Ana Hasashen Kano, Kogi da Jihohin Arewa 11 Za Su Sha Ruwa da Tsawa Ranar Juma'a
- Hukumar hasashen yanayi ta kasa NiMet ta sanar da za a samu ruwan sama da tsawa a jihohin Arewa, ciki har da Kano, Katsina
- A safiya da yammacin Juma'a, rahoton ya nuna Abuja da jihohin Niger, Nasarawa, Benue, za su fuskanci ruwan sama mai karfi
- A kudancin Najeriya kuma, NiMet ta yi hasashen hadari, yayyafi da ruwan sama a jihohi da dama ciki har da Oyo, Enugu, Imo da Lagos
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar hasashen yanayi ta kasa (NiMet) ta fitar da hasashen ruwan sama da tsawa a gobe Juma'a, 22 ga Agusta, 2025.
A cewar rahoton da NiMet ta fitar a daren ranar Alhamis, 21 ga Agusta, 2025, za a samu ruwa da tsawa a jihohin Arewa da yayyafi a Kudu.

Source: Getty Images
Hasashen yanayi a wasu jihohin Arewa
Hukumar NiMet ta wallafa rahoton a shafinta na X, tana mai hasashen cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Za a samu ruwan sama da tsawa a wasu sassan jihohin Kano, Katsina, Kebbi, Taraba, Zamfara, Sokoto, da Kaduna a safiyar ranar Juma'a.
"Za kuma a samu ruwan sama hade da tsawa a mafi yawan jihohin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma a yammacin ranar."
Hasashen yanayi a yankin Arewa ta Tsakiya
A safiyar ranar Juma'ar, NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama mai matsakaicin karfi a sassan Abuja da jihohin Niger, Nasarawa, Benue, Kogi, Kwara, da Plateau.
A yammacin ranar kuwa, NiMet ta yi hasashen cewa:
"Za a samu ruwan sama hade da tsawa a babban birnin tarayya da kuma wasu sassan jihohin Nasarawa, Benue, Kogi, Kwara, Niger, Plateau."
Da wannan hasashen, ana iya cewa babu wata jihar Arewa da ake sa ran za ta fuskanci ambaliyar ruwa a gobe Juma'a.

Kara karanta wannan
NiMet: Za a sheka ruwan sama mai yawa a Kaduna, Neja da jihohin Arewa 13 ranar Talata
Hasashen yanayi a Kudancin Najeriya
A Kudancin kasar nan, NiMet ta yi hasashen cewa:
"Za a samu hadari da kuma yiwuwar ruwan sama a wasu sassan jihohin Oyo, Enugu, Imo, Abia, Akwa Ibom, Delta, da Cross River a safiyar Juma'a.
"Idan yamma ta yi har zuwa dare, za a samu yayyafi da ruwa marar karfi a wasu sassan jihohin Ogun, Osun, Ekiti, Ondo, Oyo, Enugu, Imo, Abia, Anambra, Ebonyi, Delta, Lagos, Rivers, Bayelsa, Cross River, da Akwa Ibom"

Source: Twitter
Shawarwarin hukumar NiMet ga jama'a
A cikin sanarwar, NiMet ta bayyana cewa:
"Ruwan sama na iya zuwa da iska mai ƙarfi; ku kasance masu lura da hakan tare da ɗaukar matakan kariya.
"Akwai bukatar direbobi su guji tuƙi a lokacin ruwan sama mai yawa domin kauce wa haɗurra. Sannan a guji neman mafaka karkashin bishiya don gudun faduwar rassa."
Hukumar ta kuma bukaci kamfanonin jiragen sama su nemi bayanan yanayin da suka shafi filayen jiragen sama daga NiMet domin tsara zirga-zirgar su.
Karanta rahoton a nan kasa:
Ruwa da iska ya kifar da kwale-kwale
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani jirgin ruwa ya gamu da hatsari a kauyen Zangwan Maje da ke ƙaramar hukumar Taura a jihar Jigawa.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 27 ga Yuli, 2025, lokacin da kwale-kwale da ke dauke da yara 15 daga gonar Jejin Gunka zuwa ƙauyensu ya kife a ruwa.
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da mutuwar mutum shida, tare da ceto bakwai a raye, har yanzu ana ci gaba da laluben ragowar mutum biyu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
