Mutuwa Ta Ratsa Masana'antar Fim, Firaccen Jarumi Ya Yi Bankwana da Duniya
- Masana'antar shirya fina-finai ta Nollywood ta sake yin babban rashin fitaccen jaruminta da ya ba da gudunmawa na shekaru
- Shahararren ɗan wasan kwaikwayo na Nollywood, Fabian Adibie, ya rasu yana da shekara 82 a duniya bayan ya yi fama da jinya
- Shugaban Best of Nollywood, Seun Oloketuyi ya tabbatar da mutuwarsa a safiyar Laraba, inda ya ce ya rasu ƙarfe 2:30 na dare
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - An shiga jimami bayan sanar da mutuwar fitaccen jarumin fina-finai a Najeriya wanda ya ba da gudunmawa sosai.
Shahararren ɗan wasan a masana'antar Nollywood, Fabian Adibie ya rasu yana da shekara 82 a duniya bayan fama da jinya na tsawon lokaci.

Source: Facebook
An sanar da mutuwar jarumin fim a Najeriya
Labarin mutuwarsa ya tabbata ne a safiyar ranar Laraba daga bakin shugaban Best of Nollywood (BON), Seun Oloketuyi wanda ya wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Seun Oloketuyi ya tabbatar da cewa marigayin ya rasu ƙarfe 2:30 na dare ranar Laraba 20 ga watan Agustan 2025 da muke ciki.
Mutuwar dattijon ta yi matukar taba mutane da dama musamman abokan aikinsa a masana'antar Nollywood duba da irin girman da yake da shi a idonsu.
A cikin gajeren rubutun da ya yi, Seun Oloketuyi ya ce:
"Jarumi a shirin 'Things Fall Apart', Fabian Adibie ya rasu, jarumin ya bar duniya da misalin karfe 2:30 na daren ranar Laraba. Karin bayani na biyo baya."
Gudunmawar marigayin a masana'antar shirya fim
Adibie ya yi fice wajen fitowa a fina-finan Nollywood na gargajiya, inda ya zama ɗaya daga cikin fitattun jaruman da ake darajawa a masana’antar.
An fi sanin jarumin da rawar da ya taka a fim ɗin “Things Fall Apart,” wani littafi na marubuci, Chinua Achebe.

Source: Facebook
Rudani da abokan aikin marigayin suka shiga
Tun bayan rasuwarsa, abokan aikinsa a masana'antar Nollywood da masoya sun rika aiko da sakwannin ta’aziyya ga iyalansa da kuma abokan arziki.

Kara karanta wannan
Kashim: Wike ya fallasa dalilin da ya sa Babachir Lawan ke yawan sukar Bola Tinubu
An fahimci cewa wasu sun yi jimamin rasuwarsa inda suka bayyana shi a matsayin wanda ya ba da gudunmawa a masana'antar.
Mutane da dama sun yi martani bayan sanar da rasuwar marigayin inda suke ta yi masa fatan samun rahama a gobe kiyama.
Daga cikinsu akwai wadansa suka yaba da yadda ya ba tsaya tsayin daka domin ganin an samu ci gaba a masana'antar.Nollywood saboda kwarewar da yake da shi.
Shahararren jarumin Nollywood ya bar duniya
A baya, mun ba ku labarin cewa jarumin masana'antar shirya fina-finan Nollywood, Olusegun Akinremi da aka fi sani da Cif Kanran ya mutu yana da shekaru 70 a duniya.
An tabbatar da cewa jarumin wanda ya shahara wajen fitowa a matsayin Sarki ko mai mulki ya rasu ne da safiyar ranar Juma'a 15 ga watan Agustan 2025.
A shekarun baya, Cif Kanran ya bayyana cewa ya ja baya daga shiga harkar shirin fina-finai saboda wasu matsaloli da yake fuskanta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
