Gwamnatin Abba za Ta Yi wa Tubabbun 'Yan Daba Auren Gata a Kano

Gwamnatin Abba za Ta Yi wa Tubabbun 'Yan Daba Auren Gata a Kano

  • Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da shirin tallafa wa matasan da su ka zubar da makamansu, su ka tuba daga ayyukan daba
  • Shugaban hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa an fara shirin sanya matasan a tsarin auren gatan gwamnatin jihar
  • Gwamnatin jihar za ta haɗa hannu da NDLEA wajen tantancewa da kuma shigar da su cikin shirye-shiryen bayar da tallafi don dogaro da kai

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoHukumar Hisbah ta Kano ta bayyana cewa za ta ɗauki nauyin aurar da matasan da su ka tuba daga ayyukan daba a jihar.

Kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga wasu matasa da suka yi watsi da harkar daba da tayar da zaune tsaye a Kano.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta bude shafin daukar matasa 100,000, ta fadi alherin da za su samu

Sheikh Aminu Daurawa
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, wasu daga cikin matasan da su ka daina daba Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Source: Facebook

PM News ta wallafa cewa Sheikh Daurawa ya bayyana cewa shirin na cikin manufofin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na inganta rayuwar matasan.

Gwamnatin Kano za ta aurar da matasa

Daily post ta wallafa cewa Sheikh Daurawa ya kara da cewa matakun aurar da su da sauran matakan da gwamnatin Kano ke shirin dauka wai yunkuri ne na ganin matasa sun samu rayuwa mai inganci.

Ya kara da cewa:

“Wannan shiri wani ɓangare ne na manufofin Gwamna Abba Kabir Yusuf domin tallafa wa matasan da suka daina aikata laifuka kuma suke son rayuwa mai tsafta."

Sheikh Daurawa ya ƙara da cewa wannan yunƙuri ba wai kawai za a tsaya a wajen aurar da matasan ba, za a kuma buɗe musu hanyoyi daban-daban na samun ilimi da kuma dogaro da kai.

Gwamnati ta nusar da matasan Kano

A ci gaba da jawabinsa, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya kuma yi kira ga sauran matasa da ke cikin harkar daba da su guji wannan hali.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta bullo da shirin afuwa ga 'yan daba, ta fadi wadanda za su amfana

Ya kwadaitar da su cewa gwamantin Kano a shirye ta ke wajen taimaka masu su zama 'yan kasa na gari, tare da zama mutanen kwarai ga kawunansu.

Da ya ke fadin alherin shirin gwamnati na karbar tubabbun 'yan daba, Sheikh Daurawa ya ce shirin zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a cikin al’umma tare da rage yawan aikata laifuffuka.

Gwamnatin Kano ta karbi tubabbun 'yan daba
Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf (D), Wasu daga cikin tubabbun 'yan daba (H) Hoto: Abba Kanir Yusuf/Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

A wani ɓangare na wannan tsari, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa hukumar NDLEA za ta fara wani shirin tantancewa da don taimaka wa tsofaffin 'yan daban.

Ya ce za a yi bincike kan matasan da su ka tuba domin tabbatar da gaskiyar nadamar su kafin a haɗa su da shirye-shiryen tallafi da kuma aurar da su.

Gwamnatin Kano na yi wa 'yan daba afuwa

A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa ta ƙaddamar da shirin “Safe Corridor” inda an riga an yi rajista da tantance matasa 718, da su ka ajiye aikin daba.

Ta bayyana cewa a yanzu haka, akwai wasu matasan akalla 960 da ke jiran tantancewa daga ‘yan sanda kafin a haɗa su cikin shirin da ake sa ran zai maido su turbar zama mutanen kwarai.

Kwamishinan Yada Labarai, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana damuwar Gwamna Abba Kabir Yusuf kan matsalar daba da illolin da ta ke haddasa wa a sassan jihar Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng