Ana Kukan Kisan Masallata a Katsina, Gwamna Radda Ya Nada Sababbin Hadimai 15
- Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda na jihar Katsina ya sanar da nadin sababbin mataimaka na musamman guda 15
- Wadanda aka nada suna da kwarewa a fannoni daban-daban, kuma za su taimaka wajen aiwatar da shirin “Gina makomarka”
- Radda ya bukaci sababbin jami’an da su nuna ƙwazo da jajircewa wajen yi wa jama’ar Katsina aiki cikin gaskiya da amana
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya amince da nadin sababbin manyan mataimakan na musamman har guda 15.
Hakazalika, mai girma Dikko Radda ya nada sabon shugaban hukumar otel otel na Katsina domin ƙarfafa jajircewar gwamnati wajen samar da sauye-sauyen mulki a fadin jihar.

Source: Facebook
Gwamna Radda ya nada hadimai 15
Mai magana da yawun gwamnan Katsina, Ibrahima Kaulaha Mohammed ne ya sanar da nadin a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 21 ga Agusta, 2025.
Sanarwar ta ce Gwamna Dikko ya zakulo wadanda aka yi wa nadin ne bayan nazari kan kwarewarsu a fannoni daban daban.
Manufar nade-naden shi ne aiwatar da shirin Gwamna Radda na "Gina makomarka da kanka," tare da tabbatar da isar da ayyukan gwamnati ga al'umar Katsina.
Sababbin hadiman sun shiga jerin masu tallafawa Gwamna Radda domin sauke nauyin shugabanci da ke kansa da kuma cika alkawurran da ya dauka.
Sunayen wadanda Gwamna Radda ya nada
Sanarwar ta ce:
“Gwamna Radda ya umarci sababbin jami’an da su rungumi shirin ‘Gina makomarka da kanka’ tare da nuna ƙwazo da jajircewa wajen yi wa jama’ar Katsina aiki cikin gaskiya, riƙon amana, da kwarewa.”
Sababbin manyan mataimaka na musamman da Gwamna Dikko Radda ya nada su ne:
- Hajiya Aisha Barda – Babbar mataimakiya ta musamman kan ciyar da dalibai,
- Musa Ado Faskari – Babban mataimaki na musamman kan CDP/Kodinetan Faskari/Kankara/Sabuwa,
- Nu’uman Imam Muhammed – Babban mataimaki na musamman kan CDP/Kodinetan Batagarawa/Charanchi/Rimi,
- Dr. Habibu AbdulKadir – Babban mataimaki na musamman kan CDP/Kodinetan Matazu/Musawa,
- Ali Mamman Bakori – Babban mataimaki na musamman kan CDP/Kodinetan Bakori/Danja,
- Labaran Magaji Ingawa – Babban mataimaki na musamman kan CDP/Kodinetan Ingawa/Kankia/Kusada,
- Bishir Sabi’u – Babban mataimaki na musamman kan CDP/Kodinetan Jibia/Kaita,
- Murtala Adamu Baure – Babban mataimaki na musamman kan CDP/Kodinetan Baure/Zango,
- Yusuf Mamman Ifo – Babban mataimaki na musamman kan CDP/Kodinetan Batsari/Danmusa/Safana,
- Sanusi Dangi Abbas – Babban mataimaki na musamman kan harkokin tsaro,
- Faruk Hayatu – Babban mataimaki na musamman kan ci gaban matasa,
- Bala Garba Tsanni – Babban mataimaki na musamman kan ci gaban jama’a,
- Musa Maikudi – Babban mataimaki na musamman kan harkokin jam’iyya,
- Aminu Ashiru Kofar Sauri – Babban mataimaki na musamman kan shirin SPIME,
- Mannir Shehu Wurma – Babban mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai,
- Rabi’u Aliyu Kusada – Shugaban hukumar otel otel na Katsina.

Source: Twitter
'Yan bindiga sun kashe masallata a Katsina
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kashe mutane akalla 13 su na tsakiyar sallar Asubah a kauyen Unguwan Mantau da ke Malumfashi a Katsina.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Katsina, Dr. Nasir Mu'azu ya bayyana harin a matsayin na ramuwar gayya.
Dr. Nasir Mu'azu ya ce kwanaki biyu da suka wuce mazauna kauyen suka yi wa yan bindiga kwantan bauna, suka kashe da dama suka ceto yan uwansu.
Asali: Legit.ng

