Tsohon Ministan Buhari Ya Yi Magana game da Mulki, 'Yan Adawa da Halin da APC Take Ciki

Tsohon Ministan Buhari Ya Yi Magana game da Mulki, 'Yan Adawa da Halin da APC Take Ciki

  • Tsohon Ministan wutar lantarki, Injiniya Abubakar D. Aliyu ya bayyana abin da ya zama matsala ga samun sahihin ci gaba a Najeriya
  • Ya bayyana cewa da mummunan hali da wasu daga cikin talakawan Najeriya ke da shi za su mulki kasar nan idan su ka samu dama
  • Ya yi kira ga ‘yan siyasa da al’umma su yi haƙuri da juna, domin siyasar cin mutunci ba za ta haifar da ci gaban da kasa ke bukata ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, AbujaTsohon ministan lantarki a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Injiniya Abubakar D. Aliyu, ya bayyana cewa 'yan kasar nan su ne matsalar Najeriya.

A cewar tsohon ministan, ko da mutum ya samu mukami mai muhimmanci, zai yi aiki da irin halayensa da ya saba dasu tun kafin hawa kujerar mulki.

Kara karanta wannan

Sheikh Daurawa ya jero abubuwa 7 da za su karawa mace daraja

Injiniya Abubakar D. Aliyu, tsohon Minista a zamanin Muhammadu Buhari
Tsohon Minista lantarki, Injiniya Abubakar D. Aliyu Hoto: Engr. Abubakar D. Aliyu, CON, FNSE, FNICE
Source: Facebook

A wata hira da ya yi da BBC Hausa da aka wallafa a shafin Facebook, Injiniya Abubakar ya ce matukar ana son a samu canjin da ake marari, dole kowa ya sake hali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan Buhari ya magantu kan mulkin kasa

Da yake magana kan siyasar Najeriya, Aliyu ya bayyana cewa dole sai an yi hakuri da juna tare da gudanar da siyasa ba tare da gaba ba, domin kasa ta samu ci gaba.

Ya ce hali shi ne abokin rayuwa, kuma rashin hali mai kyau ba zai kawo ci gaba ga siyasar Najeriya ko ya samar da ci gaban kasa ba.

A cewarsa:

“Matsalar tana kanmu ne ‘yan Najeriya gaba ɗaya. Idan za mu duba halayenmu mu canza, mu yi hali mai kyau. Idan ba haka muka yi ba, ba za mu samu ci gaba a kasar nan ba.”
“Mu ‘yan Najeriya ne muke yin jam’iyyun. Babu wani ɗan Togo ko ɗan Ghana ko ɗan Amurka da za a kawo ya shugabanci Najeriya. Mu ne za mu shugabanci kanmu.”

Kara karanta wannan

Babbar magana: Gwamnan Neja ya ce za su daina tura shanu Kudancin Najeriya

Ya ƙara da cewa:

“Ka fita bakin kwalta ka ga yadda ‘yan Najeriya suke. Idan aka ɗauke ka, aka kai ofis da wannan hali, haka za ka yi. To me ya sa ba za mu canza halayenmu gaba ɗaya ba?”

Tsohon minista ya magantu kan rikicin APC

Injiniya Abubakar D. Aliyu ya nanata cewa babu wata baraka da za ta kawo wa jam’iyyar APC matsala, kamar yadda aka gani a zaben cike gurbi da ya gabata.

Tsohon Ministan lantarki a Najeriya
Tsohon Minista, Injiniya Abubakar D. Aliyu lokacin yana ofis Hoto: Engr. Abubakar D. Aliyu, CON, FNSE, FNICE
Source: Facebook

Ya ce:

“Siyasa a Najeriya akwai yadda ake yinta. Amma ummul abasin matsalar shi ne hali. Idan ba za mu canza halayenmu ba, ba za mu ci gaba ba.”

Ya ce ba wai saboda yana cikin APC ne ya yi wannan magana ba, amma don shi da sauran ‘yan Najeriya suna cikin jam’iyyar ne suke gudanar da ita.

Injiniya Abubakar D. Aliyu, ya shawarci ‘yan siyasa kan muhimmancin zama tsintsiya madaurinki ɗaya domin samun ci gaba.

Kara karanta wannan

An bukaci a kashe Bello Turji kamar Shekau duk da ya nemi ya Mika Wuya

A kalamansa:

“Babban shawarar da zan bayar shi ne mu yi hakuri da junanmu. Shugabanni su haɗa kai domin ganin yadda za a samar da ci gaba. Siyasa ta gaba ba za ta kai mu ko ina ba. Idan ka zo kana da lokaci, sai ka yi ka tafi. Wannan shi ne dalilin da yasa ake sauya shugabanci, domin wani ya dora inda wani ya tsaya.”

Yadda aka cire Ministan Buhari da yana gwamna

A wani labarin, kun samu labarin cewa tsohon gwamnan jihar Anambra, Sanata Chris Ngige, ya bayyana dalilin da ya sa aka cire shi daga kujerar gwamna a shekarar 2006.

Ya bayyana cewa ya samu matsala ne saboda ya ki amince wa da daukar Chris Uba a matsayin mataimakinsa, mutumin da ya ke ganin zai iya cutar da shi kai tsaye.

Sanata Ngige, wanda ya riƙe mukamin Ministan Kwadago a gwamnati mai mulkin Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa bai yi nadamar wannan tsari ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng