Ana Batun Ƙarin Albashi, an Buƙaci Shugaba Tinubu, Masu Mukamai Su Yi Murabus
- Wani 'dan gwagwarmaya mai kokarin ganin sauyi ya yi magana kan neman karawa Bola Tinubu albashi
- Hamzat Lawal ya ce shugabanni da ke neman karin albashi su yi murabus su koma kasuwanci
- Ya bayyana cewa shirin karin albashin na iya zama makarkashiya domin ya ɓata wa Tinubu suna
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Shugaban ƙungiyar 'Follow The Money', Hamzat Lawal ya caccaki yan siyasa da ke neman karin albashi.
Hamzat ya ce duk wani ɗan siyasa da ke son a ƙara masa albashi ya yi murabus ya koma harkar kasuwanci.

Source: Facebook
An bukaci Tinubu, yan siyasa su yi murabus
Hamzat ya yi wannan magana ne yayin shirin Morning Brief na Channels TV ranar Alhamis 21 da watan Agustan 2025.
Matashin yana magantu e kan shirin Hukumar RMAFC na duba albashin manyan jami’an gwamnati, ciki har da na Shugaba Bola Tinubu

Kara karanta wannan
Tsohon ministan Buhari ya yi magana game da mulki, 'yan adawa da halin da APC take ciki
Ya ce:
“Na fahimci cewa a tsawon shekaru 33 ba a sake duba albashin ba, amma wannan ba shi ne lokacin yin hakan ba; ƙasar ba ta da hali.
“Idan ‘yan siyasa suna ganin ba a biyan su yadda ya kamata, su yi murabus, su je neman aiki ko su kafa kamfanoni su biya kansu albashi.
“Su daina ɗora wa ‘yan Najeriya nauyin da ya riga ya yi yawa."

Source: Facebook
An soki maganar karawa Tinubu albashi
Ya ce aikin hukumar RMAFC shi ne duba amfanin kuɗin gwamnati da kuma ba da shawara kan yadda za a zuba jari mai tasiri a gine-gine.
"Wannan batun ba komai ba ne face neman farin jini; don faranta wa Shugaba rai, ba tare da bin kundin tsarin aiki ba.
“Ban san dalilin da ya sa ba su yi magana ba kan yadda aka yi da kasafin kuɗi ko kuma yadda aka kashe kuɗaɗen gwamnati ba.

Kara karanta wannan
'Akwai matsala a N70, 000,' Amurka ta fitar da rahoto kan mafi karancin albashin Najeriya
“Sun yi kuskuren fifiko, ya kamata su maida hankali kan ayyukan kundin tsarin mulki maimakon neman karin albashi."
- Cewar Hamzat
Lawal ya ce yana ganin wannan shiri a matsayin rashin tausayi da kuma makirci na sanya Tinubu cikin bakin ciki da rashin farin jini.
Hamzat ya ce:
“Dalilin menene talakawa kawai za su ɗauki nauyi? Me ya sa ba a tattauna kan alawus da kuɗin tafiyar aiki na shugabanni ba?
“Wasu daga cikinsu ma suna hawa motocin sulke. Wannan rashin tausayi ne kuma zai zama siyasa idan aka amince da shi.”
Ya ce kamata ya yi a ƙara wa kananan hukumomi kuɗaɗe ta hanyar ba su cikakken ‘yanci domin su gudanar da ayyukan da suka dace.
An fadi albashin Tinubu, Kashim a Najeriya
Kun ji cewa shugaban hukumar tattara kudin shiga da raba su, RMAFC, Muhammed Shehu ya ce albashin shugabanni bai da yawa.
Shehu ya bayyana cewa shugaban kasa na karbar kasa da N1.5m a wata, yayin da wasu ma’aikatan CBN ke karbar kudi fiye da ministocin tarayya.
Rahotanni sun bayyana yadda albashin ministoci da hadimai ke da yawan kudi kuma hakan na iya gyara wasu bangarori idan an sake zuba su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng