Gwamnatin Tinubu Ta Bude Shafin Daukar Matasa 100,000, Ta Fadi Alherin da Za Su Samu

Gwamnatin Tinubu Ta Bude Shafin Daukar Matasa 100,000, Ta Fadi Alherin da Za Su Samu

  • An bude shafin daukar matasa 100,000 da gwamnatin tarayya za ta bai wa horo kan harkokin neman kudi a jihohi 36 da Abuja
  • Ma'aikatar harkokin matasa ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da daraktar yada labarai, Misis Omolara Esan ta fitar
  • Ta ce shirin zai rika ba matasan Najeriya 100,000 horo duk shekara kan harkokin kudi, kasuwanci, sana'o'i da zuba hannun jari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin Tarayya bude shafin yanar gizo domin daukar matasa 100,000 da za a horar da su harkokin daban-daban da za su taimaka masu wajen dogaro da kai.

A karkashin shirin na musamman da gwamnatin ta bullo da shi, za a bai wa matasa horon ilimi kan harkokin kuɗi kyauta a fadin jihohi 36 da Abuja.

Shugaba Bola Tinubu.
Hoton shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana jawabi a wurin taro Hoto: @officialABAT
Source: Facebook

Tribune Nigeria ta rahoto cewa shirin zai koyar da matasa 100,000 a kowace shekara kan batutuwan da suka shafi ilimin kuɗi, kasuwanci, sana’o’in dogaro da kai da kuma zuba jari.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba za ta yi wa tubabbun 'yan daba auren gata a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan shiri zai gudana ne tare da haɗin gwiwar Investonaire Academy, kamar yadda daraktar yada labarai da hulɗa da jama’a na Ma’aikatar harkokin Matasa, Mrs. Omolara Esan, ta bayyana a Abuja.

Me gwamnatin Najeriya za ta koyawa matasan?

Esan ta ce shirin zai ba matasa cikakken horo a muhimman fannoni na kasuwanci da zuba jari a duniya, kamar su tallar haja, harkokin ma'adanai, da kasuwancin musayar kuɗi da sauransu.

“Wannan shiri wata manufa ce da ke nuna jajircewar ma’aikatar wajen baiwa matasan Najeriya ilimi da kwarewa da suka dace domin su yi nasara a duniya.
"Ta hanyar fadada damar samun ilimin kuɗi, shirin zai taimaka wajen canza rayuwa, samar da damarmakin aiki da kuma gina arziki mai ɗorewa a ƙasar nan.”

- In ji Omolara Esan.

Esan ta bayyana cewa waɗanda suka kammala horon za su samu takardar shaidar kwarewa da ake amincewa da ita a harkar kasuwanci.

Kara karanta wannan

Tallafin wankin koda: Gaskiya ta fito kan zargin Tinubu da ware Kano, jihohin Arewa 5

A cewarta, takardar za ta taimaka musu wajen bunkasa sana’o’in dogaro da kai da kuma samun ayyukan yi, cewar rahoton Punch.

Yadda sabon shirin zai gudana a fadin Najeriya

Ta ce za a bayar da horon ta hanyar manhajar koyarwa ta zamani (LMS) wacce ke kunshe da gwaje-gwaje da yadda kasuwanci ke tafiya a duniya domin koyarwar ta gudana cikin sauki da nishadi.

Mista Esan ta kara da cewa, za a fara gudanar da horon a zahiri a Abuja nan ba da jimawa ba, sannan daga baya za a fadada shi zuwa sauran jihohi 36.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Hoton shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu yana rattaba hannu kan doka a fadar shugaban kasa Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter
"Duka matasan Najeriya na da damar rijista a shirin, ciki har da ɗalibai, masu bautar ƙasa (NYSC), ’yan kasuwa, masu neman aiki da ƙwararrun matasa a jihohi 36 da Abuja.
"Rijista kyauta ce kuma tana gudana yanzu haka a shafin yanar gizo: www.investonaire.org," in ji ta.

Gwamnatin Tinubu za ta samar da ayyuka

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bullo da wani sabon shiri da zai horar da matasa kuma ya bude masu kofofin samun ayyuka a duniya.

Kara karanta wannan

"Sojoji ba za su iya murkushe yan bindiga a jihohi 7 ba," Gwamna ya tsage gaskiya

Gwamnatin ta ce wannan shirin, zai horar da matasa miliyan 20 a fannoni daban-daban daga nan zuwa shekarar 2030.

A tsarin za a koyar da fasahar zamani a karkashin shirin DALI, wanda zai ba matasa damar haduwa da wadanda za su dauke su aiki ko su samu damar yin kasuwanci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262