'Akwai Matsala a N70, 000,' Amurka Ta Fitar da Rahoto kan Mafi Karancin Albashin Najeriya

'Akwai Matsala a N70, 000,' Amurka Ta Fitar da Rahoto kan Mafi Karancin Albashin Najeriya

  • Gwamnatin Amurka ta ce sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 ba zai iya fitar da ‘yan ƙasa daga talauci ba saboda tsananin matsin tattalin arziki.
  • Duk da cewakusan an ninka albashin daga yadda ya ke a baya, rahoton ya bayyana cewa har yanzu ana fama da wasu jihohin kasar kan biyan N70,000
  • Rahoton ya ce 70% zuwa 80% na ‘yan Najeriya ba da gwamnati ko ma'aikatu su ke aiki ba, inda ba a bin ka’idojin albashi da kare mutuncin ma'aikatan

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar AmericaGwamnatin Amurka ta bayyana rashin gamsuwa da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 da Najeriya ta amince da shi a 2024.

A cewar rahoton da Ma’aikatar Harkokin Waje ta Amurka ta fitar ranar 12 ga watan Agusta, 2025, sabon albashin bai da ƙarfin da zai ceto talakawa daga cikin tsananin talaucin da su ke ciki.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta rufe shafukan 'yan Najeriya miliyan 13 a Facebook, Instagram da TikTok

Amurka ta damu kan albashin 'yan Najeriya
Hoton Shugaba Bola Tinubu (H), Shugaban Amurka, Trump (D) Hptp: Bayo Onanuga/Donald J Trump
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa rahoton ya bayyana cewa sabon albashin ya kai kusan $47.90 kacal a wata, wanda bai yi daidai da tsadar rayuwa da hauhawar farashi a ƙasar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amurka ta damu kan albashin 'yan Najeriya

Business Day ta wallafa cewa rahoton ya nuna cewa duk da an ninka albashin ma'aikatan kasar nan, gwamnati ba ta da tsayayyen tsarin aiwatar da shi.

Ta nuna damuwa da rashin gamsuwa ganin yadda jihohi da dama suka ƙi biyan sabon albashin bisa dalilan rashin kuɗi.

Rahoton ya kara da bayyana cewa dokar karin mafi karancin albashin ta shafi kamfanoni da ke da ma’aikata 25 zuwa sama.

Ta ce wannan ya bar yawancin masu aiki a ƙananan masana’antu da sauran ayyukan kwadago ba tare da kariyar doka ba da ya wajabta biyansu mafi karancin albashin.

Haka kuma, ma’aikatan wucin-gadi, na noman damuna da waɗanda ke aiki da kwangila na kwamitoci ba su cikin tsarin.

Kara karanta wannan

N70,000: Amurka ta koka da karin albashi, matsalolin shari'a da tsaro a Najeriya

Amurka: 'Ma'aikatan Najeriya na jin jiki'

Rahoton ya kara bayyana cewa kimanin 70% zuwa 80% na ma’aikata a Najeriya suna aiki ne a kasuwar bayan fage, inda babu cikakken tsari na albashi, tsawon sa’o’i, da sauransu.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Kasa, Bola Tinubu yana addu'a Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya ce hakan ya bar ma’aikata da dama cikin haɗarin cin zarafi da rashin biyansu hakkokinsu yadda ya kamata.

Rahoton ya kara da bayar da tabbacin cewa al'amura da dama sun jefa jama'a a halin ni 'ya su, yayin da miliyoyin ma’aikata ke cikin wahala da rashin tabbacin samun rayuwa mai kyau.

Amurka ta yi magana kan halin Najeriya

A baya, mun ruwaito cewa gwamnatin Amurka ta nuna damuwa game da matsalolin da ke damun Najeriya a fannin tsaro da yadda ake gudanar da harkokin shari'a.

Amurka ta bayyana cewa har yanzu akwai batutuwa na tsare mutane ba tare da gurfanar da su gaban shari’a ba, sannan kuma ana fama da jinkiri mai tsawo wajen yanke hukunci.

Amma fadar Shugaban Kasa ta ce gwamnati na ci gaba da aiki tuƙuru wajen gyara tsarin shari’a da inganta tsaro, tare da aiwatar da matakai na sauƙaƙa wahalhalun tattalin arziki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng