Gwamnatinsa
- Bola Tinubu ya ce Najeriya tana dakile matsalolinta a karkashin shugabancinsa, inda ya bukaci goyon bayan yan Najeriya a ketare
- Ya jaddada cewa ci gaban kasa ba na gwamnati kadai ba ne, ya bukaci yan Najeriya su zama jakadun kasa a waje
- Shugaba Tinubu ya ce an inganta fannin tattalin arziki, lafiya da fasfo, tare da jawo zuba jari domin samar da ayyukan yi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Yokohama, Japan - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya karawa yan Najeriya karfin guiwa kan gwamnatinsa bayan shekaru biyu a mulki.
Tinubu ya bayyana cewa Najeriya tana komawa kan turbar ci gaba a karkashin shugabancinsa duk da wasu kalubale da ake fuskanta.

Source: Facebook
Tinubu ya yaba kokarin gwamnatinsa a shekaru 2
Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin taro da wasu yan Najeriya mazauna Japan a taron kasa da kasa na Tokyo kan ci gaban Afrika (TICAD9), cewar Tribune.

Kara karanta wannan
Tsohon ministan Buhari ya yi magana game da mulki, 'yan adawa da halin da APC take ciki
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya jaddada kokarin da yake yi inda ya ce gwamnatinsa ta dauki matakin gina kasa mai dorewa.
Ya yi kira ga yan Najeriya da ke ketare da su ba da gudummawa wajen ilimi, bunkasa kudi da basirarsu domin karfafa ci gaban kasa.
A cewarsa, ci gaban kasa ba na gwamnati kadai ba ne, ya ce kowa na da rawar da zai taka wajen tabbatar da dorewar ci gaban Najeriya.
Shugaban ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fara aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da suka sa kasuwanci yake gogayya da wasu kasashen duniya da jawo sababbin masu zuba hannun jari a cikin kasa.
Ya ce yanzu samun fasfo ya fi sauki ga yan kasa ciki har da mazauna ketare, domin rage wahalar da ake fuskanta a baya.

Source: Facebook
Matakan da gwamnatin Bola Tinubu ke dauka
Haka kuma, Tinubu ya jaddada cewa gwamnatinsa ta dauki matakan bunkasa harkar lafiya domin rage yawon neman magani zuwa kasashen waje.
Ya bukaci yan Najeriya a ketare da su zama jakadu nagari ta hanyar wakiltar kasa da kyau a duk inda suka samu kansu.
Wasu daga cikin al’ummar Najeriya a Japan sun nuna jin dadinsu kan sauye-sauyen gwamnati, inda suka tabbatar da goyon bayansu ga Tinubu.
Yabon da Shugaba Tinubu ya samu a Japan
Shugaban kungiyar yan Najeriya a Japan, Emeka Ebogota, ya gode wa Tinubu bisa samun lokaci da ya dauka ya gana da su, cewar TheCable.
Ya kuma jaddada cewa yan kungiyar za su taimaka wajen tabbatar da nasarar shirye-shiryen gwamnati domin dorewar ci gaban kasa baki daya.
Gwamnatin Tinubu za ta horas da matasa 100,000
Mun ba ku labarin cewa an bude shafin daukar matasa 100,000 da gwamnatin tarayya za ta bai wa horo kan harkokin neman kudi a jihohi 36 da Abuja.
Ma'aikatar harkokin matasa ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da daraktar yada labarai, Misis Omolara Esan ta fitar.
Ta ce shirin zai rika ba matasan Najeriya 100,000 horo duk shekara kan harkokin kudi, kasuwanci, sana'o'i da zuba hannun jari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
