'Dan Kano da Ya Yi Nasara a Gasar Kur'ani a Saudi Ya Samu Naira Miliyan 163

'Dan Kano da Ya Yi Nasara a Gasar Kur'ani a Saudi Ya Samu Naira Miliyan 163

  • Ɗan Najeriya, Buhari Sanusi daga Kano, ya zo na uku a gasar Alƙur’ani ta duniya da aka gudanar a Masallaci mai alfarma a Saudiyya
  • Ɗan Tchadi ya lashe gasar yayin da ɗan Saudi Arabia ya zama na biyu, lamarin da ya sanya Najeriya cikin farin ciki da alfahari
  • Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto ya jaddada muhimmancin aiki da Alƙur’ani domin samun karramawa ta gaskiya a lahira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ɗan Najeriya, Buhari Sanusi daga Kano, ya samu nasarar wakiltar ƙasar a gasar Alƙur’ani ta duniya da aka gudanar a Masallaci mai alfarma a Saudiyya.

Rahotanni sun nuna cewa Buhari Sanusi ya zo na uku cikin mahalarta daga ƙasashe 128 da suka fafata a gasar.

Tawagar Najeriya a gasar Kur'ani da aka yi a Saudiyya
Tawagar Najeriya a gasar Kur'ani da aka yi a Saudiyya. Hoto: Mansur Ibrahim
Source: Facebook

A wani bidiyo da jagoran musabakar Najeriya, Farfesa Masur Sokoto ya wallafa a Facebook, Buhari ya nuna farin ciki da nasarar da ya samu.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Malaman Musulunci sun yi zanga zanga kan alaƙar Najeriya da Isra'ila

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasarar ta sanya Najeriya cikin farin ciki da alfahari, musamman ganin cewa sauran matasan Musulmi daga Tchadi da Saudiyya suka rike matsayi na farko da na biyu.

Farfesa Mansur Ibrahim daga Sokoto, ya bayyana godiya ga Allah tare da jaddada kira ga mahalarta da su yi aiki da Alƙur’ani domin samun daraja mai ɗorewa a lahira.

'Dan Najeriya ya zo na 3 a gasar Kur'ani

Bincike ya nuna cewa Buhari Sanusi ya kasance ɗalibi mai hazaka da jajircewa wajen haddace Alƙur’ani.

Legit ta rahoto cewa a shekarar 2024 ya lashe gasar Alƙur’ani ta ƙasa da aka yi a Najeriya, wanda hakan ya ba shi damar wakiltar ƙasar a 2025 a Saudiyya.

A jawabin da ya yi bayan samun nasarar, Buhari ya fara da miƙa godiya ga Allah, sannan ya gode wa malamansa da shugabannin da suka tsaya masa tsayin daka har ya kai wannan matsayi.

Rahoton shafin Ummi na kasar Saudiyya ya bayyana cewa an ba Buhari kyautar Riyal 400,000 da ya haura Naira miliyan 160 a kudin Najeriya.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta ragargaji Atiku, El Rufa'i kan wata nasarar da Tinubu ya samu

Jagoran tawagar Najeriya ya yi kira

Jagoran tawagar Najeriya, Farfesa Mansur Ibrahim, ya bayyana farin cikinsa da yadda matashin ɗan Najeriya ya yi bajinta.

Ya yi kira ga mahalarta musamman waɗanda suka samu gurbin girmamawa da su mayar da hankali wajen aiki da Alƙur’ani a rayuwarsu.

A cewarsa, karramawar gasar ba ta kai karramawar lahira ba, don haka ya kamata a yi amfani da wannan dama wajen neman yardar Allah.

Ya kuma bukaci a yi wa dan takarar karramawa ta musamman a Najeriya kamar yadda aka masa a Saudiyya.

Jagoran musabakar Najeriya, Farfesa Mansur.
Jagoran musabakar Najeriya, Farfesa Mansur. Hoto: Mansur Ibrahim Sokoto
Source: Facebook

Godiya ga gwamnati ga makarantu

Farfesa Mansur ya kuma mika godiya ga gwamnatin tarayya da kuma gwamnatocin Kano da Zamfara bisa gudumawar da suka bayar.

Haka kuma ya yaba wa Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sokoto bisa gudumawar da ta ke bayarwa a harkar musabaka.

Legit ta tattauna da malamar Kur'ani

Wata malamar Kur'ani a jihar Gombe, Nusaiba Bala Adamu ta zantawa Legit Hausa cewa ya kamata a karrama Buhari.

Kara karanta wannan

Nijar: An harbe shugaban Boko Haram da ya maye gurbin Shekau har lahira

Malamar ta ce:

"Wannan nasara ce a gare mu baki daya. Ya kamata a karrama shi yadda ya kamata."
"Kwanakin baya wasu daliban Turanci sun ci gasa a Birtaniya kuma labarinsu ya karade kafafen sada zumunta, amma shi ba a yada labarin shi kamar nasu ba."

Nasiha ga musulmai kan gyara sallah

A wani rahoton, kun ji cewa malamin Musulunci a jihar Sokoto, Dr Jabir Sani Mai Hula ya yi nasiha ga Musulmi kan gyaran sallah.

Dr Jabir Mai Hula ya bukaci mutane su rika lura da tufafin da suke sakawa wajen gudanar da ibadar sallah.

Ya ja hankalin al'umma a kan sanya tufafi mai dauke da hoton 'yan siyasa, 'yan kwallo da sauransu wajen gudanar da sallah a kodayaushe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng