Tinubu Ya Dawo da Shirin GEEP da Mutane ke Samun Tallafin Kudi da Bashi a Najeriya

Tinubu Ya Dawo da Shirin GEEP da Mutane ke Samun Tallafin Kudi da Bashi a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta dawo da shirin GEEP wanda ke bai wa kananan yan kasuwa rancen kudi da kuma tallafi a Najeriya
  • An sauya fasalin shirin zuwa RHGEEP 3.0 kuma ana sa ran 'yan Najeriya miliyan biyar za su amfana daga nan zuwa 2027
  • NSIPA ta bayyana cewa an dauki darussa daga GEEP 1.0 da 2.0 kuma za a dauki matakin fadadawa da inganta sabon shirin a zagaye na uku

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da zagaye na uku na shirin tallafa wa kananan sana’o’i da ake kira Government Enterprise and Empowerment Programme (GEEP).

Gwamnatin ta canza wa shirin suna zuwa Renewed Hope GEEP (RHGEEP 3.0), tare da burin tallafawa yan Najeriya masu kananan san'o'i miliyan biyar daga nan zuwa 2027.

Wurin taron aiwatar da shirin GEEP 3.0.
Hotun wurin taron kaddamar da shirin GEEP karo na 3 da aka radawa suna RHGEEP 3.0 Hoto: @Abduldanja08
Source: Twitter

Shugaban Hukumar Kula da Shirye-Shiryen Tallafi da Jinkai (NSIPA), Malam Badamasi Lawal ne ya sanar da hakan a taron masu ruwa da tsaki a Abuja ranar Alhamis, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Kamfanin Amurka ya kawo shirin da za a tallafa ma matasa sama da 300,000 a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya dawo tare da fadada shirin GEEP

Malam Badamasi Lawal, ya bayyana cewa a sabon zagayen shirin, za a sake fasalin tsarin bisa ginshiƙai uku, aminci, daidaito, da gaskiya.

Ya ce:

"Taruwar mu a nan ta nuna karfin hadin kai da jajircewar da muka yi wajen samar da tsarin rance ga kananan yan kasuwa, da tallafawa mata, matasa, kananan ma'aikata da masu sana'ar hannu."

Badamasi Lawal ya bayyana cewa tun farko an kirkiro shirin GEEP ne a ƙarƙashin hukumar (NSIP) da nufin samar da ƙaramin bashi da tallafin kuɗi ga miliyoyin ‘yan Najeriya.

Tsare-tsaren da ke karkashin shirin GEEP

A cewarsa, ta hanyar shirye-shiryen TraderMoni, MarketMoni, da FarmerMoni, GEEP ya taimaka wajen bunƙasa kananan sana’o’i, tallafawa maraaa kargi, tare da samar da dama ga waɗanda aka bari a baya.

Ya kuma bayyana cewa duk da nasarorin da aka samu a GEEP 1.0 da 2.0, sabon shirin RHGEEP 3.0 ya zo da sauyi na musamman.

Kara karanta wannan

Najeriya ta samu rancen $238m daga Japan, minista ya lissafa ayyukan da za a yi

“Manufarmu ita ce wadanda za su ji gajiyar shirin nan su kai mutane miliyan biyar nan da 2027, tare da kafa kyakkyawan tsarin biyan bashi.
"Wannan buri ne mai girma da wahala amma babu abin da ba za mu iya cimma ba idan muka haɗa kai,” in ji shi.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Hoton shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wurin taro a Abuja Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Yadda NSIPA ta shirya inganta shirin RHGEEP

Ya ƙara da cewa darussan da suka dauka daga shirin baya sun nuna akwai bukatar tabbatar da gaskiya da lissafi, da samar da ingantaccen tsarin maido da bashi.

Malam Badamasi ya kara da cewa za su yi haɗin gwiwa da kamfanonin fasaha da kuma zurfafa haɗin kai da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi don inganta shirin.

Wani matashi daa ya amfani da shirin GEEP run na farko, Abdulhafiz Ahmed ya shaidawa Legit Hausa cewa tsarin yana da kyau duk da bashi ne, amma dai ya kamata a sabunta shi

A cewarsa, a wancan lokacin da aka ba su N50,000 kudi na da daraja amma yanzu ba za su yiwa mutum komai ba.

"Shirin GEEP ya taimake ni gaskiya, tun na farko aka bani rancen N50,000, kudin sun mani amfani ba kadan ba, amma yanzu darajar kudin ta ragu, ya kamata a gyara.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba za ta yi wa tubabbun 'yan daba auren gata a Kano

"Za mu jira muga tsare-tsaren wannan da za a yi, ina so gaskiya amma na fi son a bani kudi masu nauyi da zan kara jari," in ji shi.

Yadda matasa za su yi rijista a sabon shirin gwamnati

A wani labarin, kun ji cewa an bude shafin daukar matasa 100,000 da gwamnatin tarayya za ta bai wa horo kan harkokin neman kudi a jihohi 36 da Abuja.

Shirin zai ba matasa cikakken horo a muhimman fannoni na kasuwanci da zuba jari a duniya, kamar su tallar haja, harkokin ma'adanai, da kasuwancin musayar kuɗi da sauransu.

Ma'aikatar harkokin matasa ta bayyana yadda za a yi rijista domin shiga wannan shiri na matasa, ta ce kyauta gwamnati za ta taimakawa mutane.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262