Bayan Kisan Masallata 32, Ƴan Ta'adda Sun Gindiya Sharadin Zaman Lafiya a Katsina

Bayan Kisan Masallata 32, Ƴan Ta'adda Sun Gindiya Sharadin Zaman Lafiya a Katsina

  • ‘Yan bindiga sun kakaba harajin Naira miliyan 15 kan garuruwan gundumar Almu da ke karamar hukumar Malumfashi, jihar Katsina
  • Kansilan gundumar Almu, Usman Usman ya ce yanzu haka ana karbar N10,000 daga kowane gida don hada wa miyagun kudin
  • Usman ya ce 'yan bindigan sun sha alwacin ci gaba da kai hare-hare tare da hana mutane zuwa gona ma damar ba a biya harajin ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina – ‘Yan bindiga sun kakaba haraji na Naira miliyan 15 kan mutanen garin Almu da ke ƙaramar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.

Kansilar gundumar Almu, Usman Usman, wanda ya bayyana hakan ya nuna damuwa kan tsanantar hare-haren ‘yan bindiga a yankin.

'Yan bindiga sun kakaba harajin N15m kan garuruwan Katsina bayan kisan mutane 32
Taswirar jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan bindiga sun kakaba haraji a Katsina

A zantawarsa da jaridar Leadership, Usman Usman ya ce 'yan bindiga sun koma farmakar garuruwansu a kullum, suna kashe na kashe wa, suna garkuwa da wasu.

Kara karanta wannan

Gudaji Kazaure da manyan ƴan siyasa 7 da suka hango faduwar Tinubu da APC a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, ‘yan ta’addan Boko Haram sun bukaci Naira miliyan 10 da kuma babura Honda guda biyu daga kauyuka kusan takwas zuwa tara, abin da ya kai kimanin Naira miliyan 15 baki ɗaya.

Ya jaddada cewa manoma za su samu damar zuwa gona ne kawai daga ƙarfe 8:00 na safe zuwa 1:00 na rana idan sun bi sharuddan ‘yan ta’addan.

“Sun shaida mana cewa wannan shi ne sharadin sulhu idan muna son zuwa gona cikin lumana ba tare da hare-hare ba,” inji Usman Usman.

Kansilan ya ƙara da cewa an yanke hukuncin cewa kowane gida zai bayar da N10,000 domin biyan tarar, amma duk da haka ‘yan ta’addan ba su daina kai hare-hare kan mutane ba.

Mutanen Katsina na tsere wa daga gidajensu

Usman Usman ya bayyana cewa:

“Jiya an kai hari a garuruwa biyu. Sun kwashe wayoyi, kuɗi tare da yin garkuwa da mutane da dabbobi. Duk lokacin da suka zo sai sun tafi da mutane uku zuwa biyar da kuma dabbobi."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe fiye da mutum 10, sun raba dubban mutane da gidajensu a Filato

Kansilan ya ce yanzu jama’a sun fara yanke tsammani daga gwamnati, suna ganin kamar an barsu ba tare da wani dauki ba yayin da 'yan bindigar suka mamaye su.

Ya ƙara bayyana cewa mazauna garuruwa 16 suna tsere wa kullum zuwa garuruwa irin su Dayi da Malumfashi, suna barin gidajensu idan dare ya yi.

Ya ce:

"Sai idan safiya ta yi ne za ka ga mutane suna dawowa garuruwansu suna zuwa gona, shi ma na dan wani lokaci ne, kafin rana ta fadi."

Hare-haren 'yan bindiga a jihar Katsina

Ya bayyana cewa ‘yan bindigar suna da sansani a yankin ƙaramar hukumar Kankara, musamman wuraren Wawa Kaza da Gimi, inda ya roki a gaggauta tura jami’an tsaro don kakkabe su.

A cikin makon da ya gabata, ɗan majalisar ya ce mutane da dama sun rasa rayukansu yayin da wasu ke kwance a asibiti suna jinya.

“A Gidan Mantau, an kashe mutane 27 zuwa 30, yayin da a a garin Almu aka kashe kwamandan CJTF,” inji Usman.
Kansilar Almu, Usman Usman ya ce mutane sun fara yanke tsammani daga gwamnati.
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda a ranar da ya kai ziyara ofishin NIPC a Abuja. Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Mazauna Karadua sun yi magana

A zantawar Legit Hausa da wata majiyar tsaro a yankin Karadua, watau shiyyar Funtua wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce 'yan bindiga sun riga sun gano lagon mutanen Katsina.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ta'asa a Plateau, an kashe mutane tare da bankawa gidaje wuta

Majiyar ta ce tun daga lokacin da garuruwa suka fara yin zaman sulhu da 'yan bindiga, hare-haren wulakanci suka karu, maimakon a ga sauki.

Ta ce:

"Idan mutane suka yi sulhu da dabar wane, to gobe sai ka ga wata dabar ta zo tana ta'addanci, ka ga an gudu ba a tsira ba kenan.
"Mutanen nan ('yan bindiga) fa ya su ya su ma fa fada suke yi, to don me za a yi tunanin cewa sulhu da kungiya daya shi zai kawo zaman lafiya a garuruwanmu?
"Yanzu ka ga wata dabar ta sanya harajin miliyoyin kudi da babura kan garuruwan Almu, kuma ba su ne suka gashe mutane masu yawa a masallacin garin Gidan Mantau, ke nan a Malumfashi akwai dabobin yan ta'adda da dama."

Majiyar ta roki gwamnatin Katsina ta taimaka ta samar da tsaro kamar yadda Gwamna Dikko Radda ya yi alkawarin a lokacin yakin neman zabe.

Wata Nafisa Abdullahi a Funtua, ta ce 'yan bindiga yanzu sun fara shiga Funtua, Inda suke kai hari Unguwar Dahiru, Bagari, Sabuwar Abuja, Bye Pass da sauran yankunan da suka zagaye cikin garin Funtua.

Kara karanta wannan

Duk da yin sulhu, 'yan bindiga sun kashe manoma a Kaduna

Nafisa ta ce:

"Wallahi kullum muna cikin zulumi, yau ne, gobe ne, abin kullu kara karuwa yake yi. Gaskiya ya kamata gwamnati ta dauki mataki."

An san makasan masallata 32 a Katsina

Tun da fari, mun ruwaito cewa, dan majalisar wakilai daga Katsina, Sada Soli Jibia ya yi ikirarin cewa an san yan bindigar da suka kashe masallata akalla 30.

Hon. Sada Soli ya bayyana cewa yan bindigar da suka kashe masallatan a garin Malumfashi su na rike da wani yanki a jihar Katsina da ake yawan ta'adi.

Gwamnatin jihar Katsina dai ta bayyana cewa adadin wadanda aka kashe a harin da 'yan bindiga suka kai masallaci a Malumfashi ya karu zuwa 32.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com