Farashin Litar Mai Ya Haura N1,000, NBS Ta Bayyana Jihohi 3 da Fetur Ya Fi Araha
- Hukumar ƙididdiga ta ƙasa NBS ta ce farashin lita ɗaya na fetur ya ƙaru daga N770.54 a Yulin 2024 zuwa N1,024.99 a Yulin 2025
- Jihohin Jigawa, Lagos da Sokoto ne suka fi tsadar man fetur inda lita ta kai sama da N1,100 duk da tagomashin da Lagos ke da shi
- Zamfara, Yobe da Kogi ne suka fi arahar man fetur yayin da rahoton ICIR ya nuna farashin ya ƙaru duk da ragin danyen mai a duniya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce matsakaicin farashin lita ɗaya na fetur ya ƙaru daga Naira 770.54 a Yulin 2024 zuwa Naira 1,024.99 a Yulin 2025.
An bayyana haka ne a cikin rahoton 'Nazarin farashin man fetur' na watan Yulin 2025, wanda hukumar NBS ta fitar ranar Alhamis a Abuja.

Kara karanta wannan
'Akwai matsala a N70, 000,' Amurka ta fitar da rahoto kan mafi karancin albashin Najeriya

Source: Getty Images
NBS ta bayyana cewa farashin litar fetur da ya kai N1,024.99 a Yulin 2025 ya nuna karin kaso 33.02 idan aka kwatanta da farashin N770.54 na Yunlin 2025, inji jaridar Punch.
NBS: Jihohin da suka fi tsadar fetur
Amma rahoton da NBS ta fitar, ya nuna cewa farashin litar fetur na Yulin 2025 ya ragu da kashi 1.22 idan aka kwatanta da N1,037.66 da aka sayar da litar a Yunin 2025.
A farashin da jihohi suka sayar fetur din, NBS ta ce jihar Jigawa ce aka fi sayar da man da tsada, inda lita ta kai har N1,107.52.
A Lagos, duk da kasancewarta cibiyar manyan ma’adanan mai, tashar jiragen ruwa da ma matatar Dangote, an sayar da litar fetur kan N1,100.29 a jihar.
Yayin da masu sharhi ke ganin cewa farashin man fetur ya kamata ya yi sauƙi a Lagos saboda an samu ragin kuɗin jigilarsa, rahoton NBS ya nuna akasin haka.

Kara karanta wannan
Gwamnati ta rufe shafukan 'yan Najeriya miliyan 13 a Facebook, Instagram da TikTok
A jihar Sokoto da ke Arewa maso Yammacin ƙasar, litar fetur din ta kai har Naira 1,100, wanda ya sa ta zama jiha ta uku a masu tsadar mai.
NBS: Jihohin da suka fi arahar man fetur
The Cable ta rahoto cewa jihohin Zamfara, Yobe da Kogi ne suka fi arahar man fetur a watan Yulin 2025, kamar yadda rahoton na NBS ya nuna.
Rahoton ya nuna cewa an sayar da litar man kan N884.63 a Zamfara, inda ta kai Naira 950.60 a Yobe da kuma Naira 986.67 a Kogi.
Idan aka kwatanta da bara, farashin matsakaicin lita ɗaya ya tashi daga N770.54 a Yuli, 2024 zuwa N1,024.99 a Yuli, 2025, abin da ya nuna ƙarin N254.45.

Source: Getty Images
Tsadar fetur duk da arahar danyen mai
Rahoton ya ƙara da cewa, yankin Arewa maso Yamma ne ya fi tsadar mai, inda lita ta kai N1,035.85, yayin da Arewa maso Gabas ta fi arahar man, inda aka sayar da lita kan N1,017.65.
Rahoton ICIR ya nuna cewa farashin litar fetur ya tashi daga N770.54 a Yulin 2024 zuwa N1,024.99 a Yulin 2025, duk da cewa matsakaicin farashin danyen mai a kasuwar duniya ya fadi daga Dala 85.15 kan kowace ganga a Yulin 2024 zuwa Dala 71.04 a Yulin 2025.

Kara karanta wannan
Kotu ta rufe asusun banki 4 da ake zargin na da alaka da tsohon shugaban NNPCL, Kyari
Ya zuwa yanzu, yaƙin Rasha da Ukraine da kuma tashin hankula a Gabas ta Tsakiya na ci gaba da janyo raguwar farashin danyen mai a kasuwar duniya.
Dangote ya rage farashin man fetur
A wani labarin, mun ruwaito cewa, fetur ya fara sauka a gidajen man yan kasuwa da na kamfanin NNPCL musamman a Legas.
Hakan dai na zuwa ne kwanaki kalilan bayan matatar Dangote ta yi ragin N30 a farashin da take sayar wa ya kasuwa a rumbun ajiya.
Sai dai har yanzu wasu na ganin kamata ya yi farashin litar fetur ya dawo tsakanin N200 zuwa N500 idan ana so talaka ya samu sauki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng