Sarkin Musulmi Ya Yi Magana kan Nada Tsohon Gwamna a Matsayin Sarki Mai Daraja a Najeriya

Sarkin Musulmi Ya Yi Magana kan Nada Tsohon Gwamna a Matsayin Sarki Mai Daraja a Najeriya

  • A jiya Laraba, 20 ga watan Agusta, 2025, Gwamnan jihar Oyo ya kara tabbatar da nadin Rashidi Lodoja a matsayin sabon Sarkin Ibadan
  • Gwamna Seyi Makinde ya tabbatar da hakan ne a lokacin da ya kai masa ziyara har gidansa da ke Bodija a Ibadan, babban birnin jihar Oyo
  • Sarkin musulmi ya yabawa gwamnan bisa amincewa da zabin jama'a, yana mai cewa sabon Sarkin yana da gogewa a fannoni daban-daban

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Sarakuna ta Ƙasa (NTRCN), Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya taya sabon Sarkin Ibadan murna.

Sultan ya yaba da nadin Alhaji Rashidi Adewolu Ladoja, a matsayin Olubadan na 44 na Ibadanland da ke jihar Oyo a Kudu maso Yammacin Najeriya.

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III.
Hoton mai alfarma Sarkin Musulmi a fadarsa a Sakkwato Hoto: Daular Usmaniyya
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Alhaji Sai’idu Maccido, Sakataren Fadar Sarkin Musulmi, ya rattaba wa hannu a safiyar Alhamis, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Jakadan Najeriya ya rasu a lokacin da ba a yi tsammani ba

Tsohon gwamna na shirin zama Sarkin Ibadan

Sarkin Musulmi ya yi farin ciki da nasarar da sabon sarkin ya samu, wanda zai gaji marigayi Oba Akinloye Owolabi Olakulehin da ya rasu a ranar Litinin, 7 ga Yuli, 2025.

Tun farko dai majalisar masu nadin sabon Olubadan sun zabi, Rashidi Ladoja, tsohon gwamnan jihar Oyo a matsayin Sarki na 44.

Gwamma Seyi Makinde na jihar Oyo ya amince da wannan zabi na Majalisar sarakunan a lokacin da ya kai wa Ladoja ziyara a gidansa jiya Laraba, rahoton Arise tv.

Sarkin Musulmi ya ce gogewar Oba Ladoja ya samu a tsawon rayuwarsa ta kasuwanci, noma, tsohon ɗan majalisar tarayya, da kuma matsayin da ya rike na Gwamnan Jihar Oyo zai taimaka masa.

Sarkin Musulmi ya taya Olubadan na 44 murna

“Muna taya sabon Olubadan na Ibadanland murna, wanda muka dade muna da kyakkyawar alaƙa da shi.

Kara karanta wannan

An gama shirye shirye, tsohon gwamna zai zama sabon Sarki mai martaba a Najeriya

"A matsayinsa na shugaba mai tsoron Allah, mai kishin zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Najeriya, muna da tabbacin cewa Oba Alhaji Rashidi Adewolu Ladoja zai ba marada kunya wajen jagorantar al’ummarsa.”

- In ji Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III.

Oba Ladoja da Sarkin Musulmai.
Hoton sabon Sarkin Ibadan mai jiran gado da mai alfarma Sarkin Musulmi Hoto: Daular Usmaniyya
Source: Facebook

Sarkin Musulmi ya yabawa Gwamna Makinde

Sarkin Musulmi ya kuma jinjina wa Gwamnan Jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, bisa bin muradun jama’a wajen tabbatar da sabon Olubadan, tare da yi masa fatan alheri.

Ya roƙi Allah Ya ci gaba da jagorantar Gwamna Makinde a tafarkin alkhairi, ya kuma taimaki sabon Olubadan wajen samun nasara a matsayin da zai hau na jagorantar al'umma.

An sanya ranar da za a nada Sarkin Ibadan

A wani labarin, kun ji cewa an sanya ranar bikin nadin sabon Sarkim Ibadan, Rashidi Ladoja bayan amincewar majalisar sarakuna da mai girma gwamnan Oyo.

Bayanai sun nuna cewa za a naɗa tsohon gwamna, Rashidi Ladoja a matsayin Olubadan na 44 na Ibadan, babban birnin jihar Oyo a ranar Juma'a 26 ga watan Satumba, 2025.

An tattaro cewa tuni tawagar gwamnatin jihar Oyo ta gana da Ladoja da sauran mambobin majalisar masarautar a gidansa da ke Bodija a ranar Laraba domin tattaunawa kan bikin madin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262