Matsayar Al’ummomin Sokoto, Zamfara yayin da Ake Tababa kan Sulhu da Bello Turji

Matsayar Al’ummomin Sokoto, Zamfara yayin da Ake Tababa kan Sulhu da Bello Turji

  • Al’ummomin Sabon Birni, Isa da Shinkafi a jihar Zamfara da Sokoto sun bayyana matsayarsu kan sulhu
  • Mutanen sun yi watsi da kiran tattaunawa da hatsabibin dan bindiga, Bello Turji, suna cewa sulhun bai da amfani
  • Jama'a sun zargi Turji da kashe-kashe, garkuwa da mutane, cin zarafin mata da kona kauyuka da-dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Al’ummomin Sabon Birni da Isa a Sokoto, tare da wasu daga Shinkafi a Zamfara sun yi magana kan sulhu.

Al’ummomin yankunan sun yi watsi da kiran yin sulhu da Bello Turji da suka ce ya kashe mutane da dama.

Ana ta maganganu kan sulhu da Bello Turji a Najeriya
Rundunar sojoji ta yi watsi da batun cewa Turji wai ya mika wuya. Hoto: HQ Nigeria Army.
Source: Twitter

Matsayar wasu mazauna Zamfara, Sokoto kan sulhu

Rahoton Zagazola Makama ya ce mutanen sun maida martani ga Farfesa Abubakar Usman Ribah da aka ce yana son a yi sulhu.

Kara karanta wannan

Sheikh Asada ya yi watsi da batun sulhu da Bello Turji, ya kawo mafita

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rabah ya bukaci sake tattaunawa da Turji da mabiyansa domin tabbatar da zaman lafiya a Arewa maso Yamma.

Mazauna yankin a wata sanarwa sun ce su ne mutane na farko da suka fuskanci zaluncin Turji tsawon shekaru, ba za su amince da sulhu ba.

Sun tunatar da cewa cikin shekaru 13, Turji ya kai hari kan akalla kauyuka 89 a Sabon Birni da Isa, ya kashe, ya yi garkuwa da dubban mutane.

A cewarsu, fiye da rabin jama’ar yankin sun gudu zuwa Jamhuriyar Nijar, sakamakon hare-haren da suka hallaka daruruwan mutane.

Sanarwar ta ce:

“Farfesa Ribah, mu ’yan asalin kauyukan da Turji ya lalata ne, ba mu bukatar labari daga waje, mun sha wahala.”
Mazauna Zamfara da Sokoto sun ki maganar sulhu da Turji
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma a Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

An soki maganar sulhu da Bello Turji

Al’ummomin sun zargi mabiyan Turji da kisan gilla, kona gidaje, satar shanu, garkuwa da mutane, karbar kudin fansa da kuma fyade ga mata.

Sun kuma yi Allah wadai da sulhun da gwamnati ta taba yi da shi, wanda suka ce ya ci kudi, ya kara masa karfi amma bai dakatar da shi ba.

Kara karanta wannan

Sheikh Pantami ya nuna bacin rai kan an bindige Musulmai 27 suna salla a masallaci

Sanarwar ta kara da cewa:

“Duk wani yunkurin tattaunawa sai ya ƙara ƙarfafa shi, Bello Turji har yanzu na ci gaba da zaluntar jama’armu.”

Sun tambayi ko Farfesa Ribah ya taba shawartar sarakunan gargajiya ko shugabannin kauyukan da aka raba da muhallansu kafin ya nemi sulhu da Turji.

“Sulhu abin so ne a Musulunci, amma ba a wajabta a sa musulmi sau biyu cikin rami guda, mun yi asara sosai.”

- Cewar mutanen

Al’ummomin sun dage cewa zaman lafiya na gaskiya ba zai tabbata ba sai an samu adalci da dawo da hakkokin al’ummomin da abin ya shafa.

Bello Turji dai ya kasance jagoran ’yan bindiga da sojoji suka ayyana a matsayin mai laifi, wanda ake zargi da kisan daruruwan mutane a iyakokin Sokoto, Zamfara da Nijar.

Turji: Sheikh Asada ya yi tone-tone kan sulhu

Mun ba ku labarin cewa Sheikh Murtala Bello Asada ya fito da sabon bidiyo inda ya soki masu fakewa da sulhu da ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Mamakon ruwan ya lalata gidaje, ya raba mutane sama da 600 da muhallansu a Yobe

Malamin ya ce dan bindiga mai suna Dan Sadiya ya karɓi miliyan bib-biyu a matsayin kudin fansa ba sulhu ba.

Sheikh Asada ya tabbatar da cewa bayan an biya kuɗin fansa, Dan Sadiya ya kai hari inda ya sace mutane 27.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.