Bayan Kusan Wata 1 a Asibitin London, Ganduje Ya Dawo Gida, an Fadi Halin Lafiyarsa
- Tsohon shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje, ya dawo Najeriya daga kasar Birtaniya bayan shafe kusan wata guda
- Hakan ya biyo bayan tafiya London bayan ya yi murabus daga shugabancin APCwanda ya jawo alamar tambaya wancan lokacin
- Ganin Ganduje ya dawo cikin koshin lafiya ya sa magoya baya farin ciki, Mohammed Garba ya tabbatar da dawowarsa daga tafiyar lafiya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya dawo Najeriya daga kasar London bayan jinya a asibiti.
Ganduje ya dawo ne a ranar Laraba 20 ga watan Agustan 2025 bayan shafe kusan wata a London da ke kasar Birtaniya.

Source: Twitter
Tsohon shugaban ma’aikatansa, Mohammed Garba shi ya tabbatar da haka ga jaridar Punch a jiya Laraba 20 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan
Akpabio ya bayyana ana rade radin shugaban majalisa yana kwance a asibitin Landan
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganduje ya tafi London domin kula da lafiyarsa
Ganduje ya tafi London ne domin duba lafiyarsa jim kaɗan bayan ya yi murabus daga shugabancin jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Ajiye aikin da Ganduje ya yi ta jawo maganganu inda ake ta zargin ainihin dalilin yin murabus dinsa da cewa tilasta shi aka yi.
An zabi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC a watan Agusta 2023, sai dai ya yi murabus ranar 27 ga Yuni 2025 saboda ya ba lafiyarsa muhimmanci.

Source: Twitter
Mukamin da Tinubu ya ba Ganduje a Najeriya
Bayan murabus dinsa, an nada shi shugaban hukumar kulawa da aikin filayen jiragen saman Najeriya (FAAN) a ranar 9 ga Yulin 2025.
Shugaba Bola Tinubu ne ya nada tsohon gwamnan Kano mukamin wanda wasu ke cewa an yi haka ne domin saka masa bayan tilasta shi yin murabus daga shugabancin jam'iyyar.
Tsohon ministar jin kai, Netanwe Yilwatda, shi ne aka zaba a matsayin sabon shugabar jam’iyyar APC bayan saukarsa daga wannan kujera.
A jawabinsa na farko, Yilwatda ya sha alwashin dawo da martabar APC mai mulkin kasar tare da tabbatar da hadin kan mambobinta.
An tabbatar da dawowar Abdullahi Ganduje Najeriya
Na kusa da Ganduje, Garba ya ce mai gidansa ya iso Najeriya da safiyar Laraba 20 ga watan Agustan 2025 bayan hutun jinya a waje.
Tsohon gwamnan Kano ya bar kasar don jinya jim kadan bayan murabus dinsa daga shugabancin jam’iyya, wanda ya jawo cece-kuce a cikin APC.
Ya ce:
“Eh, ya dawo Najeriya yau, lafiyarsa ta inganta, ya dawo gidansa cikin walwala."
Garba ya bayyana cewa Ganduje ya bar Najeriya zuwa London kwanaki biyar bayan murabus dinsa daga shugabancin jam’iyyar don neman kulawar lafiya.
An musanta cewa Ganduje ya kwanta a asibiti
A baya, kun ji cewa a ranar Lahadi 20 ga Yuli 2025, rahotanni sun yaɗu cewa an kwantar da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje a asibiti a London.
Sai dai daya daga cikin makusantansa, Salihu Tanko Yakasai ya musanta rahoton, yana mai cewa Ganduje na cikin koshin lafiya kuma bai kwanta a asibiti ba.
Yakasai ya bayyana cewa Ganduje ya tafi London kafin rasuwar Muhammadu Buhari da kafarsa, kuma ba don jinya ya tafi ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
